Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-06 18:10:33    
Gwamnatin kasar Sin tana kokarin daidaita matsalar rashin wurin kwana da matalauta suke fuskanta

cri
A gun wani taron manema labaru da aka shirya a birnin Beijing a ran 6 ga wata, jami'an gwamnatin kasar Sin sun ce, kasar Sin za ta ci gaba da daukar matakai domin tabbatar da ganin an raya kasuwar samar da gidajen kwana ta kasar yadda ya kamata, kuma wannan kasuwa za ta iya bayar da gudummawarta wajen habaka bukatu a gida da cigaban tattalin arziki. A waje daya, kasar Sin za ta kara karfin samar da gidajen kwana ga wadanda suke samun kudin shiga kadan domin kyautata sharadinsu na kwana.

A gun wannan taron manema labaru, madam Wang Xiaohua, mataimakiyar direktan hukumar tsara manufofin haraji ta ma'aikatar sha'anin kudi ta kasar Sin, ta ce, "Ba a iya samun sakamakon da ake nema ba nan da nan sakamakon manufofin da gwamnati ta bayar a 'yan watannin da suka gabata. An daidaita manufofin da suke da nasaba da kasuwar samar da gidajen kwana sau da yawa a shekara ta 2008. Amma ko za a bayar da sabbin manufofi a shekara ta 2009, za mu tsai da wani kuduri bisa yadda ake aiwatar da wadannan manufofin da muka tsara a shekara ta 2008. Idan ana aiwatar da su da kyau, to, za mu ci gaba da aiwatar da su. Idan ba a iya aiwatar da su kamar yadda ake fata ba, shi ke nan, mai yiyuwa ne za mu nemi tsara sauran manufofin da suke dacewa."

Tun bayan da aka shiga karshen rabin shekarar da ta gabata, yawan gidajen kwana da ake sayarwa a kasuwa ya ragu sosai sakamakon matsalar hada hadar kudi ta duniya da raguwar saurin karuwar tattalin arzikin kasar Sin. Sakamakon haka, a cikin 'yan watannin da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta bayar da jerin manufofin sa kaimi ga bunkasuwar kasuwar samar da gidajen kwana.

A lokacin da gwamnatin kasar Sin take kokarin raya kasuwar samar da gidajen kwana kamar yadda ya kamata, gwamnatin kasar Sin tana kuma mai da hankali kan matsalar rashin wuraren kwana da wadanda suke samun kudin shiga kadan suke fuskanta. Bisa shirin da ta tsara, gwamnatin kasar Sin tana son yin amfani da shekaru 3 domin warware matsalar rashin wuraren kwana da take kasancewa a gaban iyalai kusan miliyan 10 wadanda suke samun kudin shiga kadan a kowace shekara.

Mr. Qi Ji, mataimakin ministan gidajen kwana da raya birane da kauyuka na kasar Sin ya bayyana cewa, kara yawan gidajen kwana da ake samar a kasuwa ba zai kawo illa ga kasuwar cinikin gidajen kwana ba. Mr. Qi ya ce, "Bayan da aka samar da karin gidajen kwana irin na ba da tabbaci ga wadanda suke samun kudin shiga kadan, da farko dai, za a iya warware matsalar rashin wuraren kwana da wadanda suke samun kudin shiga kadan suke fuskanta a kasuwa. Sannan za a iya gane yadda ake raya kasuwar samar da gidajen kwana a kasar Sin a bayyane sosai. Iyalai wadanda suke samun kudin shiga kadan za su iya warware matsalar rashin wuraren kwana da suke fuskanta bisa taimakon da gwamnati ke samar musu. Sauran mutane za su iya saye ko yin hayan gidajen kwana a kasuwa kai tsaye."

An bayyana cewa, a kafin karshen shekarar 2008, gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta riga ta kebe kudade kimanin yuan biliyan 10 daga baitulmali na tsakiya domin tallafawa aikin gina gidajen kwana da za a sayar wa iyalai wadanda suke samun kudin shiga kadan. Mr. Qi Ji ya kara da cewa, "Ko wata rana tattalin arzikinmu ya samu cigaba sosai, yawan kudin shiga da jama'a ke samu ya karu cikin sauri, ko shakka babu, gwamnati za ta ci gaba da tallafawa wadanda suke samun kudin shiga kadan wajen samar da gidajen kwana. Wato, a ko da yaushe, gwamnati tana da nauyin samar da wuraren kwana irin na ba da tabbaci ga wadanda suke samun kudin shiga kadan." (Sanusi Chen)