Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-05 21:26:20    
Wasu labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri

---- Kwanan baya a nan birnin Beijing, Mr. Du Qinglin, mataimakin shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin, kuma shugaban sashen kula da harkokin hadin kai na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar kwaminis ta Sin ya gana da Kelsang Gyaltsen, wakilin Dalai lama da 'yan rakiyarsa.

Mr. Du Qinglin ya yi wa Kelsang Gyaltsen da 'yan rakiyarsa bayani kan babbar nasarar da aka samu wajen shirya wasannin Olimpic da wasannin Olimpic na nakasassu na Beijing, da yadda aka yi zirga-zirgar kumbo mai daukar mutane kirar shenzhou 7 tare da cikakkiyar nasara, kuma ya bayyana halayen bunkasa tattalin arziki da ake yi jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta da ma a duk kasar Sin baki daya, da yadda aka sha fama da bala'in girgizar kasa da guguwar iska da dusar kankara a jihar Tibet.

Mr. Du Qinglin ya bayyana cewa, a kowane lokaci kuma bisa kowane hali, kada a dakushe niyya kan matsalar kiyaye dinkuwar kasa mahaifa daya da cikakken yankin kasar. Ya kamata Dalai lama ya girmama tarihi da tinkarar hakikanin abun da ake ciki, kuma ya gyara ra'ayin da ya dauka kan siyasa sosai, ya daina nuna goyon bayansa ga dukkan ra'ayoyi da danyun aikin da aka yi domin neman "mulkin kan Tibet" da jawo baraka ga kasar mahaifa wato kasar Sin.

Mr. Du Qinglin ya kuma bayyana cewa, manufar da gwamnatin tsakiya ta dauka kan Dailai lama ta kullum ne kuma a bayyane, kuma kofar yin shawarwari kullum a bude take.

---- Wakilinmu ya samu labari daga wajen hukumar kiyaye muhalli ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin cewa, nan gaba kadan za a fara aiki na mataki na 2 domin kiyaye muhallin wuri mai danshi na Lalu da ke birnin Lhasa na jihar wanda aka ware kudin Sin wato Yuan miliyan 50 ga yin sa. Sabo da haka za a kara ba da kariya ga wannan wuri mai danshi na birni wanda ya fi tsayi daga matsayin teku kuma ya fi fadi a kasar Sin'

Wani jami'in da abin ya shafa na hukumar kiyaye muhalli ta jihar Tibet ya ce, kudin Sin mai yawan Yuan miliyyar 50 da aka ware a wannan karo za a yi amfani da shi ne musamman domin kyautata muhimman koramu da kuma kiyaye tsire-tsiren da ke wuri mai danshi na Lalu.

Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, yawan nau'o'in dabbobi da na tsire-tsire da ke wannan wuri mai danshi ya karu a bayyane. Bisa kididdigar da aka yi an ce, yawan nau'o'in dabbobi da na tsire-tsiren daji da ke wuri mai danshi na Lalu ya wuce 470, shi ya sa wannan wuri ya zama wani siton adana kwayoyin halitta wato gene na nau'o'in halittu masu rai na birnin dake faffadan tsauni.