A cikin 'yan shekarun da suka wuce, batun tsimin makamashi da na rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli sun riga sun zama batutuwan da ke jawo hankalin jama'a a duk duniya, ko shakka babu a kasar Sin ma ana kula da su sosai. A cikin shirinmu na yau, za mu bayyana muku yadda unguwar raya masana'antun kimiyya da fasaha ta Zhongguancun ta birnin Beijing, wadda ke matsayi mafi girma a cikin unguwannin raya masana'antun kimiyya da fasaha na kasar Sin, take tsimin makamashi da rage abubuwa masu gurbata muhalli.
A shekarar 1988 ce aka kafa unguwar raya masana'antun kimiyya da fasaha ta Zhongguancun ta Beijing, wadda ke kunshe da masana'antun kimiyya da fasahohin zamani fiye da dubu 18 na kasar Sin da na kasashen waje. Lokacin da wakilinmu ya yi ziyara a wannan unguwa, da farko dai, ya ga muhalli mai kyaun gani da kyawawan ayyukan yau da kullum da aka samar a ciki. Mr. Dai Wei, shugaban kwamitin kula da harkokin wannan unguwa ya bayyana cewa, "A wajen tsimin makamashi da ruwa, mun yi amfani da wasu fasahohin yin amfani da makamashin da za a iya sake yin amfani da shi, kuma mun yi amfani da fasahohin tsimin makamashi a lokacin da muke gina sabbin gine-gine a unguwarmu domin cimma burinmu na tsimin wutar lantarki. A waje daya kuma, muna da tsarin samar da ruwan da aka sake tsabtace shi da yin amfani da ruwan sama a unguwarmu domin tsimin ruwa. Sannan kuma, a wajen aikin tabbatar da ingancin muhalli, mun yi kokarin tabbatar da kasancewar albarkatun halittu iri iri a unguwarmu domin kara shimfida ciyayi da itatuwa da kuma yin amfani da makamashin da za a iya sake yin amfani da shi a unguwarmu."
Ko shakka babu, ba ma kawai an samar da wadannan ayyukan yau da kullum wajen raya wata unguwa mai daukar sauti ba, hatta ma an shigar da wasu kamfanonin da suke nazarin fasahohin tsimin makamashi da na rage abubuwa masu gurbata muhalli a unguwar raya masana'antun kimiyya da fasahohi ta Zhongguancun. Alal misali, fasahar Membranereactor da kamfanin kimiyya da fasaha ta Originwater ya mallaka tana mataki na farko a duk duniya, kuma shi kamfani ne da ke gaban takwarorinsa a kasar Sin wajen samar da fasahar tsabtace gurbataccen ruwa.
A waje daya kuma, kamfanin Tsinghua Tongfang muhimmin kamfani ne da ke samar da fasahohin bayanai a kasar Sin. Amma kamfanin yana kuma amfani da fasahohin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli a cikin fasahohin da yake samarwa a fannonin kera kayayyakin fasaha da akwatunan talibijin da injuna masu kwakwalwa da gina gine-gine masu hazikanci. Mr. Fan Xin na kamfanin Tsinghua Tongfang ya bayyana cewa, "Muna amfani da fasahar magance sinadarin sulphur a manyan kamfanonin samar da wutar lantarki da yawa, kuma mun samu sakamako mai kyau. A waje daya kuma, ana amfani da sabbin fasahohinmu na tsimin makamashi da tabbatar da ingancin muhalli wajen ba da haske a dimbin matsakaita ko manyan ayyuka, ciki har da filaye da dakunan wasannin motsa jiki na Olympic. Lokacin da muke aiwatar da kwangilolin da muka samu, mu kan yi amfani da wadannan fasahohin tsimin makamashi da tabbatar da ingancin muhalli a cikin ayyukanmu."
Kamfani daban da ke cikin wannan unguwa, wato kamfanin Dynamic Power na Beijing kamfani ne da ke kera kayayyakin tsimin makamashi da kiyaye muhalli musamman. Sabuwar na'urar tsabtacen iskar AC da kamfanin ya samar a kwanan baya ba ma kawai zai iya kara tsabtacen iska ba, har ma yana iya yin amfani da makamashi da tsimin makamashi sosai idan an kwatanta shi da na tsoho. Yanzu, ana sayar da irin wadannan sabbin na'urorin tsabtace iska a kasuwa cikin sauri, kuma ana amfani da su kwarai da gaske. A cikin gine-ginen da aka gina domin gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta Beijing, an kuma yi amfani da irin wadannan na'urorin tsabtace iskar AC.
An labarta cewa, a cikin unguwar raya masana'antun kimiyya da fasahohi ta Zhongguancun ta Beijing, irin wadannan kamfanoni, kamar su kamfanin kimiyya da fasaha ta Originwater da kamfanin Tsinghua Tongfang da kamfanin Dynamic Power wadanda suke samar da kayayyakin tsimin makamashi da na kiyaye muhalli suna kusan dubu 2. Ya zuwa shekara ta 2007, jimlar GDP da wadannan kamfanoni suka yi a unguwar ta kai kudin Sin yuan biliyan 80, wato ta kai kashi 10 cikin kashi dari bisa na dukkan GDP da aka yi a wannan unguwa.
Mr. Dai Wei, shugaban kwamitin kula da harkokin wannan unguwa ya bayyana cewa, akwai dimbin dakunan gwaje-gwaje da cibiyoyi wadanda suke nazarin fasahohin tsimin makamashi da na kiyaye muhalli a cikin unguwar. Wato masana da kwararru wadanda suke nazarin fasahohin tsimin makamashi da na kiyaye muhalli, kuma suka kai kashi 1 cikin kashi 4 suna aiki a cikin wannan unguwa. A kan samu sabbin fasahohin zamani na tsimin makamashi da na kiyaye muhalli da suke kan gaba a duk duniya ko a duk kasar Sin a cikin wannan unguwa. Sabo da haka, kwamitin kula da harkokin wannan unguwa ya sa aikin raya fasahohin kiyaye muhalli da tsimin makamashi kan muhimmin matsayin da zai dauka lokacin da yake neman cigaban wannan unguwa. Mr. Dai Wei ya ce, "A cikin 'yan shekarun da suka gabata, masana'antun kera kayayyakin tsimin makamashi da na kiyaye muhalli wadanda suke cikin unguwarmu suna samun cigaba cikin sauri. A bayyane ne irin wadannan masana'antu wadanda suke cikin unguwa daya suna samun cigaba tare. Bisa shirin da muka tsara, za mu kara karfin kirkiro sabbin fasahohin tsimin makamashi da na kiyaye muhalli, da kuma samar da irin wadannan fasahohi da yin amfani da su a kasuwa. Sannan za mu iya hada jerin masana'antu wadanda suke kirkiro sabbin fasahohin tsimin makamashi da na kiyaye muhalli, ko suke amfani da wadannan fasahohi a cikin kayayyakinsu ko suke samar da kayayyakin da ke kunshe da irin wadannan fasahohi a cikin unguwarmu."
Sannan Mr. Dai ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 masu zuwa, unguwar raya masana'antun kimiyya da fasaha ta Zhongguancun ta Beijing za ta nuna goyon baya sosai ga kamfanoni da masana'antun da suke nazarin fasahohin tsimin makamashi da na kiyaye muhalli, ko suke samar da kayayyakin da ke kunshe da irin wadannan fasahohi ta hanyoyin tsara shirin neman cigaban masana'antu da samar da tallafin kudi da dai makamantansu.
Yanzu kwamitin kula da harkokin unguwar raya masana'antun kimiyya da fasaha ta Zhongguancun ya riga ya soma tsara shirin neman cigaban masana'antun samar da kayayyakin tsimin makamashi da na kiyaye muhalli, ya kuma tsara ma'aunin da matakai wajen tsimin makamashi da sake yin amfani da abubuwan bola. A waje daya kuma, an tabbatar da aiwatar da muhimman ayyuka 10 domin yin amfani da sabbin fasahohin tsimin makamashi da na kiyaye muhalli a cikin unguwar.
Bugu da kari kuma, za a samar da tallafin kudin da yawansa mai yiyuwa ne zai iya kai kudin Sin yuan miliyan 5 ga masana'antu da kamfanoni wadanda suke kirkiro sabbin makamashi da fasahohin sake yin amfani da makamashi da na kiyaye albarkatun ruwa da tsimin makamashi. Mr. Li Shizhu, mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin unguwar raya masana'antun kimiyya da fasaha ta Zhongguancun ta Beijing ya bayyana cewa, "Da farko dai za a yi amfani da wannan kudi domin sayen kayayyaki da hidimomin da kamfanoni da masana'antu wadanda suke cikin unguwarmu suka samar. Yawan tallafin kudin da za a samar ba zai wuce kashi 40 cikin kashi dari bisa na jimlar kudaden jarin da ake bukata a wani ayyuka. A waje daya kuma, jimlar tallafin kudin da za mu samar ba za ta wuce kudin Sin yuan miliyan 5 ga kowane shiri."
Mr. Dai Wei, shugaban kwamitin kula da harkokin wannan unguwa ya bayyana cewa, masana'antun samar da kayayyakin tsimin makamashi da na kiyaye muhalli masana'antu ne da aka soma kulawa da su. Tabbas ne za su samu wata kyakkyawar makoma a nan gaba. (Sanusi Chen)
|