Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-02 19:36:18    
'Yan fasahohi na kasa da kasa sun nuna wasannin "Dauwamammen Shakespeare" a birnin Beijing

cri
Wasannin kwaikwayon da William Shakespeare ya rubuta yana da dogon tarihi, tun daga shekaru 400 da suka wuce har zuwa yanzu, 'yan wasan kwaikwayo na zamani daban-daban sun mayar da su tamkar abubuwan daraja. Kwanakin baya, 'yan fasahohi na kasa da kasa sun nuna wasanni da ke da babban taken "dauwamammen Shakespeare" a birnin Beijing, kuma sun nuna wasannin da Shakespear ya rubuta ta hanyoyi daban daban, kuma sun kawo wa 'yan kallo na kasar Sin wasan kwaikwayo na Shakespear kai tsaye.

A ko wace shekara, kasashen duniya sun nuna wasannin da Shakespeare ya rubuta ta hanyoyi daban daban kuma sun shirya bukukuwa da dama da yawansu ya wuce misali game da wasaninsa. Amma ga shi a kasar Sin, ko da yake kowa ya san sunan shakespeare, amma 'yan kallo ba safai su kan iya samun damar kallon wasannin a dandali ba. Bikin wasan kwaikwayo na Shakespeare da aka shirya a nan birnin Beijing, 'yan wasan kwaikwayo na kasa da kasa sun nuna wasanni a karkashin rubutun Shakespeare, kuma sun kara sanya abubuwan al'adu na kasashensu da fahimtarsu game da wasannin kwaikwayo na shakespeare a ciki, don su kirkiro sabbabin rubuce-rubucen Shakespeare.

"Artre aking Lear" shi ne daya daga cikin wasannin kwaikwayo 4 masu ban tausayi da william Shakespeare ya rubuta, inda ya bayyana labari mai ban tausayi game da mata yara sarkin Lear guda uku, sun kwace ikon mulki a kasar. Shahararriyar direktar wasan kwaikwayo ta Sin Tian Xinxin ta sake tsara wannan labari, inda aka bayyana cewa, a karni na 14 zuwa karni na 17 na gidan sarautar Ming, sarkin ya tsufa, amma bai san zai bar karagar mulkin kasar ga wane yaransu ba, yayin da ya shiga uku, waziri ya ba da shawara gare shi, ya gaya masa cewa, ya kamata ya karanta wasan kwaikwayo na Shakepeare "Artre aking Lear" don ya ga labari mai tausayi na sarkin Lear. Sabo da haka, an hada labarin "Artre aking Lear"da labarin "Ming" tare.

Tian Qinxin mutumiya mai son kirkiro sabbabin abubuwa, ta hada fahimtarta da wannan wasan tare. Abubuwan kawatarwa da ke cikin wannan wasa sun yi kamar zane-zane na gargajiya na kasar Sin, haka kuma an nuna su ta hanyoyi daban daban na zamani, bugu da kari kuma tufafin da 'yan wasanni suka sanya su ne tufafi na zamani masu kyaun gani, haka kuma maganganun 'yan wasanni suna da barkwanci sosai. Yayin da 'yan kallo suka kallo wasanni, sun yi kamar tafiya tsakanin lokaci na da da na zamani. Yayin da Tian Qinxin ta bayyana abubuwan da ta kirkiro, ta bayyana cewa,

"Sabon tunanin da muka kirkiro shi ne, mun kawo labarin sarkin Lear zuwa labarin Ming na kasar Sin, sabo da haka, tsarin wannan wasan ya canja sosai, ko da yake ba mu canja dangantakar da ke tsakanin mutane ba, amma mun canja yarima guda 3 zuwa gimbiya. Haka kuma 'yan wasanni da ke cikin wannan wasa sun yi sakin jikinsu sosai , kuma za su iya kallon wasanni tare da 'yan kallo ."

Haka kuma, ban da wannan labarin "Ming", mun sami wani wasan "Artre aking Lear" daban da aka nuna shi da Turanci. 'Yan wasanni na kwaikwayo na kasashen Turai da Amurka da dama sun nuna wannan wasanni tare, suna da fasahohi sosai wajen nuna wasanni, haka kuma dalibai guda 6 na cibiyar nazarin wasannin kwaikwayo da sinima na kasashen waje ta jami'ar Beijing ta kasar Sin su ma sun nuna wannan wasanni tare. Ko da yake, al'adunsu sun sha bamban, amma yayin da 'yan wasanni na gida da na waje suka nuna wasanni na shakespeare, sun hada kansu tare, kuma tauraron wannan wasa Joseph Graves yana ganin cewa, fahimtarsu ga wasannin shakespeare ya inganta hadin gwiwa da ke tsakaninsu. Ya gaya wa manema labaru cewa:

"tun daga shekaru 7 da suka wuce, mun fara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin, wannan wasa shi ne wasan kwaikwayo na 42 da muka nuna shi tare, muna farin ciki sosai sabo da mun yi hadin gwiwa tare da takwarorimmu na kasar Sin, harshen Turanci harshen waje na biyu ne gare su, ga rubuce-rubucen da shakespeare ya yi da harshen waje na uku ne gare su, sabo da haka sun fi kokari, kuma sun kara fahimtarsu game da Shakespeare, wannan ya burge mu sosai.

Wani wasan kwaikwayo mai ban tausayi daban na Shakespeare " Romeo Juliet " yana da sigogi guda biyu ne, watau na sigar Korea ta kudu da na sigar kasar Ukraine.

Babban malami na wasan kwaikwayo na kasar Korea ta kudu Oh Tae Suk ya sake tsara "Romeo Juliet" cikin tsanake, kuma an nuna shi tun daga shekaru da dama da suka wuce a kasar Korea ta kudu. Direktan ya hada wasan kwaikwayo na gargajiya na kasar Korea ta kudu da na zamani tare. Yayin da aka kaddamar da nuna wannan wasanni, sai 'yan wasanni suka sanya tufafi masu kyaun gani a dandali, kuma sun yi wasan raye-raye da takobi don bayyana kiyyaya tsakanin gidaje biyu, kuma sun bayyana halayyen musamman na wasan kwaikwayo na gargajiya na korea ta kudu da halin da ake ciki. Bayan da babban dan wasan da babbar 'yar wasa sun yi kisan kai, 'yan wasannin kwaikwayo da suka sanya tufafin gargajiya na Korea ta kudu sun ji bakin ciki, kuma sun bayyana wannan hali da raye-raye na gargajiya da takobi.

OH Tae Suk ya bayyana cewa. ya tsara wasannin Shakespeare a karkashin wasannin gargajiya na shakespeare, a sa'i daya kuma ya hada da halayyen musamman na kasarsa, watau salon wasannin gargajiya na Korea ta kudu da na zamani, don bayyana kaunar da ke tsakanin Romeo da Juliet.

Amma kungiyar wasannin kwaikwayo ta Ukraine ta OKT ta nuna wasannin "Romeo Juliet" ta hanyar daban, a cikin wasanni, an canja dandalin nuna soyayya mai romantic zuwa dakin Pizza da ke cike da gari. 'Yan wasanni sun nuna wasanni cikin barkwanci sosai, ya kara sanya mutane su ji kauna mai ban tausayi da ke tsakaninsu

An sanya direktar Oskaras Korsanovas mai shekaru 39 na wannan wasan da suna "direkta mai hazikanci sosai", kuma Romeo Juliet yana daya daga cikin fitattun rubuce-rubucensa. Yayin da Oskaras Korsan ovas ya bayyana ra'ayinsa game da wannan wasa, ya bayyana cewa;

"Muna fatan yayin da 'yan kallo suka kalli wannan wasa, sai abubuwan da suke kallo tamkar yadda suka yi a sinama, ga shi wannan dandali, ya iya canjawa, a farko, wannan dandali shi ne wani dakin dafa abinci, amma tare da juyawar hasken wutar lantarki da kide-kide, an canja dandali zuwa coci da kaburbura, game da wasannin shakespear, rikici da ke cikin wasan, shi ne abu mafi muhimmanci, ga shi muna son mu nuna wannan rikicin da ke tsakaninsu a dandali."

Kungiyar wasan kwaikwayo ta TNT ta kasar Birtaniya ta nuna wasan mai ban dariya na "Taming of the Shrew", kuma sun yi amfani da kalmomi na Shakespear, kuma sun nuna wasanni tare da irin salon barkwanci na Birtaniya, lalle 'yan kallo sun yi dariya a dukkan lokaci.

Kungiyar wasan kwaikwayo ta jama'ar Tianjin ta nuna wasa mai ban dariya daban na Shakespeare "A midsummer Night's dream", kuma sun bayyana salon rubutu na william Shakespeare na soyayya.

Bisa labarin da muka samu, an ce, Shakespeare mutum ne mai son raha sosai, ya kirkiro da rubuce-rubuce da dama, labaru masu ban tausayi da ya rubuta ya sanya mutane sun yi kuka, amma labari mai ban dariya da ya kirkiro ya sanya mutane na bushewa da dariya, lalle wasannin da Shakespeare ya rubuta ya yi farin jini a cikin jama'a, bayan da shekaru 400, 'yan fasahohi na kasa da kasa sun sake nuna wasannin da ya tsara, wannan ya fi burge mu sosai, mutane sun yi dariya kuma sun yi kuka, wannan shi ne dauwamammen shakespeare.(Bako)