Da farko dai, bari mu duba wani labari da muka samu daga jaridar 'THISDAY' ta kasar Nijeriya wadda aka fito da ita a ran 30 ga watan Disamba na shekarar 2008, inda aka bayyana cewa, rikicin kudi na duniya bai kawo babbar illa ga bankunan Nijeriya ba, sabo da haka ba a bukaci agaji gare su ba, in ji mataimakin shugaban hukumar majalisar dattawa mai kula da harkokin bankuna, da inshora, da sauran harkokin kudi ta kasar Nijeriya Mr. Kolawole Bajoko. Ya kuma gaya wa jaridar 'THISDAY' a Abuja cewa, ya kamata masu ajiye kudi a bankuan Nijeriya su yi barci sosai, sabo da kudadensu suna zaune lafiya a hannun bankuna.
Wasu mutane sun ba da shawara cewa, ya kamata gwamnatin tarayya ta ba da kudin agaji ga bankunan kasar Nijeriya sakamakon mumunar illa da rikicin kudin duniya ya kawo musu. Game da haka, Mr. Bajomo ya ce,
'Ban yi tsammanin yin haka ba.'
Ya ce, bakunan kasar Nijeriya suna da bambanci da na kasar Amurka, da kuma sauran kasashe. Ya ci gaba da cewa, ya kasance da wasu hukumomi da ke kula da bankunan kasar Nijeriya da kyau. Ya ce, ya kasance da hukumar binciken bankuna na bankin tsakiya na kasar, da kuma hukumar sa ido kan bankuna na bankin tsakiya na Nijeriya, da kuma kamfanin ba da inshore kan kudaden da aka ajiye a cikin bankuna, da kuma wasu hukumomin sarrafa harkokinsu da kansu na bankuna. Ta kafuwar wadannan hukumomi, ana iya ganin labarai idan akwai matsala a bankuna, sa'an nan kuma bankin tsakiya na kasar Nijeriya yana iya daidaita matsalolin da ya gano.
Mr. Bajomo ya bayyana cewa, babu bukata da a ba da kudin agaji ga bankunan kasar Nijeriya, sabo da bankunan ba su cikin halin kaka-ni-ka-yi kamar yadda bankunan sauran kasashe suke ciki ba. A halin yanzu dai, ana kula da bankunan Nijeirya yadda ya kamata. Sabo da haka, bai kamata a gabatar da shawarar ba da kudin agaji ga bankuna a gaban majalisar dattawa ba. Babu bukatar mai da hankali kan irin wannan lamari.
Game da laifuffukan da wasu manyan shugabannin bankuna suka yi, Mr. Bajomo ya ce,
'Wasu an riga an kai su gaban kotu, wasu kuma suna karkashin bincike daga hukumar yaki da laifin tattalin arziki da harkokin kudi ta kasar Nijeriya.'
Jama'a masu sauraro, bayan haka kuma, bari mu duba wani labari na daban da muka samu daga jaridar 'Daily Independent' ta kasar Nijeriya, wadda aka fito da ita a ran 29 ga watan Disamba na shekarar 2008, inda aka tattauna tasirin da rikicin kudi na duniya yake kawo wa tattalin arziki na tsarin kudi na kasar Nijeriya. Ko da yake wasu mutane sun ce, rikicin kudi ya kawo illa ga tattalin arizkin Nijeriya, amma wasu gwamnoni sun yi kokarin rage tsoron jama'a daga tasirin da rikicin kudi na duniya ya kawo wa tattalin arzikin kasar Nijeriya. Gwamnan bankin tsakiya na kasar Nijeriya Farfesa Chukuma Soludo ya jaddada cewa, bankunan Nijeriya suna zaune lafiya, haka kuma ya sanar da bayar da riba ga masu hannun jari.
Ko da yake haka ne, amma farashin mai a kasuwar duniya ya ragu sosai, wanda ya ragu daga kudin Amurka dala 140 ko wace ganga zuwa dala 54 ko wace ganga, sabo da haka ne, gwamnatin tarayya ta riga ta fara gargadin jama'a da su dauki matakai domin daidaita matsalar kudi a shekarar 2009. sabo da haka ne, ake iya ganin cewa, tattalin arzikin kasar Nijeriya bai iya rabuwa da na duk duniya ba, a kalla dai kudin shiga da gwamnati take samu ya riga ya ragu.
Rikicin kudi ya addabi kasashe masu sukuni, wadanda su kan shigar da mai daga kasar Nijeriya, sabo da haka ne za su rage bukatarsu wajen mai, a maimakon haka, Nijeriya ba za ta iya fitar da mai kamar yawan na da ba.(Danladi)
|