Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-02 19:26:56    
Murnar sabuwar shekara ta 2009

cri
Masu sauraro, assalamu alaikum, barkanku da sabuwar shekara. Ga shi shekarar 2008 ta kare, kuma dukan ma'aikatan sashen Hausa na rediyon kasar Sin muna taya ku murnar shiga sabuwar shekara, kuma da fatan Allah ya sa mu ga karshenta lafiya, ya kuma sada mu da dukkan alherin da ke cikinta.

Babu shakka, a shekarar 2008 da ta gabata, kowa na da abubuwan da ba za su iya mantawa da su ba, ko wannan ya kasance abin farin ciki ne, ko kuma na bakin ciki, amma duk sun wuce, yanzu kowa na rike da fatan alheri ga wannan sabuwar shekara ta 2009. Kwanan nan, masu sauraronmu su ma sun turo mana wasikunsu, inda suka bayyana mana abubuwan da suka burge su a shekarar 2008 da kuma kyakkyawan burinsu game da shekarar 2009. Kamar dai yadda Aliyu Bashir daga Katsina, Nijeriya ya rubuta cikin wasikarsa, ya ce, "A gaskiya shekarar 2008, ta yi mani dai-dai bisa ga abubuwan da suka faru na wasannin motsa jiki da ya gabatar a babban birnin kasar Sin, da kuma samun nasara da na yi a gasar kacici-kacici da na yi duk a cikin wannan shekara aini kam sai godiya da Allah san barka. kuma fatan shekara mai zuwa mu ga abin alherin da wuce haka. Sakon gaisuwa ta musanman da duk masu sauraron CRI kamar su Shugaba M. Bello gero sokoto, M. Musa Shango da dai sauransu. Sokon gaisuwa ta ga daukacin ma'aikatan sashen hausa na CRI kamar Lubabatu, Umar, Kande, Dan kano da dai duka daukacin masa bada gudunmuwa wajen gudanar shire-shire. Ina yi maku fatan Alkhari ako yaushe."

Sai kuma Salisu Muhammed Dawanau daga Garki Abuja, tarayyar Nijeriya, ya turo mana wasikar da ke cewa, "Daga farkon wannan shekara ta 2008 har zuwa wannan lokaci, hakika mun sheda irin gudunmuwar da sashen Hausa ya bayar wajen fadakarwa da kuma ilmantar da mu masu sauraren sashen. Ko shakka babu, kun yi kokari ainun wajen nuna wa Duniya zahirin gaskiya game da kasar Sin, da kuma jama'ar Sinawa baki daya. A cikin shekarar 2008 ne, duniya baki daya, ta hallara a kasar Sin saboda gasar wasannin Olympic wadda aka kammala cikin annashuwa da murna da kuma jin dadi. Hakika, gasannin da aka kammala za su bar "maki" na dindindin a zukatan mutane masu dumbin yawa a wannan Duniya tamu. A karshe, ina yi mana, baki daya, fatan alheri yayin da muke shirin shiga sabuwar shekara. Ina kuma yi mana fatan samun ci gaba, da kuma kasancewa cikin koshin lafiya a shekarar 2009."

Akwai kuma Abba Muhammad Nuhu, daga Kano, Nijeriya, wanda ya rubuto mana cewa, "shekarar 2008 abubuwa sun faru a cikinta kamar girgizar kasa da ta faru a kasar Sin, wacce aka yi hasarar rayuka masu yawa da kuma dukiyoyi. Allah ya kare aukuwar hakan a nan gaba. A shekara ta 2009, ina yi wa kasar Sin da Nijeriya da kuma sauran kasashen duniya fatan alheri, wadata, koshin lafiya da tattalin arziki mai albarka a ko da yaushe."

Har wa yau kuma, Shehu Abdullahi Dandume, daga garin Funtua, jihar Katsina, tarayyar Nijeriya, ya turo mana wasika, inda ya ce, "ina mai jin dadin sauraren shirye shiryen ku, musanman filin Musulunci a kasar Sin, da kide kide da al'adun kasar Sin, da dai sauransu. Shekara ta 2008 ta kare mun gode wa Allah da muka ga karshenta lafiya, ina mai tunawa da gasar Olympic da aka yi a Beijing, da zaben kasar Amurka wanda Obama ya yi nasara. Ina kuma mai ta'ajibi da rashin da girgiza kasa ta jawo ma jama'ar kasar Sin, data kasar Rasha, Allah ya gafarta ma wadanda suka riga mu, Ya ba mu ikon jure rashin da muka yi."

Ga kuma wasikar Alhaji Wushishi Dan Lami a Minna, jihar Neja, tarayyar Nijeriya, wanda ya rubuto mana cewa, "Ina mai mika sakon taya murna ta sabuwar shekarar 2009 ga daukacin masu saurare a Nijeriya,da Nijar,da Chadi, da Ghana har ma da Kamaru, da fatan Allah ya maimaita mana, amin. Ina kuma rokon Allah da ya kare mu daga duk sharri da bala'u irin ta girgizar kasa, da tsunami, da yake yake da sauransu."

To, amin amin. Mu ma muna fatan a shekarar 2009, Allah zai kare mu daga sharri, da bala'u da fadace-fadace, ya kawo mana zaman lafiya.

A shekarar 2008, sashen Hausa na rediyon kasar Sin ya sami dimbin wasiku daga masu sauraronsa, sai mu ce, masu sauraronmu sun nuna mana goyon baya sosai. A shekarar 2009, za mu ci gaba da kokarin kawo muku shirye-shirye masu fadakarwa da kuma nishadantarwa, muna kuma fatan za ku ci gaba da sauraronmu, ku kasance tare da mu a kullum, ku ci gaba da aiko mana dimbin wasikunku. Kuma a shirye muke a kullum mu amsa tambayoyinku, mu yi hulda da ku. Daga karshe, muna sake taya dukan masu sauraronmu da ke Nijeriya da Nijer da Kamaru da Chadi da Ghana da dai sauran kasashen duniya murnar shiga sabuwar shekara, muna kuma isar da fatan alheri gare ku da iyalanku duka. (Lubabatu)