Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-02 17:28:12    
Matsalar kudi ta duniya ta lalata sana'ar haka ma'adinai ta Afirka

cri
Ana iya samun albarkatun ma'adinai a Afirka, shi ya sa sana'ar haka ma'adinai tana daya daga cikin muhimman sana'o'i na kasashen Afirka. Amma sakamakon illa mai matukar tsanani da matsalar kudi ta duniya ta kawo wa tattalin arziki, farashin kayayyakin karfe da dai makamantansu yana ta samun raguwa, ta haka an lalata sana'ar hakar ma'adinai ta dimbin kasashen Afirka.

Tattalin arzikin nahiyar Afirka yana baya a gwargwado, amma ana iya samun yawan ma'adinai iri iri. Kafin barkewar matsalar kudi, har kullum yawan karuwar tattalin arzikin Afirka ya iya kaiwa kashi 5 cikin kashi dari a 'yan shekarun nan da suka gabata sakamakon farashin kayayyakin ma'adinai mai kauri. Amma yanzu domin raguwar farashin kayayyakin, sana'ar hakar ma'adinai ta duk Afirka ta shiga mawuyacin hali. Domin kiyaye zamansu, wasu wuraren haka sun riga sun dauki matakai kamar rage yawan ma'aikatansu don rage yawan kudaden da suka kashe, wasu kuwa sun yi iyakacin kokari wajen kiyaye ayyukansu ta hanyar rage yawan lokutan aiki da kuma tsawaita yawan lokutan hutu.

Haka kuma sabo da illar da matsalar kudi ke kawowa, farashin tagulla a kasuwannin duniya ya fara raguwa, har ma ya ragu daga dala kimanin 8000 a ko wane ton zuwa dala kimamin 3000 a ko wane ton a cikin watanni shida kawai. Raguwar farashin tagulla sosai ta haifar da babbar illa ga kasar Zambia wadda a kan kiranta "Daular ma'adinin tagulla". Wasu kwararru na Zambia suna ganin cewa, wuraren haka ba su iya samun riba sosai ba sakamakon raguwar farashin tagulla, shi ya sa da kyar masu mallakar wuraren haka suna iya samun kudade wajen haka sabbin ma'adinai. Sabo da haka, karfin hakar ma'adinin tagulla na duk fadin kasar ya ragu, dimbin ma'aikatan hakar ma'adinin sun rasa ayyukansu yayin da masu zuba jari suka janye kudadensu sakamakon rashin imani.

Ban da wannan kuma, rashin bunkasuwar sana'ar ma'adinai shi ma ya haifar da babbar illa ga kasar Congo Kinshasa. Sakamakon raguwar jimlar kayayyakin ma'adinai da aka aika da su zuwa waje, yawan kudaden da gwamnatin kasar Congo Kinshasa ta samu ya samu raguwa a bayyane, sabo da haka ba yadda za a yi sai a dakatar da dimbin shirye-shiryen raya zaman al'umma da hukumomin gwamnatin suka tsara.

Bugu da kari kuma sakamakon matsalar kudi ta duniya, darajar daimon din da har kullum ya kan alamta dukiya ba za ta kai kamar ta lokacin da ba. Tun bayan watan Oktoba na shekarar bara, bukatar da kasuwannin duniya suka yi wa daimon ta samu raguwa a bayyane, haka kuma farashinsa ya ragu da kusan kashi 30 cikin kashi dari.

Game da kasar Botswana wadda ta kasance kamar wata muhimmiyar kasa wajen samar da lu'ulu'u a duniya, an haifar da babbar illa gare ta kwarai sakamakon matsalar kudi. A lokacin da, yawan kudaden da kasar Botswana ta kan samu daga sana'ar haka daimon ya kai sulusi bisa na duk kasar, wanda kuma ya kai kashi 70 zuwa kashi 80 cikin kashi dari bisa na dukkan kayayyakin da ta samar ga kasashen waje. Sana'ar daimon ta taba kawo wa dukiya sosai ga wannan kasa da ta taba fama da talauci, har ma ta sa kasar ta zama daya daga cikin kasashen da suka fi samun saurin karuwar tattalin arziki a duniya. Amma yanzu raguwar kasuwar sayen daimon da kuma raguwar farashin daimon sun haifar da illa mai tsanani ga wannan kasa da ta fi dogara bisa sana'ar haka daimon.

Dimbin kasashen Afirka suna dogara bisa aikin fitar da danyun kayayyai zuwa kasashen waje wajen raya tattalin arzikinsu, shi ya sa ko shakka babu, karuwar farashin danyun kayayyaki na duniya za ta kawo alheri ga wadannan kasashe, amma raguwar farashin za ta yi illa sosai tare su. Sabo da haka ana iya gano cewa, illar da matsalar kudi ta duniya ke kawowa sana'ar haka ma'adinai ta kasashen Afirka ta sake shaida cewa, tattalin arziki na wasu kasashen Afirka ba ya da karfi sosai.(Kande Gao)