Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-01-01 19:33:20    
Zaman wani bajamushe saurayi a birnin Lanzhou na kasar Sin

cri
Bajamushe saurayi da ake kiransa da suna Stephan Mueller wanda ya ke da shekaru 37 da haihuwa yana aiki a kamfanin Netzsch na kasar Jamus. Ya zo birnin Lanzhou na kasar Sin ne a shekarar 2006 sabo da aiki. Bayan da shekara daya da 'yan kai da yake aiki a birnin Lanhou ya fara kaunar wannan birnin dake arewa maso yammacin kasar Sin. Ya ce yana so ya zama a birnin nan Lanzhou a raguwar rayuwarsa.

Kamfanin Netzsch ya shahara kan kera injuna a duniya, yana da tarihin sama da shekaru dari,hedkwatarsa yana jihar Bavaria ta kasar Jamus. A shekara ta 1993 kamfanin Netzsch ya zabi birnin Lanzhou na kasar Sin da ya zama cibiyarsa na kera famfuna. A shekara ta 2006, Mr Stephan Mueller ya zama manaja na sashen kula da 'yan kasuwa na kamfanin fanfo na Lanzhou na Netzsch,daga nan yana zama birnin Lanzhou. Kafin wannan Mr Stephan ya zo nan kasar Sin amma ba birnin Lanzhou ya sa kafa ba sai birane ne da ke bakin teku saboda kamfanin Netzsch yana da sassa da dama a kasar Sin. Stephan ya ce abubuwa masu kyau da dama na kasar Sin sun burge shi kwarai da gaske.

Ya ce abin da ya fi ba shi sha'awa a kasar Sin shi ne bambance-bambancen da kasar Sin ta ke da su, tana da biranen dake bakin teku, ta kuma na da birane na yankin ciki, tana da yankuna masu yanayin sanyi ta kuma na da yankuna masu yanayin zafi. Ina kaunar kasar Sin. Stephan ya ce kwanakin baya ya karanta wata mujjalar da ake kira "times" ta kasar Amurka wadda a ciki an tanadi cewa baki ma'aikata su kan samu wahala wajen fahimtar al'adun kasar Sin da na Indiya da na Rasha, amma Mr Stephan ya ce shi bai sha wahala ba yana jin dadin zaman birnin Lanzhou na kasar Sin.

Tarihin lardin Gansu inda birnin Lanzhou ke ciki da hanyar da mutanen wurin ke bi wajen yin mu'amala suna da nasu halayen musamman. Kowa da kowa na dauke da wasu alamu na al'adu da dabi'unsa, a ganinsa idan wani bako na ketare ya zo wannan yanki, bai kamata ya yi fatan mutanen wuri su bi salonsa na tunani ba.

A birnin Lanzhou, Mr Stephan ya rungumi al'adun kasar Sin da zuciya daya. Da akwai garuruwa da dama a cikin lardin Gansu inda hanyar silk ta daular Han da Tang ta ketare, kuma da akwai shahararrun wuraren tarihi da dama da kayayyakin tarihi na fasaha masu dimbin yawa da ake tanada a cikin ramuka. Hanyar silk ta zamanin gargajiya,hanyar cinikayya ce da ta hada nahiyar Asiya da Turai ta fi daukar hankalin baki masu dimbin yawa. Mr Stephan ya ce ya yi sa'a sabo da abokansa na kasar Sin sun zagayar da shi cikin mota a wuraren tarihi dab da hanyar silk,alal misali, ramukan Mogao da suka kasance tsofaffin al'adu na duniya sun fi shahara sabo da zanen dutse da gumakai masu kyaun gani da suke da su a ciki. Ga shi a yau wurin da ramukan Mogao ke zaune a ciki ya zama wuri mafi daraja da ya so ya nuna wa baki. A duk lokacin da ya gana da aminai na shi kansa ko masu saye na kamfninsa, ya fi so ya zagaya da su a wurin ramukan Mogao da farko.

Mr Stephan ya kan je gidan sinima dokin kallon siniman kasar Sin, duk da haka ya zama dole ya yi kallon sinima da ke babakun Turanci. Kwanan baya ya kalaci wata sinima na kasar Sin mai suna "rana ta fito kamar yadda ta yi kullum", wadda a ciki da akwai labarun kasar Sin da dama na shekaru sittin ko saba'in na karnin da ya shige, ya ce ba ya fahimci dukkan abubuwan da take nufi ba sosai. wata sinima dabam da ya yi kallo mai suna "garin dake cike da sojoji masu dawaki", a ganinsa ya yi kamar da littafin " Hamlet" wanda William Shakespeare ya rubuta, kidan da ake yi amfani da ita a cikin sinima ta fi dadin ji sosai.

A cikin shekara daya kawai,Mr Stepah, wani saurayin da ya zo daga wani al'adun dabam ya saba da zaman wurin. Har ma wasu abokan aikinsa na kamfanin Lanzho na Netzsch sun ce watakila kakani kakaninsa basine.

Miss Zheng Yinjie, wata manaja ta sashen kasuwanci na kamfnin kuma tafinta ce na Mr Stephan. Watakila wannan yarinya ta fi sauran ma'aikatan kamfanin sane da Stephan. Da farko Zheng Yinjie tana aiki tare da Mr Stephan, tana aiki karkashin jagorancinsa. A wancan lokaci Mr Stephan ya kan mayar da takardun da Miss Zheng Yinjie ta shirya domin ta gyara. Ko ma idan ya sami wani kankancin kuskure a cikin takardarta,ya mayar da ita ga Miss Zheng. Da ganin haka Miss Zheng ta gaza fahimtar abin da Stephan ya yi, a ganinta,mayar da hankali kan abubuwan kankanci ba shi da ma'ana. Wani lokacin da suka yi magana kan wata takarda kome dadewarta, nan take Mr Stephan ya iya gano shafinta daga cikin bayyanai masu yawa da ya tanadi a cikin yanar gizo ta internet,wannan ya girgiza Miss Zheng Yingjie. Daga bisani Mr Stephan ya gaya wa Deng Yingjie sirinsa kan yadda ya nada suna ga kowace takarda a injin mai kwakwalwa. Bayan shekara daya ta hadin kai, miss Zheng yingjie ta kara kwarewa wajen aiki, ba wannan kawai ba ta samu ci gaba har ma aka daukaka matsayinta zuwa na manaja. Da waiwayar tarihinta, Miss Zheng Yingjie ta ce ta koyi abubuwa masu yawa daga wajen Mr Stephan.

"A ganina, Mr Stephan ya girmama al'adunmu da dabiunmu. Babu shakka ya zabi wanda ya ke so ya koya. Mu ma mun yi koyi da shi. Ya kawo tasirinsa ga ayyukanmu da dama, ciki har da tunani. Muna cikin kyakkyawan hali na hadin kai. "

Mr Cai Shaojie, mataimakin manaja ne na sashin kasuwancin duniya na kamfanin Netzsch a birnin Lanzhou yana aiki tare da Mr Stephan, har ya zama babban amininsa cikin dogon lokaci. Mr Cai Shaojie ya ce ya fara nuna masa ban girma ne kan wata haliyar da ya ke da ita,wato ya kasance mutumin na farko da ya shiga ofisi kullum. Bisa tsarin ka'idodji na kamfanin, ya kamata ko wane ma'aikaci ya zo aiki daidai da karfe takwas da rabi na safe, amma Mr Stephan ko yaushe ya shiga ofisi karfe takwas daidai. Mr Cai ya yi tsammanin yin kalubale da wannan dabi'ar kiyaye lokacin da jamusawa ke da ita. Duk da haka a shekara daya,sau uku ne kawai Mr Cai ya riga Mr Stephan zuwa ofis.

" Mr Stephan ya cancanci abar misali wajen aiki gare ni. da ya ke kamfanin ba ya sa hankali sosai wajen duba zuwansa a ofis, a ganina shi bai yi makara ba ko sau daya. Ko yaushe ya riga ni zuwa ofis, wurin da ya ke zama ya yi nisa da ofishin."

Mr Stephana yana tare da sinawa ba ma kawai wajen aiki har ma da sauran ayyuka da dama.Ya ce.

Ni da sinawa masu aiki da ni, mu kan fita waje cin abinci tare da yin wasannin badmiton da na balling da wasan iyo da rera wakokin Kara-Ok. Ba na iya,amma ina saurara yadda suka rera wakokin,muriyarsu na da dadin ji sosai. Wasunsu suna so su rera wasu wakoki na al'ada,wasun kuwa sun fi rera wakoki na zamanin baya.

Wani lokaci Mr Stephan ya kan tafi tare da sinawa masu aiki zuwa shagon shan tea inda suka saurara wasan Opera na Qingqiang,wata wasan Opera ta gargajiya da ta fi bazuwa a arewa maso yammacin kasar Sin. Mr Stephan ya ce ko da ya ke ba ya fahinta abin da aka rera ba, amma ina sha'awar kwarewarsu kan wasan opera, yana jin dadin saurara. Mr Stephan ya kan cin abincin taliya mai naman shannu wanda ya fi shahara a kasar Sin tare da abokan aikinsa. Da ya fara da ci irin taliya, zafin abincin ya gagare shi ci. Amma yanzu ya saba, har ma yana kaunar irin abincin. Wani lokacin da ya koma gidansa a Jamus domin hutu, yana cin abincin da mamarsa ta dafa masa wanda ya fi so, ya tuna da irin abincin da ya ci a birnin Lanzhou na kasar Sin. Duk da haka bai gaya mamarsa abinda ke cikin tunaninsa ba domin kada ranta ya baci.

Mr Stephan ya taba tunanin dalilin da ya sa yana zaman jin dadi a birnin Lanzhou na kasar Sin a matsayin bako. A ganinsa baiwar saukin kai da yake da shi ya kawo masa sauki wajen saje da mutanen wurin, a wani bangare ya fi mayar da hankalinsa kan tunani da koyo. Mr Stephan ya ce an fi mayar da hankali kan haliya wajen yin mu'amala tsakanin mutum da mutum. A lokacin da ake mu'amala, an fi mayar da hankali kan haliyar da mutum ya ke da ita da kuma hanyar da ya ke bi wajen yin magana. Wannan ya bambamta da na kasashen yamma. Ya kan mayar da hankalinsa kan irin wadannan abubuwan da sinawa su kan nuna.

" A ganina, kamata ya yi in yi iyakacin kokarina wajen kara fahimtar sinawa masu aiki nawa. Idan ban kulla kyakkyawar dangantak da su ba, in yi kome domin aiki kawai,zan sha wahala. Amma ina jin dadin aiki saboda kasancewar hadin kai mai karfi tsakanina da su."

Ko da ya ke Mr Stephan yana jin dadin zama a birnin Lanzhou na kasar Sin,wani lokaci ya tuna da wurin mahaifinsa. Ya gaya wa ma'aikatan kamfaninsa da cewa gidansa yana cikin wani karamin gari a kasar Jamus. Sunan garin yana da ma'anar garin da ke cikin daji, lalle wurin ne mai kyakkyawar gani sosai. Duk ranar da baubu tsanannin iska da zafin rana, mutanen garin su kan fita waje su shiga tafkin dab da garin su yi ninkayya.da aka tabo maganar wurin mahaifinsa, sai a ga murmushi a fuskarsa.

" Na zo ne daga kudancin kasar Jamus inda da akwai dazuzzuka da duwatsu da kuma tafkuna. Gidana yana cikin wannan yanayi mai kyau. Idan ka kashe rabi ko sa'i daya za ka iya shaka iska mai dadi a cikin dajin "