Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-31 21:33:58    
Cin cakulan yadda ya kamata zai iya ba da taimako wajen tsawaita ran dan Adam

cri
Da ma ana ganin cewa, cakulan tana kunshe da kitse da yawa, shi ya sa cin cakulan zai iya yin illa ga lafiyar jiki, amma manazarta na sashen ilmin kimiyya na abinci na jami'ar fasaha ta Cornell ta kasar Amurka sun bayyana cewa, bisa sakamakon binciken da suka gudanar cikin dogon lokaci, an ce, cakulan wani irin kyakkyawan abinci ne wajen kiyaye lafiyar jiki, haka kuma yana iya taka muhimmiyar rawa wajen tsawaita rai.

Kuma manazarta sun bayyana cewa, sun gudanar da wani bincike ga cocoa da ke cikin cakulan kan halinsa na musamman wajen kiwon lafiya, daga baya kuma sun gano cewa, wani sinadarin da ke hana toshewar hanyar jini wato antioxidant da ke cikin cocoa ya ninka har sau biyu bisa na jar wine, ya kuma ninka har sau uku bisa na koren shayi wato green tea. Dukkan manazartan sun yi mamaki sosai sakamakon abin da suka gano a cikin bincike, kuma sun nuna cewa, kafin su yi wannan bincike, suna kiyasta cewa, ya kamata a iya samun sinadarin antioxidant mafi yawa a cikin koren shayi, amma bayan da suka kwatanta cakulan da jar wine da kuma koren shayi, sun gano cewa, cocoa abinci ne da ke iya hana toshewar hanyar jini sosai.

Sinadarin antioxidant yana iya ba da taimako wajen rage saurin yaduwar kwayoyin sankara da kuma shawo kan barkewar sankara, ban da wannan kuma yana iya ba da tasiri wajen yin rigakafin cututtukan zuciya da sauran cututtukan da ke da nasaba da tsufa. A cikin dukkan sinadarin antioxidant, sinadarin polyphenol ya fi kyau. Cocoa yana kunshe da dimbin irin wannan sidanari, inabi da cherry da kuma jar wine su ma suna kunshe da sinadarin.

Ban da wannan kuma manazarta sun yi bayanin cewa, ana iya samun sinadarin ferrum da magnesium da kuma phosphor da yawa a cikin cocoa, kuma bakar cakulan tana kunshe da sinadarin ferrum mafi yawa idan an kwantanta da farar cakulan.

Amma ya kamata a ci cakulan kamar yadda ya kamata, dalilin da ya sa haka shi ne sabo da ana iya samun kitse da kuma saturated acid a cikin cakulan. Alal misali, garin cocoa gram 100 yana kunshe da kitse gram 24, wanda ya iya samar da calorie 250.

Jama'a masu sauraro, yanzu sai ku huta kadan, bayan haka kuma za mu karanta muku wani bayani kan tsimin makamashi. Yanzu ana yin amfani da wani sabon salon tsimin makamashi a jihar Mogolia ta gida da ke arewacin kasar Sin, kamar yin amfani da gurbataccen ruwa wajen samar da wutar lantarki, da kuma sarrafa abubuwa marasa amfani da aka samu bayan da aka kone kwal domin su zama siminti. To, a cikin shirinmu na yau, za mu shiga jihar Mongolia ta gida domin ganin yadda suke tsimin makamashi da kuma kiyaye muhalli.