Bisa ci gaban zamantakewar al'umma, dimbin ma'aikata mata suna gudanar da ayyukansu a fannin kimiyya da fasaha a duk duniya. A kasar Sin kuma, ana iya samu mace daya a cikin ko wadanne ma'aikata uku a fannin kimiyya da fasaha. To a cikin shirinmu na yau, za mu leka Sinawa mata masu ilmin kimiyya.
Mao Jianqin, wata forfesa ce ta jami'ar koyar da ilmin zirga-zirgar sararin samaniya ta Beijing. Bayan da ta gama karatunta daga jami'ar da kuma jami'ar Peking a shekaru 60 na karnin da ya gabata, ta kaddamar da aikinta a fannin nazarin ilmin kimiyya na tsaron kasa, kuma a shekara ta 1985, ta zama daya daga cikin masu digirin dakta na rukunin farko bayan kafuwar Jamhuiriyar Jama'ar Sin a shekara ta 1949. A matsayinta na wadda ta ganam ma idonta, Madam Mao ta shaida girman kungiyar ma'aikata mata a fannin kimiyya da fasaha. Kuma ta bayyana cewa,
"Ma'aikata mata a fannin kimiyya da fasaha da kasar Sin ta horar bayan da ta samu 'yancin kai ya zarce wadanda kasar ta horar a da ko a fannin matsayinsu na zaman al'umma, ko a fannin yawansu. Musamman ma bayan da aka bude kofa ga kasashen waje da kuma yin kwaskwarima a gida, yawan ma'aikata mata da ke gida da waje a wannan fanni yana ta karuwa."
Gaskiya ne, bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin a shekara ta 1949, dimbin mata masu ilmin kimiyya da ke samun girmamawa a gida da waje kamar Mao Jianqin sun bullo. Bisa kididdigar da gwamnatin kasar Sin ta bayar, an ce, ya zuwa yanzu, ana iya samun ma'aikata mata iri daban daban a fannin kimiyya da fasaha a kasar Sin fiye da miliyan 10, wanda ya kai kusan kashi 37 cikin kashi dari bisa yawan dukkan ma'aikata a fannin. Madam Liu Shu, tsohuwar shugabar kungiyar kimiyya da fasaha ta kasar Sin da ta taba shugabantar rahoton nazari kan ma'aikata mata a fannin kimiyya da fasaha na kasar Sin, ta bayyana cewa, yanzu wannan rukunin mutane yana cikin kyakkyawar halin bunkasuwa. Kuma ta ce,
"Shekarun mata masu ilmin kimiyya da fasaha da haihuwa ba yawa, shekarun yawancinsu bai kai 50 da haihuwa ba, kuma yawan mata masu neman digiri na biyu da ke cikin jami'o'in kasarmu ya samu karuwa sosai, wanda ya shaida cewa, ya kasance da isassun ma'aikata mata masu ilmin kimiyya da fasaha a matsayin 'yan ko-ta-kwana a kasar Sin."
Bullar dimbin ma'aikata mata a fannin kimiyya da fasaha tana da nasaba da namijin kokarinsu, haka kuma ba a iya raba batun da ci gaban zaman al'ummar Sin da kuma kyautatuwar matsayin mata ba. A kasar Sin, mata suna iya samun hakki iri daya da maza a fannin samun ilmi, wanda ya kafa tushe mai inganci gare su wajen kara ilminsu a fannin kimiyya da fasaha. Wang Yanling, shugabar jami'ar koyar da ilmin ayyukan gona ta lardin Henan ta bayyana cewa,
"A 'yan shekaru nan da suka gabata, yawan dalibai mata ciki har da masu neman digiri na biyu da ke cikin dalibai ya samu karuwa sosai wanda ba a taba ganin irinsa a tarihi ba. Yawan dalibai mata da ke cikin jami'o'in duk fadin kasar Sin ya kai kashi 47.08 cikin dari, a ciki yawan mata masu neman digiri na biyu ya kai kashi 46.02 cikin dari yayin da wannan jimla ta kai kashi 32.57 cikin dari ga mata masu neman digiri na dakta."
Ban da wannan kuma abin farin ciki shi ne, a 'yan shekarun nan da suka gabata, kasar Sin ta dauki jerin matakai wajen kare da kuma sa kaimi ga bunkasuwar ma'aikata mata a fannin kimiyya da fasaha. A shekara ta 2007, kungiyar ma'aikata mata a fannin kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta kafu. Kuma ta hanyar yin cudanya da juna, da ba da shawara, mata suna ba da muhimmin amfani wajen ci gaban kimiyya da fasaha da tattalin arziki da kuma zamantakewar al'umma. (Kande Gao)
|