Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-29 16:10:33    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri
---- kwanan baya, ofishin inshorar zaman al'umma na hukumar kudi ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta ta kasar Sin ya sanar da cewa, a shekarar da muke ciki baitulmalin gwamnatin tsakiya ya kara ware kudin taimako da yawa wajen aikin likitanci da ake yi a yankunan noma da kiwon dabbobi na jihar, matsakaicin yawan kudin taimakon da kowane manoma da makiyaya na jihar ya samu domin samun damar ganin likita ya karudaga kudin Sin Yuan 100 zuwa 140 a shekara.

An ce, tun shekarar 2006 zuwa yanzu, wannan ya zama karo na 7 ke nan da baitulmalin gwamnatin tsakiya ya daga ma'aunin kudin taimako da aka bayar ga manoma da makiyaya na jihar Tibet domin samun damar ganin likita a kyauta yawa wajen aikin likitanci.

An fi nuna gatanci ga yankunan noma da kiwon dabbobi na jihar Tibet wajen tafiyar da tsarin likitanci a kasar Sin, kowane manomi da makiyayi ya bada kudi a kalla Yuan 10 ga hukumar likitanci a shekara, zai iya gabatar da rasidi kan kudin da ya kashe wajen jiyya lokacin da yake kwantawa a asibiti domin a maida masa kudaden da ya kashe fiye da kashi 60 cikin 100. Don su manoma da makiyaya wadanda ba su shiga wannan tsarin likitanci ba kuwa su ma an ba su kudin taimako kadan wajen likitanci. Yanzu manoma da makiyaya na jihar Tibet wadanda yawansu ya kai kashi 90 cikin 100 suka shiga wannan tsarin likitanci.

---- Cikin shekaru 8 da suka wuce wato tun shekarar 2000 zuwa yanzu, kasar Sin ta riga ta ware kudin Sin Yuan biliyan 10.6 domin tafiyar da ayyukan gyare-gyare ga kogin Tarim da ke jihar Xinjiang ta kasar, ta yadda fidin tsire-tsire na halitta da ke bakin kogin Tarim ya karu har ya kai murabba'in kilomita 180, wato ya nika sau 5 idan an kwatanta shi da na kafin shekaru 8 da suka wuce.

Kogin Tarim kogi ne mafi tsawo kuma maras mafita ta teku a kasar Sin, sabo da sauye-sauyen yanayi da ayyukan raya kasa da aka yi da sauri fiye da yadda ya kamata a mafarin kogin, shi ya sa kogin ya kafe a wasu sassa nasa, kuma tsire-tsire sun yausasa a wurare masu fadi, muhallin halittu kuma yana lalacewa. Bayan gyare- gyaren da aka yi, yanzu yawan nau'o'in tsire-tsiren da ke kasance a bakin kogin Tarim ya riga ya karu daga 17 zuwa 46, ba ma kawai an samu sakamako wajen kyautata halittu masu rai ba, har ma an kara samun sakamakon tattalin arziki sosai.