Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-29 16:09:22    
Wakar Changdiao wakar da ke shiga zuciya ce ta kabilar Mongoliya

cri
Makiyaya masu yawo da dabbobi na kabilar Mongoliya wadanda suke zama a babban filin ciyayi da ke arewacin kasar Sin daga kakanni zuwa kakanni, kuma suna da al'adun musamman na filiyan ciyayi. Mutane sukan ce, kabilar Mongoliya tana da abubuwa 3 masu daraja wato filin ciyayi da doki mai kyau da wakar gargajiya da ake kira Changdiao. Jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau za mu ja ku zuwa wannan babban filin ciyayi don jin yadda jama'a suke rera wakar Changdiao mai shiga zuciya ta kabilar Mongoliya.

Jama'a masu sauraro, wakar da kuke saurara wakar gargajiya ta Changdiao ce ta kabilar Mongoliya wadda wani yaro mai shekaru 10 da haihuwa mai sunan Batutulaga ya rera. Yaron nan ya fito ne daga Gundumar Ujimqin ta gabas ta jihar Mongoliya ta gida mai ikon tafiyar da harkokin kanta, tun yarantakarsa ya fara koyon fasahar rera wakokin Changdiao daga wajen kakarsa, muryarsa tana da dadin ji, rera wakoki ya zama abu mai farin ciki ne gare shi.

Ko sabo da filin ciyayi ne ya ba wa 'yan kabilar Mongoliya hazikanci, ko kuma sabo da gadon al'adun kiwon dabbobi da suka ci daga wajen kakanninsu, shi ya sa rera waka ya zame musu jiki, duk wanda ya sa kafa a filin ciyayi, ba wanda bai jiku ba sabo da muryar wakokin gargajiya musamman ma wakokin gargajiya na Changdiao na kabilar Mongoliya.

Wakar gargajiya ta Changdiwo wadda ake kiranta "wakar rukun filin ciyayi" ta zama wata irin fasahar murya ta musamman ta kabilar Mongoliya, ba kawai tana da dajin ji ba, kuma tana da dogon tarihi. Mr. Man Dufu, manazarci na cibiyar binciken kimiyyar zaman al'ummar jihar Mongoliya ta gida wanda ya shahara wajen binciken wakar Changdiao ya bayyana cewa,

"Al'adun kiwon dabbobi wajibabben abu ne da ya kasance daga zaman al'ummar kiwon dabbobi a daji, daga cikin su da akwai kide- kide, musamman ma ga wakokin Changdiao wadanda suke wakiltar dukkan al'adun kiwon dabbobi a daji. Halin musamman na wannan al'adu shi ne kiyaye cudanyar mutane da sauran halittu cikin jituwa, wakar Changdiao kuma ta ba da misali mafi kyau a wannan fanni, kuma ba safai akan ga irin al'adu kamar haka ba a duniya."

Tsohuwa Hada tana zama a filin ciyayi tun kakanninta, tana rera wakokin gargajiya na Changdiao cikin duk zaman rayuwarta, ko da yake yanzu tana da shekaru 68 da haihuwa, amma tana ci gaba da rera wakokin, tana kaunar wakokin Changdiwo daidai kamar yadda take kaunar filin ciyayi. 'Ya'yan tsohuwa kuma suna son rera wakokin Changdiao, wannan ya faranta ran tsohuwa kwarai, amma tana dan damuwa sabo da bisa ci gaban zaman al'umma na zamani, hanyar da makiyayan kabilar Mongoliya suke bi wajen zaman rayuwa da aikin kawo albarka tana ta sauyawa. Ban da wannan kuma, yanzu ana yin zaman nishadi a filin ciyayi ta hanyoyi da yawa, shi ya sa wakar Changdiao take fuskantar matsalar rasa muhallin halitta da take dogara a kai.

Kan al'amarin da ake ciki kamar haka, gwamnatin kasar Sin ta mai da muhimmanci kan kiyaye wakar Changdiao. A shekarar 2005, hukumar UNESCO ta MDD ta zabi wakar Changdiao ta kabilar Mongoliya kuma ta shigar da ita cikin "sunayen abubuwan 'yan adam da suke wakiltar abubuwan baki da wadanda ba na kayayyaki ba na al'adun tarihi da aka gada daga kakanni zuwa kakanni". Mr. Li Xunjie, shugaban hukumar al'adu da wasannin motsa jiki ta yankin Xilingul ya bayyana cewa,

"A kowace shekara mukan shirya gasannin rera wakokin Changdiao na duk yankinmu ko kuma na duk kasar Sin baki daya, mawakan Changdiao da suka zo daga larduna da jihohi daban-daban na duk kasar sun taru a gun gasannin da aka shirya a yankin Silingul, ta haka ne muka ci gado da kuma yadada wakar Changdiao tare."

Kwanan bayan an shirya wata gasar rera wakokin Changdiao a gundumar Ujimqin ta gabas da ke yankin Xilingul. Akan ce gundumar Ujimqin ta gabas garin wakokin Changdiao ne na kasar Sin, a nan daga yara masu shekaru 8 da haihuwa har zuwa tsofaffi masu shekaru 80 da haihuwa dukkansu sun kware wajen rera wakokin Changdiao na kabilar Mongoliya.