Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-29 12:18:23    
Israela ta ci gaba da kai hare hare ta jiragen sama a zirin Gaza

cri

Assalamu alaikum jama'a masu sauraro, barkanku da war haka, barkanmu da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na duniya Ina labari. A cikin shirinmu na yau za mu gabatar muku da wani bayanin da wakilin gidan rediyo na kasar Sin ya kawo mana kan hare haren da Isra'ila ta ci gaba da kaiwa kan zirin Gaza.

A ran 28 ga wata, an shiga kwana na biyu a cikin matakin sojan da sojojin tsaron kasa na Isra'ila suka dauka dake da lakabi haka"Cast Lead" kan kungiyar Hamas a zirin Gaza. A wannan rana sojojin Isra'ila sun ci gaba da kai hare hare ta jiragen saman yaki da rokoki kan ayyukan kungiyar Hamas da kuma dakarunta. Halin da ake ciki a zirin Gaza da ke kara tsamari ya cigaba da daukar hankalin duniya.

A ran 28 ga wata, cikin duhu jiragen saman yaki na Isra'ila sun sake jefa bama bamai a zirin Gaza,, sun fara aikinsu na soja a kwana na biyu. Bayan gari ya waye, sojojin Isra'ila sun canza salonsu na kai farmaki da manyan makamai zuwa kanana. Yayin da kakakin rundunar sojan tsaro ta Isra'ila Avital Leibovitz ke hira da manema labarai, ta bayyana cewa

"Jiya mun kai farmaki kan ayyuka hamsin na kungiyar Hamas,yawan ayyukan da za mu kai hari da jiragen saman yaki a yau sun yi daidai da na jiya.A cikin harinmu na karshe a yau muna so mu rushe ramuka guda 40 da jiragen saman yaki. Dukkan ramuka 40 suna a tsakanin zirin Gaza da yankin kasar Massar, sun kasance hanyoyi ne da dakarun Falastinawa ke amfani da su wajen yin fasa kwaurin makamai da rokoki, haka kuma hanyoyin ne da 'yan ta'adda ke amfani da su wajen kai da kawowa tsakanin zirin Gaza da Massar da kuma samun horo a sauran kasashe.

Avital Leibovitz ba ta bayyana anihin adadin yawan Falastinwa da suka rasa rayukansu  ba sakamakon kai hare haren jiragen saman yaki na Isra'illa ba, ta jaddada cewa mutanen da suka rasa rayuka yawancinsu dakaru ne na kungiyar Hamas. Duk da haka labaran da suka zo daga ma'aikatar kiwon lafiya ta zirin Gaza sun yi nuni da cewa har zuwa yanzu hare haren jiragen saman yaki na Isra'illa sun haddasa a kalla mutuwar mutane 296 da wasu 950 da suka jikata.

Kakakin ofishin firayim ministan Isra'ila Mark Regev a ran 28 ga waa ya fayyace cewa majalisar ministoci ta Isra'illa ta yanke kudorori uku masu muhimmanci kan batun Gaza a wannan rana. Ya ce

"na farko Isra'ila ta kafa dokar ta-baci a kudancinta domin tinkarar halin kaka-nika-yi da ta sami kanta a ciki a halin yanzu, na biyu ta kafar dokar ta baci ta fannin tattalin arziki domin tabbatar da samar da  abinci da sauran kayayyaki yadda ya kamata, na uku ta yi kira ga majalisar dokoki ta Isra'illa da ta amince da bukatunta na daukar sojoji masu share fage. A ganin Isra'ila wannan halin da take ciki ba zai kammala nan da nan ba, da akwai wajibcin daukar sojoji masu share fage."

Ma'aikatar tsaron kasa ta Isra'ila ta ce shirin daukar sojojin share fage dubu 6 da dari bakwai, shirin da ake yi domin magance yiwuwar karin kamarin lamari a zirin Gaza. Bisa labaran da aka bayar, an ce an riga an tura darurruwan dakaru da sojojin tankokin yaki zuwa yankin iyaka da zirin Gaza domin share fage ga sojojin Isra'ila da su dauki mataki kan zirin Gaza ta kasa.Ministan tsaron Isra'ila Barak ay ce ba a kawar da yiwuwar kai hari kan zirin Gaza daga kasa ba. Duk da haka kakakin sojojin Isra'ila Leibovitz ta ce kai hare hare da jiragen sama muhimmin mataki ne da Isra'ila ta dauka kan zirin Gaza. Ta bayyana cewa

" ba mu da shirin yin amfani da dakarun kasa tukuna, a halin yanzu muna amfani da jiragen saman yaki ne domin kai hari. Kan batun daukar sojoji masu share fage,abu mafi muhimmanci shi ne  shirin ya samu amincewar majalisar ministoci, sa'an nan ya samu amincewar ma'aikatar tsaron kasa, kamata ya yi mu share fage kafin kayyadaden lokaci. Duk da haka ba mu dauki mutum ko daya ba tukuna,zabi ne kawai. Idan ya zama wajibi, za mu yi amfani da sojoji masu share fage."

Kan hasarar rayukan Falastinawa masu yawa da hare haren jiragen saman yaki na Isra'ila suka haddasa, shugaban hukumar Falastinu Abbas wanda ke ziyara a birnin Alkahira na Massar ya bayyana a fili cewa yana adawa da matakin soja da Isra'ila ta dauka,ya yi fatan a gaggauta  maido da  tattaunawa domin tabbatar da tsaron mutanen Falastinu.(Ali)