Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-26 16:11:08    
Ra'ayoyin masu sauraro a kan manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da Sin ke aiwatarwa

cri
Tun daga ran 18 zuwa ran 22 ga watan Disamba na shekarar 1978, an gudanar da cikakken zama na uku na kwamitin tsakiya na 11 na jam'iyyar kwaminis ta Sin a birnin Beijing. A gun wannan taro mai matukar muhimmanci a tarihin jam'iyyar kwaminis ta Sin, an gabatar da sabuwar hanyar gurguzu da ke da sigar musamman ta kasar Sin, wadda kuma ta bude wani sabon babin na yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga kasashen waje. A cikin shekaru 30 daga bisani, kasar Sin ta sami manyan nasarori a wajen daukaka cigaba a fannoni daban daban, wadanda suka burge duniya kwarai da gaske. A cikin shekarun nan 30 da suka gabata, kasar Sin ta mai da hankali a kan bunkasa tattalin arziki, kuma ta sauya tsarin tattalin arzikinta daga wanda aka riga aka tsara zuwa na kasuwanci. Ban da wannan, Sin ta kuma yi ta inganta gyare-gyaren tsarurrukan siyasa da al'adu da zaman al'umma da dai sauransu, har ma ta cimma samun wani sabon tsari mai inganci da ya dace da halin da take ciki. Sakamakon manufar, a cikin shekaru 30 da suka gabata, yawan GDP na kasar Sin ya yi ta karuwa da kusan kashi 10% a kowace shekara, kuma matsayin tattalin arzikinta ya dagu har ya zama na hudu a duniya. A cikin shekarun nan 30 da suka gabata, yawan kudaden shiga da jama'ar kasar Sin suke samu ya yi ta saurin karuwa, wato matsakaicin kudaden da mazauna birane da garuruwa na kasar Sin suke iya kashewa ya karu daga yuan 343 zuwa 13786, sa'an nan, yawan mazauna kauyuka da ke fama da talauci ya ragu daga miliyan 250 zuwa miliyan 14. A sa'i daya kuma, da ma kasar Sin ta kasance kofarta a rufe, amma a cikin shekaru 30 da suka gabata, Sin ta fara bude kofarta ga kasashen duniya daga dukkan fannoni, ta kulla kyakkyawar huldar aminci da hadin gwiwa da kasashen duniya, tana mu'amala da su ta fannoni daban daban, ciki kuwa har da kawayenta na Afirka.

To, ga shi kwanan baya, masu sauraronmu su ma sun rubuto mana ra'ayoyinsu game da manufar yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje da Sin ta aiwatar. Yanzu sai a gyara zama a saurari ra'ayoyinsu.

Malam Salisu Muhammed Dawanau, daga Garki Abuja, tarayyar Nijeriya ya ruwaito mana cewa, "yayin da wasu kasashen Duniya suka dauki shekaru masu yawan gaske wajen ganin sun cimma nasarori na game da ci gaba, kasar Sin kuwa shekaru 30 kacal ta dauka kuma duk duniya mun sheda da yin na'am da bunkasuwar da kasar Sin din ta yi a wadannan shekaru ta hanyar bude kofofinta masu alfarma ga kasashen waje.

Ko shakka babu, Duniya baki daya na sane da irin bunkasar da kasar Sin ta yi. A cikin wadannan shekaru 30, Sinawa sun yi fice sosai, kuma sun samu riba mai dumbin yawa. Harkar sufuri da kimiyya da fasaha da noma da ilimi duk sun ingantu sosai. Kana, tsarin bude kofa ga kasashen waje ya haifar da shiei da fice cikin sauki. Tsarin ya haifar da inganci da bunkasuwar karfin tattalin arziki ga kasar Sin.

Hakika, hangen-nesa wani yanayi ne da kan haifar da cin moriya mai tsoka, da kuma samun riba mai dumbin yawa, kuma ya kan haifar da bunkasa sosai. Saboda haka, kasar Sin duk ta cimma wadannan buri nata a wadannan shekaru 30, sai dai kawai sauran kasashen Duniya (masu niyyar ci gaba) su bayar da himma don yin koyi da kasar Sin don su ma su cimma nasarorinsu kamar yadda kasar Sin ta cimma nata.

Babu shakka, yayin da muka shiga wannan karni, duniya baki daya ta juya akalar hankalinta ya zuwa ga kasar Sin don sanin asalin sirrin da ke tattare da samun nasarorin kasar Sin, ina kyautata zaton shine yasa miliyoyin mutane su ka ziyarci kasar Sin a lokacin gasannin Olympic da aka kammala watannin baya a Beijing.

Na yi amanna, kasar Sin da Sinawa baki daya za su dada samun karbuwa sosai a Duniya (kamar yadda ake gani yanzu)."

Sai kuma a cikin sakonsa, shugaba Muhammed Idi Gargajiga daga kungiyar masu sauraronmu ta Gombawa CRI Listeners' Club, ya ce, "Tun bayan da sabuwar kasar Sin da kasashen Afrika suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu yau da shekaru fiya da 50 da suka shige jama'ar Sin da Afrika sun hada kansu, su goyi bayan juna su tsaya tsayin daka kan ka'idoji da ra'ayoyi na yin mu'amala cikin sahihanci da yin zaman daidai wa daida da moriyar juna da kuma hada kai da hada guiwa don samun bunkasuwa tare, sun rika zurfafa zumunci a tsakanin su, shi ya sa har kawo yanzu suke samun sakamako mai yawa.

A hakikanin gaskiya kasar Sin ta zama madigar tafiya kuma madigar dawowa ga kasashen Afrika domin har kullum kasar Sin tana nuna goyon baya na gaskiya da kuma nuna kyawawan manufofi tare da jigajigan misalai da nuna namijin kokari kan kasashen Afrika, wajen taimakawa kasashen Afrika ta fannoni daban daban, domin dora tubali na samar da sauki da samar da tsabtatacciyar rayuwa mai inganci ga al'ummar kasashen Afrika.

Ina iya tunawa cewa cikin shekara ta 2007, wani kamfani dake karkashin hukumar bincike ta sararin samaniya ta kasar Sin ya fitar da tauraron dan adam zuwa kasar Nigeria, kuma wani kamfani mai aikin gina hanyar dogo na kasar Sin ya zo kasar Nigeria domin yin aikin garanbawul ga hanyoyin dogo na kasar Nigeria.

Kasar Sin ta dauki wasu daga cikin manyan Harsunan kasashen Afrika domin yin amfani da su wajen watsa shirye- shirye da harsunan kasashen Afrika a babbar tashar gidan Radiyonta domin taimakawa jama'ar Afrika su kara sanin irin halin da kasar Sin ke ciki a kullum da ma na duniya baki daya.

Haka kuma daga ran 28 ga watan janairu na shekarar 2006 kasar Sin ta kafa tashar gidan Radiyo na FM 91.9 ta farko a kasar kenya, kuma kasar Sin ta sake kafa tashar gidan Radiyo ta FM na biyu a kasar Niger tare da gudanar da aikin gina hasumiyar samar da ruwa a kasar Niger.

Babu shakka duk irin wadannan muhimman abubuwa da kasar Sin ta taimaka da su ga kasashen Afrika za su kara taimakawa kwarai da gaske wajen warware Tangarda da Tarnaki na Tangadin da Tattalin arzikin kasashen Afrika ke ciki a kullum domin kasashen Afrika su kai ga shiga sabon mataki da kuma bude sabon babi na tarihi tare da aminiyarsu kasar Sin".

To, malam Salisu Muhammed Dawanau da Muhammed Idi Gargajiga da dai sauran masu sauraronmu da suka rubuto mana, wadanda ba mu samu damar karanta sakonninsu duka ba sabo da karancin lokaci. Sakonninku sun burge mu sosai, kuma muna muku godiya da ruwaito mana su, mun gode, kuma muna fatan za ku ci gaba da mai da hankali a kan bunkasuwar kasar Sin da cigaban huldar da ke tsakaninta da kasashen Afirka a nan gaba. (Lubabatu)