Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-23 19:34:15    
Birnin Yibin da ke gabar kogin Yangtse

cri

Jama'a masu sauraro, barkanku da sake saduwa da ku a cikin shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici wato 'Kai ziyara ga kyakkyawan lardin Sichuan'. Ni ce Tasallah da ke jan akalar wannan shiri. Yau ma bari mu kai ziyara ga birnin Yibin da ke gabar kogin Yangtse. Amma kafin mu soma shirinmu na yau, kamar yadda mu kan yi a da, ga wasu tambayoyi 2 da muka yi muku, da farko, wane ne fim din da ya sami lambar yabo ta Oskar, kuma an yi shi ne a tekun gorori na Shunan? Ta biyu kuma, ko tsohon garin Lizhuang yana kasancewa a gabar kogin Yangtse? To, yanzu bari mu shiga wannan birni na Yibin!

Mai yiwuwa ne masu sauraro kun tuna da fim din mai suna 'Crouching Tiger, Hidden Dragon' da ya sami lambar yabo ta Oskar a fannin fina-finai da ba na Turanci ba a shekarar 2001. A cikin fim din nan, wata fada da aka yi a cikin tekun gorori ta fi samun amincewa. Tekun gorori da ke cikin wannan fim shi ne tekun gorori na Shunan da ke kudu maso gabashin birnin Yibin na lardin Sichuan. An mayar da shi daya daga cikin tekunan gorori mafiya kyan gani a kasar Sin.

A cikin wannan wurin yawon shakatawa na tekun gorori na Shunan mai fadin murabba'in kilomita 120, a ko ina ana iya ganin kwarran gorori, ana iya jin kukan tsuntsaye, ana iya ganin magangarar ruwa da kuma ruwan da ke gangara sannu sannu, babu zafi a nan. Tun zamanin da, gora tana babban matsayi a cikin zukatan Sinawa, haka kuma gora ita ce alamar al'adun kasar Sin da kuma al'adun gabashin duniya. Tsawon kasancewar tekun gorori na Shunan ya wuce dubu guda, shi ne daga daga cikin mafarin al'adun gora na kasar Sin. Bai Hao, shugaban sashen kula da wurin yawon shakatawa na tekun gorori na Shunan ya yi karin bayani cewa, "Wannan wurin yawon shakatawa na da halayen musamman 3 a fannin kiwon lafiya, wato more ido da gorori masu yawan haka, da kyautata huhun mutum bisa danyun iska mai cike da iskar Oxygen, da kuma cin abinci mai dadi da aka dafa da gorori."

Yayin da aka yawo a titunan da ke kunkurmin daji na gora, ana iya ganin gorori masu dubu da masu haske da kuma tsiren gorori da ke gindin gororin. Bayan ruwan sama, a cikin kungurmin daji na gora, ana yin tsit a wajen, sai dai amon da gororin ke yi kawai za a iya ji a yayin da suka yi girma. A lokacin da ake tafiya a nan, ba zato ba tsammani ana iya karo da zomaye da sauran dabbobin daji.

Akwai wani tabki mai fadin murabba'in mita dubu 40 a tekun gorori na Shunan, mazauna wurin na kiransa 'Haizhonghai', wato tekun da cikin cikin tekun gorori. A lokacin da ake tukin kwale-kwale a kan tabkin, ana iya ganin ruwa mai tsabta da kwarran gorori da kuma fararen gaurakin da suka tashi sannu a hankali a tsakanin gororin. Mr. Chen, wani mazauni wurin ya gaya mana cewa, "Fim din mai suna 'Crouching Tiger, Hidden Dragon' aka yi shi a wannan tekun da ke cikin tekun gorori. In mai yawon shakatawa bai zo wannan tabki ba, to, zai yi da na sani sosai. Bugu da kari kuma, ya iya shan kwafi daya na shayi mai dadi a wajen. Shayin din nan na da kamshi sosai. Mun hada ruwan da muka samu a wurin da kuma shayin da muka samu a babban tsauninmu tare. Ruwan shayin na da dadi sosai."

Tekun gorori mai fadi haka ya sanya matafiyan da suka zo daga nesa su kwantar da hankulansu, su kuma manta da komawa gida. Feng Hui, wanda ya zo daga birnin Chengdu, babban birnin lardin Sichuan ya bayyana mana cewa, "Bayan da na zo nan tekun gorori na Shunan, na ji sakin jiki saboda ganin kyawawan gorori masu yawan haka. Na ji kamar ina cikin aljanna. Baya ga gorori, na iya tukin kwale-kwale a tabki. Na iya dandana abinci mai dadi. Ban ji damuwa ba ko kadan, na ji farin ciki sosai."

Garin Lizhuang da ke bayan birnin Yibin ya shahara ne kamar yadda tekun gorori na Shunan yake kasancewa. Garin Lizhuang na gabar kudu ta kogin Yangtse, shi ne wani gari ma tsawon shekaru 460 da ya yi suna ne a fannin al'adu. Yanzu a wannan garin da ke gabar kogi, ana adana cikakken jerin gine-ginen gargajiya, wanda ya nuna halin musamman na gidajen mazauna kudancin Sichuan daga tsakiyar karni na 14 zuwa farkon karni na 20. Garin Lizhuan muhimmin wurin yawon shakatawa ne da kada matafiya su manta da kai masa ziyara.

Ban da albarkatun halittu da na al'adun mutane masu yalwa kuma, masu yin bulaguro suna iya kara fahimtarsu kan halin musamman na kananan kabilu a birnin Yibin. A gundumar Xingwen da ke kudu maso gabashin birnin Yibin, tekun duwatsu na Xingwen da ke cikin wurin shakatawa na tsarin kasa na duniya ya shahara sosai, inda akwai tekun duwatse na Xingwen mai girma da kuma wurare masu ban mamaki ta fuskar tsarin kasa. Dadin dadawa kuma, gundumar Xingwen wuri ne da mafi girma da aka fi samun 'yan kabilar Miao a lardin Sichua.

Abin da aka lura da shi shi ne gundumar Xingwen wuri ne na karshe da 'yan wata tsohuwar kabila wato Bo a lardin Sichuan suka taba zama. Yang Ting, wata 'yar kabilar Miao tana aikin mai jagorar masu yawon shakatawa a wurin yawon shakatawa na tekun duwatsu na Xingwen, ta yi mana karin bayani cewa, kabilar Bo ita ce wata karamar kabila mai dogon tarihi a kudu maso yammacin kasar Sin. Gundumar Xingwen wuri ne da 'yan kabilar Bo suka gina fadarsu a ciki, haka kuma, shi ne wuri na karshe da 'yan kabilar Bo suka taba zama. A wurin yawon shakatawa na tekun duwatsu na Xingwen, in an daga kansa, sai ya iya ganin abubuwan tarihi na al'adu da 'yan kabilar Bo suka ba mu, wato akwatunan jana'iza da aka rataya a hayi. Madam Yang ta ce, "Akwatunan jana'izza da muka gani a yanzu aka rataya su a hayi ne ta hanyar binnewa a kan katako a hayi. Matsayin akwatunan jana'izza na da nasaba da mukaman da matattu suka taba tsayawa. Akwatin jana'izzar babban mutum yana wuri mai tsayi a hayin. Hanyar binnewa a kan katako a hayi ita ce an haka ramuka a hayi, daga baya, an ajiye katako a ramukan, an sanya akwatin jana'iza kan wadannan katako. Dalilin da ya sa akwatin jana'izar da kuka gani a yau bai rube ba har tsawon darurukan shekaru shi ne domin an samar da shi da katako na aji na farko, wato katakon Nanmu."

'Yan kabilar Bo na zamanin da sun bace a karni na 16 da suka wuce, sun rikitar da tunanin na baya da su a fannoni da yawa, har ma ya zuwa yanzu mutane na zamanin yanzu ba su iya gane ba. Donme 'yan kabilar Bo sun rataya akwatunan jana'izzarsu a hayi mai tsayi? Ya zuwa yanzu yana kasancewa sabani a tsakanin masana a wannan fanni. Mr. Mao Jianhua, wani masani mai ilmin al'adun gargajiya kuma shehun malami da ke aiki a jami'ar Sichuan ya yi bayani cewa, wani zance yana da kan gado. Ya ce,"Wannan hanyar rataya akwatunan jana'izza a hayi ita ce al'adar gargajiya mai halin musamman a cikin tsarin al'adun gargajiya na kasar Sin a fannin binnewa. A tsakanin masana masu ilmin nazarin abubuwan tarihi, akwai wani zance cewar, an rataya akwatunan jana'ina a hayin da ke kusa da ruwa, a maimakon hayin da ke sauran wurare. Dalilin da ya sa haka shi ne domin 'yan kabilar Bo sun yi fatan cewa, fatalwarsu za ta iya bin sawun kakanin-kakaninsu. Saboda sun gaskata cewa, kaka kakaninsu sun zo nan ne daga bangare na kasa na kogi, shi ya sa suka yi fatan cewa, bayan mutuwarsu, za su iya bin sawun kakanin-kakaninsu, za su iya komawa wuraren da kakanin-kakaninsu suka taba zama."

To, masu sauraro, karshen shirinmu na yau na gasar kacici kacici ta 'Kai ziyara ga kyakkyawan lardin Sichuan' ke nan. Amma kafin mu sa aya ga shirinmu na yau, bari mu maimaita tambayoyi 2 da muka kawo muku a farko shirinmu na yau. Da farko da farko shi ne, wane ne fim din da ya sami lambar yabo ta Oskar, kuma an yi shi ne a tekun gorori na Shunan? Ta biyu kuma, ko tsohon garin Lizhuang yana kasancewa a gabar kogin Yangtse?