A matsayinta na wata fasahar da ke hada da ilmin kimiyya iri daban daban, fasahar zirga-zirgar sararin samaniya tare da daukar mutane ta shaidar da kwarewar kimiyya da fasaha da wata kasa ke da ita daga manyan fannoni. A shekara ta 1999, kasar Sin ta yi gwajin farko na harba kumbo ba tare da daukar mutane ba, a shekara ta 2003, Yang Liwei, dan sama-jannati na farko na kasar Sin ya yi zirga-zirgar sararin samaniya cikin nasara, a shekara ta 2005 kuma 'yan sama-jannti biyu na kasar Sin sun yi zirga-zirgar sararin samaniya har 'yan kwanaki da dama, haka kuma a shekarar da muke ciki, Zhai Zhigang dan kasar Sin na farko da ya yi tafiya a sararin sama. Zhou Jianping, babban mai tsara fasalin kumbo kirar "Shenzhou-7" ya bayyana cewa, aikin zirga-zirgar sararin samaniya tare da daukar mutane na kasar Sin ya shaidar da matsayin bunkasuwar kimiyya da fasaha ta kasar Sin. Kuma ya kara da cewa, "Harba kumbo kirar 'Shenzhou-7' cikin nasara ya sauke nauyi na mataki na biyu da aka dora wa aikin zirga-zirgar sararin samaniya tare da daukar mutane na kasar Sin. Daga baya kuma za mu harba kumbo domin kammala aikin haduwa da kumbuna biyu tare. Bayan da aka kammala wadannan ayyuka, to za mu samu kwarewar gudanar da tashar sararin samaniya da kuma dakunan gwaje-gwaje na sararin samaniya, ta haka za mu iya kafa dakin gwaje-gwaje na sararin samaniya ko kuma tashar sararin sama."
Amma dukkan abubuwan da suka faru yanzu wani buri ne da ke da wuyar samuwa ga Sinawa yau da shekaru 30 da suka gabata, sai dai bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar bude kofa ga kasashen waje da kuma yin kwaskwarima a gida a shekara ta 1978, an kauce hanyar da aka bi wajen raya kimiyya da fasaha ta kasar Sin sosai. Kuma daga wancan lokaci, kasar Sin ta tabbatar da hasashen cewa "kimiyya da fasaha karfin samarwa ne da ke gaban kome", da kaddamar da ayyukan samun kimiyya da fasaha ta zamani cikin himma da kwazo, da yin kokari wajen kafa tsarin taimaka wa bunkasuwar kimiyya da fasaha da kuma horar da kwararru, da kuma shigad da ingantuwar kwarewar kirkire-kirkire cikin gashin kai cikin manyan tsare-tsare na kasa.
Sabo da haka, a cikin 'yan shekaru da suka gabata, sha'anin kimiyya da fasaha na kasar Sin ya samu kyautatuwa kwarai da gaske, kuma karfin kimiyya da fasaha ya samu ingantuwa sosai. Ya zuwa yanzu, yawan kudaden da kasar Sin ta samar wa duk zaman al'umma wajen yin nazari da samun bunkasuwa a ko wace shekara ya riga ya zarce kudin Sin wato Yuan biliyan 300, wanda ya zo na biyar a duk duniya. Mei Yonghong, shugaban sashen kula da manufofi da ka'idoji da kuma yin kwaskwarima kan tsari na ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ya nuna cewa, "A 'yan shekaru nan da suka gabata, kasarmu ta riga ta samu bunkasuwa sosai a fannin kimiyya da fasaha. Muna da cikakken tsarin sassan ilmi da ba safai a kan iya samun irinsa da yawa a duniya ba. Ban da wannan kuma mun tattara dimbin kwararru a wannan fannin ciki har da manazarta, wadanda ke kan gaba a duniya."
A ran 28 ga watan jiya da maraice, kumbo kirar "Shenzhou-7" ya dawo wa doron kasa bisa lokacin da aka tsara, duk fadin kasar Sin cike yake da halin annashuwa. Zhou Jianping, babban mai zayyane-zayyane na kumbon ya bayyana cewa, za mu ci gaba da sa kaimi ga samun dauwamammiyar bunkasuwar zirga-zirgar sararin samaniya tare da daukar mutane domin dan Adam ya iya yin doguwar tafiya a sararin samaniya da kuma samun yawan sabbin abubuwa. (Kande Gao)
|