Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-23 17:19:04    
Somaliya a shekarar 2008

cri

A shekarar 2008, an yi ta samun tashe-tashen hankula a Somaliya, wadanda suka ta kawo illolinsu.

A fannin siyasa da tsaro, an mayar da hannun agogo baya a kasar har zuwa yau da shekaru biyu da suka gabata. Ba a rasa samun arangama a cikin gwamnatin wucin gadi na Somaliya. Shugaban Somaliya da firaministan kasar sun sha sabani sosai a kan batun dakarun da ba sa ga maciji da gwamnati, har ma a kwanan baya, shugaba Abdullahi Yussuf Ahmed ya sanar da soke mukamin firaminista Nur Hassan Hussein, wanda a cewarsa ya yi sakaci da aiki tare kuma da ci hanci da karbi rashawa. Amma duk da haka, majalisar wucin gadin kasar ta nuna goyon baya ga Nur Hassan Hussein da ministocinsa da su ci gaba da tafiyar da mukamansu, har ma a ran 17 ga wata, ta fara shirin tube shugaban kasar, wanda a cewarsu ya lalata yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar. Hakan ya tsumduma wannan gwamnati maras karfi cikin wani hali na kaka-nika-yi.

A waje daya, dakarun da ba sa ga maciji da gwamnati, musamman ma kungiyar matasan Islama, sai kara ingantuwa suke ta yi, har ma a halin yanzu, suka mallaki akasarin yankunan kudu masu tsakiyar kasar. Bugu da kari, bayan da Habasha ta dauki shekaru biyu tana yakin sari-ka-noke da dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin Somaliya, ta riga ta sanar da janye sojojinta daga Somaliya kafin karshen shekarar da muke ciki, don fid da kanta daga mawuyacin halin da ake ciki a Somaliya. Manazarta suna ganin cewa, idan aka janye sojojin Habasha daga Somaliya, to, da wuya ayarin sojojin kiyaye zaman lafiya na tarrayar Afirka wadanda yawansu ya kai kimanin 3,500 su dogara bisa karfin kansu, har ma ba yadda za su yi sai su ma su janye jikinsu daga kasar. Lalle, idan hakan ya faru, dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin Somaliya za su fi karfi a fannin soja kan gwamnatin wucin gadi.

Tashe-tashen hankula a Somaliya sun kuma kawo dimbin matsaloli ga kasashen da ke makwabtaka da ita. Kenya ta yi ta fama da laifuffuka masu yawa sakamakon kwararowar dimbin makamai zuwa kasar, balle ma a ambaci yawan sojoji da kayayyakin da Habasha ta zuba domin yakar dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin Somaliya. Ban da wannan, a shekarar da muke ciki, sau da dama ne dakarun Somaliya suka ketare kan iyakar da ke tsakanin Kenya da Somaliya, wadanda suka kai hare-hare ga ofishin 'yan sanda tare kuma da sace mutanen kasashen yammaci.

'Yan fashin ruwa na Somaliya sun jawo hankulan duniya sosai a shekarar da muke ciki. Bisa kididdigar da kungiyar samar da taimako ga ma'aikatan jiragen ruwa ta yi, an ce, a shekarar da muke ciki, gaba daya, yawan sacewa da jiragen ruwa da 'yan fashin teku suka yi a mashigin tekun Somaliya ya kai 123, ciki har da manyan jiragen ruwa masu jigilar mai fiye da 50, kuma har zuwa yanzu 15 daga cikinsu a hannun 'yan fashin suke, a yayin da yawan mutanen da 'yan fashin ke garkuwa da su ya kai sama da 300.

Mashigin teku na Aden wata muhimmiyar hanya ce da jiragen ruwa ke bi wajen shiga bahar Rum da tekun Atlantic daga tekun Indiya. Amma sabo da 'yan fashin tekun Somaliya, kudin inshora da jiragen ruwa ke biya wajen wucewa wurin ya karu kwarai da gaske, shi ya sa dimbin jiragen ruwan kasuwanci sun fara tunani kan canza hanyoyinsu zuwa Good Hope na Afirka ta kudu. Hakan zai kara yawan kudade da lokuta da ake bukata wajen sufuri, har ma zai kawo manyan illoli ga harkar sufurin jiragen ruwa na duniya.

A halin da Somaliya ke ciki yanzu, idan kasashen duniya ba su samar da taimako cikin lokaci ba, to, kasar za ta kara shiga rudani a nan gaba, wanda har ma zai shafi yankunan da ke makwabtaka da kasar da kuma tsaron duniya baki daya. Tun daga watan Yuni na bana, bisa shiga tsakani da MDD ta yi, gwamnatin wucin gadi ta Somaliya da masu sassaucin ra'ayi na dakarun da ba sa ga maciji da gwamnatin kasar sun gudanar da jerin shawarwari a kasar Djibouti, inda suka kusan cimma yarjejeniyar kafa gwamnatin gamin gambiza. Idan an iya aiwatar da yarjejeniyar, kuma yarjejeniyar ta kara jawo sauran bangarori a ciki, to, za a iya kyautata zaton shimfida zaman lafiya a Somaliya. (Lubabatu)