Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-22 19:54:19    
Mr. Guo Yun da aikinsa na kiyaye muhalli

cri

Ya shafe shekaru 15 yana yin kasuwanci, kuma ya sha wahalhalu da yawa ga yin sa, amma yanzu ya dukufa kan aikin kiyaye muhalli, shi kansa ya tattara kudin da yawansa ya kai kudin Sin Yuan dubunnan darurruwa domin kafa kungiyar kiyaye muhalli mai zaman kanta ta farko ta jihar Xinjiang ta kasar Sin wato "kungiyar mai da Hamada ta zama gonaki". Bisa matsayinsa na wani dan kasuwa, ya dukufa kan sha'anin kiyaye muhalli maras riba, amma bai yi nadama ba ko kadan, wannan bawan allah shi ne Guo Yun. Jama'a masu sauraro, cikin shirinmu na yau za mu kawo muku bayani dangane da Mr. Guo Yun da sha'anin kiyaye muhalli da yake tafiyarwa.

Mr. Guo Yun yana da shekaru 47 da haihuwa, ya taba yin kasuwanci a fannonin man fetur da kayan abinci da kanikanci. A watan Agusta na shekarar 2005, ya yada zango cikin wani gidan abokinsa lokacin da yake tafiyar da aikinsa zuwa sauran wuraren kasar, inda ya ga abokinsa ya yi tsimin ruwa sosai har ya tattara ruwan wanke hannu da na kayan lambu don sake yin amfani da shi, wannan ya burge shi kwarai. Bayan komawarsa gida, kuma cikin talabijin ne ya ga abubuwa masu bada misali da madam Yin Yuzhen ta yi wajen hana kwararowar hamada, ya ce, "Bayan da madam Yin Yuzhen ta yi aure zuwa gidan mijinta dake jihar Mongoliya ta gida lokacin da take da shekaru 19 da haihuwa, ta fara dasa itatuwa da ciyayi a nan kuma ta debo ruwa daga wuri mai nisan kilomita fiye da 10 don shayar da su, cikin shekaru 20 da suka wuce ta mai da hamada mai fadin kadada 4,000 ta zama gonaki. Bayan da na kalli wannan shirin talabijin na jiku sosai har hawaye ya zubo mini, a lokacin kuwa na kuduri niyya cewa ni ma zan yi kokarin daidaita matsalar kwararowar Hamada."

A farkon shekarar 2006, bayan da Mr. Guo Yun ya zo nan birnin Beijing don duba aiki kuma ya koma gida, ya yi saurin gabatar da rokon rajista domin kafa kungiyar kiyaye muhalli mai zaman kanta, a karshe kuwa aka kafa "kungiyar masu hidimar sa kai wacce ta mai da hamada ta zama gonaki ta jihar Xinjiang" a hukunce wato kungiyar kiyaye muhalli mai zaman kanta ta farko ta jihar wadda ta samu amincewa daga wajen hukumar gwamnatin kasar Sin.

Bayan kafuwar wannan kungiya, Mr. Guo Yun ya bar aikin kasuwanci kuma ya dukufa kan aikin kiyaye muhalli da zuciya daya. Matarsa Hu Chunhua ta ce, "A hakika da farko ba na son ya yi haka, amma daga baya ina jin cewa, wannan wani aiki ne mai kyau, babu dalilin da ba zan nuna masa goyon baya da taimako ba. Da farko shi kadai ne ya yi wannan aikin kiyaye muhalli, amma daga baya mutane da yawa da suka zo daga sassa daban-daban sun shiga wannan aiki, ni ma na yi haka, bayan da na shiga aikin, na gane cewa kowanenmu yana da hakkin yin sa."

Kowane aikin da ake yi domin kiyaye muhalli yana bukatar kudi, kamar kudin hayar filaye da motoci da cin abinci. Domin bai wa masu hidimar sa kai kwarin gwiwa, Mr. Guo Yun yakan ba wa kowanensu alawus na Yuan 10 sau daya, amma bisa ci gaban da aka samu wajen aikin, masu hidima na sa kai sai kara yawa suke sun ki karbar alawus daga wajen sa, sun zama masu aikin sa kai ba tare da karbar lada ba.

Da ma Mr. Guo Yun ya yi tsammani cewa, zai iya gudanar da aikin kiyaye muhalli cikin shekaru 2 zuwa 3 sabo da kudin Sin Yuan dubu 300 da ya samu ta hanyar sayar da dakinsa da motarsa, amma cikin tsawon lokacin da bai kai rabin shekara ba, sai ya kashe kudin fiye da Yuan dubu 100, ya bayyana cewa, muddin yana da kudi ko Fen daya ne ma zai yi kokarin ci gaba da sha'aninsa na kiyaye muhalli. Ya ce, "Da farkon lokacin kafuwar kungiyar, ina da kudin Sin kusan Yuan dubu 300, ina zato ba matsala ga aikin kiyaye muhalli cikin shekaru 2 ko 3 masu zuwa."

Ko da yake yanzu Mr. Guo Yun yana shan wahalhalu cikin zaman rayuwarsa, amma yana ganin cewa, yawan abubuwan da yake samu ya fi na batarwa. Ya ce yanzu ya samu girmamawa daga wajen jama'a, irin wannan girmamawa ba za a iya sayen ta da kudi ba. Aikin da yake yi yanzu aiki ne yake so, kuma aiki ne mai ma'ana, yana jin dadi sosai ga irin wannan halayen da yake ciki.