Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-22 16:12:27    
Iran ta sayi makamai masu linzami daga Rasha

cri

Wani jami'in kasar Iran a ran 21 ga watan Disamba, ya tabbatar da cewa, kasar Iran ta cimma yarjejeniya da kasar Rasha kan sayen wasu bomabomai masu linzami na S-300 daga hannun sojan Rasha don rigakafin hare-hare daga sama, kuma a halin yanzu kasar Rasha ta riga ta fara mika wa kasar Iran bomaboman. Manazarta na ganin cewa, sayen bomaboman zai kyautata tsarin tsaron kasar Iran, shi ya sa yana da muhimmanci sosai.

A ran 21 ga wata, Ismael Kowsari, mataimakin shugaban kwamiti mai kula da tsaron kasa da harkokin waje na majalisar kasar Iran, ya ce, za a girke wadannan makamai masu linzami a yankin iyakar kasar, ta yadda za a karfafa kwarewar sojojin kasar wajen tsaron sararin saman kasar. Amma, har zuwa yanzu, ba a samu tabbatarwa daga gwamnatin kasar Rasha ba, kan cewar za a sayar wa Iran da makamai masu linzami na S-300. Kamfanin dillancin labaru na kasar Rasha a kwanakin baya, ya ruwaito wata majiyar na fadin cewa, Rasha ta taba sayar wa Iran da makamai masu linzami na TOR-M1, kuma a halin yanzu ta fara sayar da makaman S-300 bisa yarjejeniyar da aka sa hannu a kai.

Dangane da batun, Andrei Nesterenko, kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Rasha, a watan Oktoba ya musunta labarin da aka bayar wai Rasha za ta ba Iran makamai masu linzami na S-300. Ya ce, kasar Rasha ba za ta samar da makaman zuwa ga kasashen da ke cikin shiyya maras kwanciyar hankali ba. Ya kuma jaddada cewa, shugabannin kasar Rasha za su yi la'akari da yadda za a kare daidaituwar karfin soja da kwanciyar hankali a wani wuri, kafin su yanke shawarar sayar da makamai zuwa wurin.

A halin yanzu, makaman da sojojin kasar Iran ke da su, su ne iri na TOR-M1 na kudin dalar Amurka miliyan 700, wadanda aka saye su daga hannun sojojin Rasha a shekarar 1 da ta wuce. Makami mai linzami na TOR-M1 a kan harbe shi don kai farmaki na gajeren zango, wanda tazararsa ke kasancewa a tsakanin mita 1000 zuwa 12000, kuma za a iya yin amfani da shi don kalubalantar takiti 2 cikin lokaci daya. A daura da haka kuma, makami mai linzami na S-300 daya ne daga cikin makaman sojojin Rasha da suka fi cigaba, wanda cigabansa yana kunnen doki da makaman Amurka na Patriot. Za a iya yin amfani da shi don harbi jirgin sama da makamai masu linzami, da kai farmaki ga takiti 100 cikin lokaci guda. Nisan farmakinsa ka iya kai kilomita 120.

Samun makaman S-300 zai sa kasar Iran ta iya kai farmaki ga takiti mai nisa da na sararin samaniya, ta yadda za a karya lagon hare-haren da kasar Isra'ila ka iya kai wa kasar Iran. A watan Yuni na shekarar bana, sojojin kasar Isra'ila sun yi gagarumin atasayen sojojin sama, inda aka yi amfani da jiragen yaki na F-15 da F-16 da yawansu ya kai fiye da 100, don gwajin farmaki mai nisa. A wajen atasayen da aka yi, jiragen yakin kasar Isra'ila sun yi tafiya sama da kilomita 1440, da nufin gwajin farmakin da ka iya kai wa tashar Natanz ta kasar Iran mai amfani da karfin nukiliya. Bisa halin da ake ciki ne, kasar Iran tana kokarin karfafa kayayyalin tsaro da ke kewayen tashar nukiliyarta.

Kasashen yamma da Amurka take shugabanta sun taba yunkurin hana wa kasar Rasha da ta sayar wa Iran da makamai masu cigaba. Kasar Isra'ila ita ma ta nuna rashin jin dadi kan batun, inda Amus Gilad, manzon musamman na kasar ya nuna wa gwamnatin kasar Rasha cewa, samar wa abokan gaban kasar Isra'ila da makamai masu cigaba ba zai taimaka kan aikin shimfida zaman lafiya a shiyyar ba.

Manazarta na ganin cewa, kasashen yamma na kokarin neman sa wa kasar Iran takunkumi, domin matsa wa kasar Iran lamba, ta yadda za ta daina aikin tacen sinadarin Uranium. Sayen makamai masu linzami na S-300 ka iya bayar wa kasar Iran damar samun nasara cikin muhawarar da za a yi.(Bello Wang)