Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-18 15:43:45    
Labarai na game da wani tsoho

cri
Sunan tsohon nan shi ne Wang Zhi,yana zama a cikin wani kauyen dake cikin dazuzzukan da ke cikin duwatsu na gundumar Jinxian ta lardin Anhui a yankin tsakiya na kasar Sin, ko da ya ke ya tsufa,amma ya nuna kauna da sa kulawa ga yara manyan gobe namu, har ma ya kafa wani gida mai kyau ga yaran da iyayensu suka tafi aiki waje da wuraren mahaifinsu.To sai ku ji labaran da aka kawo dangane da wannan tsoho. Shi ne Mr Wang Zhi wanda ya cika shekaru 75 da haihuwa a wannan shekarar da muke ciki.A shekara ta 1994 ne ya yi ritaya daga mukamin mataimakin shugaban dakin kula da al'adu na gundumar Jinxian ta lardin Anhui,daga baya ya koma kauyensa Gufeng na yankin Changqiao inda aka haife shi.wani caji-ofis ya gayyace shi aiki a matsayin mashawarcin harkokin shari'a saboda yana da ilimi mai zurfi wajen shari'a da ya ba da hannu wajen warware matsalolin laifuffukan da matasa suka aikata.A wannan lokaci Mr Wang Zhi ya gano cewa yaran da iyayensu ke ci rani sai kara yawa suke a kauyuka saboda iyayensu su ci rani su yi aiki a birane. Wadannan yara sun gaza samun ci gaban da ake zato wajen karatu. wasu ma sun lalata saboda iyayensu ba su gida,sun rasa kauna da kulawa.wasu ma sun aikata kanana laifuffuka.Mr Wang Zhi ya ce."kakanin yara mutane ne da suka fi tsufa,ba su da ilimi sosai,kuma ba su sa lura kan ci gaban zamani da al'umma,ba su da hanyoyin daidaici na yin hira da jikokinsu. Shi ya sa bayan makaranta,wadannan yara su kan yi abin yadda suka ga dama, cikin yawancin lokuta ba wanda ya kula da su."

Bayan da ya iske wannan al'amari,Mr Wang Zhi ya yi bakin ciki ya kuma nuna damuwarsa. Tarihin aikinsa a sahen tushe ya gaya masa cewa yara kamar bishiyoyi ne,sai a sa lura tun lokacin da suke kanana. Da ganin haka ya dauki nauyin kula da yara bisa wuyansa. Yana so ya kafa wani gidan renon yara musammman domin yaran da iyayensu suka ci rani suke aiki a birane,ya tattara yaran gu daya. Ya sa kulawa da ba da taimako ga yara wajen zama da karatu.Da ya samu wannan ra'ayi,sai a yanayin rani na shekara ta 1998 ya kinkintsa yara fiye da goma da su yi karatu tare da sauran ayyuka bayan makaranta,ya samu sakamako mai amfani. A shekara ta biyu Mr Wang Zhi ya fadada gidansa na yara,iyayen yaran da suka samu labarin gidan sun aika da yaransu zuwa gidan saboda gidan yaran ya yi suna a bangaren nan,daga baya gidan ya dauki yaran sama da dari.

Ci gaban da Mr Wang Zhi ya samu wajen shirya sansanin ci rani na yara a lokutan hutu na yanayin zafi ya karfafa masa kwarin gwiwa. Tare da taimakon gwamnatin wuri da na iyalinsa,Mr Wang Zhi ya zuba kudin Sin Renminbi dubu dari ya yi amfani da dakunan da wata masana'antar ta bari,ya kafa wata cibiyar ba da taimakon ilimi domin yaran da iyayensu suka ci rani suke aiki a wurare masu nesa da kauyukansu.

Cibiyar ba da taimakon ilimi ga yaran tana bin wata hanyar tafiyar da harkokinta a rufe.wato yaran dake cikin cibiyar su yi kome bisa wani tsarin da aka tsara dominsu,su yi karatu da wasa kuma hutu yadda tsarin ya tanada,idan wani daga cikin yana son ya fita sai ya yi rajista,haka kuma ga mai neman shiga. Da dare da akwai wadanda ke yin sintiri da kuma masu gadi.Ban da wannan kuma an gayyaci malaman koyarwa biyar wajen ba da darasi da ma'aikata guda hudu. Ya kuma kebe wani daki domin karanta mujaloli da jaridu,ya kuma saye injuna masu kwakwalwa da injin dabi da injin copy machine,da camera vidiyo,da kayan wasan dara da kwalayen wasa. Cibiyar ta shirya jarrabawa sau daya a wata. An kuma ba da kyauta ga wanda ya fi samun ci gaba wajen karatu. Ban da ilimin da ake bayarwa a cibiyar,ana kuma shirya wasanni iri iri domin yara ta haka kuwa za a karfafa ingancin yara daga dukkan fannoni.

Yarinya Liu Dan mai shekaru 16 da haihuwa tana zama a cibiyar ba da taimakon ilimi cikin dogon lokaci saboda iyayenta su kan ci rani suke aiki waje da kauyensu.Madam Bai Xiaohong,mamar Liu Dan ta gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa: "wani yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali ya game gidan yara,yaran suna girma cikin lami lafiya,ba na tsoron wata matsala ta same su. Domin malaman koyarwa da ma'aikatan sun kula da yaran yadda ya kamata daga dukkan fannoni. Yaran ba su iya fita waje yadda suka ga dama ba,sun mayar da hankalinsu kan karatu suna cikin zaman lafiya.idan suna cikin iyalansu,sai kowace rana su yi tafiyar kilomita biyar ko shida zuwa gidan,idan su yi tafiya da kekunan hawa,hankalinmu ba a kwance yake ba.Ga shi a yau kome na tafiya daidai suna cikin tsaro mai inganci."

Liu Dan ta kammala karatunta a karamar makarantar middle,ta fara karatunta a babbar makarantar middle a garin gunduma daga watan Stumba na bana.Da ta waiwayo tarihinta a gidan ba da taimakon ilimi,ta yi farin ciki da cewa:"A hakika mun yi zaman jin dadi a gidan,da akwai aminana da dama a gida,mun kula da juna muna taimakon juna,muna fahintar juna.Mu kan yi nazari tare yayin da muke karatu,haka kuma mu kan yi hira da bayyana abubuwan dake cikin zukatanmu,munajin dadin zama kamar iyali daya ne muke ciki."

Liu Dan ta gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa wani lokaci yaran da iyayensu suke cin rani suke aiki a wurare masu nesa su kan jin kadanci,suna so su yi hira tare.Ban da wannan kuma tsohon Mr Wang Zhi ya kan fadakar da yaran a tunani,ya kwantar da hankalinsu. A cibiyar ba da taimakon ilimi,malaman koyarwa su kan ba da ilimi a dare yayin da yaran ke karatu da kansu,su kan ba da amsa ga yaran da kara musu ilimi.Ana tafiyar da harkokin cibiyar ba da taimakon ilimi kamar yadda ake tafiyar da harkokin gidan renon yara.An kula da yaran cibiyar wajen abinci da dakin kwana da ba da ilimi da dai sauransu. Da rana yaran su tafi makarantu su yi karatu,da tsakar rana da dare su koma cibiyar ba da taimakon ilimi su sami kulawa da Mr Wang Zhi ya nuna musu kamar kakaninsu.

Yar cibiyar Zhu Eenzhi tana karatu a jami'a a halin yanzu, amma a da koma baya take wajen karatu. Bayan da aka shiga da ita a cibiyar, ta yi kome yadda ya kamata wajen karatu da zama,ta sami kyakkyawr al'ada,ta samu ci gaba sosaia wajen karatu,daga bisani ta cimma burinta na shiga jami'a ta hanyar jarrabawa. Mr Wang Zhi ya bayyana cewa : " A ganina abun mafi muhimmanci shi ne mu fadakar da yara da su zama masu nagarta,sa'nnan su samu ilimi mai amfani. Wadannan abubuwa biyu suna da muhimmancin kwarai da gaske.kullum muna bin wannan ka'ida.mun dora muhimmanci kan mayar da su zama nagartattu, a sa'I daya kuma ba mu yi sassauci wajen ba su ilimi ba.Idan wani ya yi kuskure,mu yi masa suka yadda ya kamata kuma cikin lokaci.idan wani ya aikata wani abin kirki,mu kan yi masa yabo,mu karfafa kwarin gwiwarsa da ya ci gaba da kokarinsa. Yaran da ke cikin cibiyar suna zaman sakin jiki da kwanciyar hankali."

Cibiyar ba da taimakon ilimi ga yara ta shafe shekaru bakwai ke nan yau bayan da aka kafa ta a shekara ta 2001,yaran sama da dari bakwai suka yi zama a ciki,yanzu sun fita daga wannan cibiya zuwa wuraren waje da duwatsu sun shiga sana'o'I daban daban.Da ganin wannan sakamako,tsohon Mr Wang Zhi mai farin gashi wanda ke aiki tukuru rana da dare,ya yi farin ciki sosai. Ya waiwayi tarihin cibiyar na tsawn shekaru bakwai ya bayyana cewa:

"Ina son in yi wani abu domin amfanin zamantakewa da jama'a.Idan na ba da tallafi ga wani yaro,yaron ya samu 'yanci.Idan na ceci wani yaro,ya yi daidai na ceci wani iyali.Idan na ba da tallafi ga wani yaro a muhimmin mataki,wannan yana nufin cewa na ba shi taimako a duk rayuwarsa." Jama'a masu sauraro,wannan ya kawo karshen shirinmu na yau na zaman rayuwar Sinawa.Mun gode muku saboda kun saurarenmu.sai mako mai zuwa za mu sake saduwa.(Ali)