A kauyen Tuohula na garin Buzhak da ke da nisan kilomita 17 da birnin Hetian na jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur, an kafa wani dutsen tunawa mai siffar rubutun "Ruwa" cikin Sinnanci. Manoma da masu kiwon dabbobi na wurin, wadanda suka riga suka sha ruwa mai tsabta, su ne suka kafa wannan dutsen tunawa, domin tunawa da aikin kyautata ingancin ruwa don magance cututtuka.
Tun daga shekaru 80 na karnin da ya wuce, gwamnatin kasar Sin ta soma aiwatar da aikin "kyautata ingancin ruwa don magance cututtuka" a jihar Xinjiang, ya zuwa watan Satumba na shekarar 2007, wato shekarar da muke ciki, gwamnatin kasar ta bayar da kudin Sin RMB biliyan 2.6 da wani abu kan gine-ginen samar da ruwan sha na iri daban daban, ta kafa kamfannonin samar da ruwan sha 3151, tsawon batutun samar da ruwa da aka gina ya wuce kilomita dubu 71, haka kuma an warware matsalar shan ruwa da ake fuskantar a shiyyar.
Yanzu yawancin manoma da masu kiwon dabbobi da ke kudancin dutsen Tian Shan na jihar Xinjiang da kuma arewacin dutsen sun yi ban kwana da halin rashin samun ruwan sha mai tsabta, a hakika dai sun kawo karshen tarihi na shan ruwan madatsar ruwa, yanzu ruwan pampo mai tsabta na gudu shiga gidajensu.
"Na yi godiya sosai ga gwamnatinmu, sabo da ta gabatar mana ruwan sha mai tsabta". Wannan magana ta fito ne daga Maimaiti Yashengjiang, wato wani manomi 'dan kabilar Uygur da ke zama a wani karamin kauye na gundumar Wushi da ke arewa maso yammacin kwarin Tarim. A da, a ko wace rana ya je wurin da ke da nisan kilomita 3 da gidansa, don dawo ruwan sha.
A jihar Xinjiang, manoma da masu kiwon dabbobi, wadanda ke zama cikin hali kamar irin na Maimaiti Yashengjiang suna da yawa. Jihar Xinjiang tana bakin iyakar arewa maso yammacin kasar Sin, sabo da haka tana da halin kasa na musamman, a sakamakon haka kuma ana yin fari da rashin ruwa a shiyyar, rashin ruwan sha mai tsabta a kauyyuka ya zama muhimmiyar matsalar da shiyyar ke fuskanta.
Ba kawai mazauna wurin na kabilu daban daban su kan samu cututtuka sabo da sun sha ruwa maras inganci ba, har ma wasu daga cikinsu ba su iya kawar da talauci a cikin dogon lokaci sabo da matsalar.
Shugaban hukumar aikin tsare ruwa ta jihar Xinjiang Wang Shijiang ya bayyana cewa, dalilin da ya sa aka aiwatar da ayyukan samar da ruwan sha shi ne, domin sanya manoma da masu kiwon dabbobi na kabilu daban daban su sha ruwan da ke bisa ma'aunin ruwan sha na kasarmu.
Yanzu, mutanen da ke iya shan ruwa mai inganci sun fara mai da hankulansu kan aikin kawo albarka, daga aikin daukar ruwa a da.
Ufli Yousufu, wani manomi na garin Yudai na jihar Xinjiang ya ce, a da bayan da na gama aiki a gonaki har dukkan rana, tilas ne in je madatsa don daukar ruwa, amma yanzu muna da ruwan pampo mai inganci a gidajenmu, mun samu sauki sosai, kuma ba za mu kashe kudi da yawa kan wannan ba, lallai muna ta kara jin dadin zama a kwana a tsahi.
|