Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-17 17:05:12    
Madam Yang wadda ta gina wata babbar hasumiya mai samar da ruwa a Hamadar Sahara

cri
Shekarar nan shekara ce ta 30 da aka gudanar da manufar gyare-gyare da bude kofa a kasar Sin. A cikin wadannan shekaru 30, an samu babbar bunkasuwa a dukkan fannoni, ba ma kawai sakamakon da aka samu wajen aiwatar da manufar gyare-gyare da bude kofa ya kawo moriya ga jama'ar kasar Sin ba, hatta ma, ya ingiza bunkasuwar dangantakar abokantaka dake kasancewa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika.

A cikin wadannan shekaru 30, kasar Sin tana yin iyakacin kokari wajen ba da tallafi ga kasashen Afrika, ya zuwa karshen shekara ta 2007, ta yi wa kasashen Afrika ayyuka fiye da 800, wadanda suka shafi masana'antu da aikin noma da zirga-zirga da tarbiyya da kiwon lafiya da kuma manyan ayyukan yau da kullum da dai sauransu. Suna takawa muhimmiyar rawa a wadannan kasashe. Masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wani bayani game da aikin samar da ruwa da kasar Sin ta gina a Jamhuriyar Nijer.

An ce, ruwa mahaifiyar rayuka ce. Shi ya sa, darajar ruwa dake a yanki dake fama da karancin ruwa kan daga.

Ranar 24 ga watan Yuni na shekarar 2005 wata rana ce ta farin ciki ga mutanen birnin Zinder. A wannan rana, mutanen birnin suna cike da jikuwa, sun fito daga gidaje don yin murnar gama aikin gina hasumiyar samar da ruwa a wannan wurin dake kudancin hamadar Sahara, wadda za ta kawo karshen matsalar rashin ruwan sha a nan.

Don haka, mutanen birnin ba za su manta da wadda ta tsara fasalin wannan hasumiya wato Madam Yang Fenglan ba. Madam Yang dake aiki a kwalejin bincike da tsara fasali kan ayyukan ruwa na birnin Beijing ta taba zuwa kasar Nijer har sau 4, mutanen kasar Nijer suna kiranta Madam Yang.

Mun yi sa'a, a kwanakin baya, mun samu damar neman labari daga wajenta, inda ta gaya mana halin kasancewarta na watanni 21 da take aiki a birnin Zinder na kasar Nijer.

Birnin Zinder shi ne babban birnin Jamhuriyar Nijer a cikin tarihi, amma sabo da karancin ruwa a kowace shekara, gwamnatin Nijer ta zabi birnin Niamey ya zama hedkwatar kasar don maye gurbin birnin Zinder. Daga bisani, birnin Zinder yana fama da rashin ruwa, mutane fiye da dubu dari ba su samun issashen ruwan sha.

Ya zuwa watan Satumba na shekarar 2002, injiniyoyin ruwa na kasar Sin sun isa Jamhuriyar Nijer a karo na farko don fara gina ayyukan samar da ruwa a birnin Zinder. Madam Yang Fenglan ta yi waiwaye adon tafiya ta ce,

"Daga watan Satumba zuwa watan Oktoba na shekarar 2002, mun yi bincike a wurin, daga bisani, mun dawo gida mun tsara fasali na matakin farko. Sa'anan, a watan Afril zuwa watan Mayu na shekarar 2004, mun yi bincike da nazari a karo na 2 a wurin. A karshe dai, a watan Oktoba na shekarar 2003, mun fara ayyukanmu."

Kyakkyawan mafari wani kashi ne mafi muhimmanci na wani aiki. Yin bincike a matakin farko na aikinmu, shi ma wani muhimmin mataki ne. Amma, injiniyoyin kasar Sin sun gamu da wahalhalu da yawa a wannan mataki. Madam Yang ta ce,

"A wancan lokaci, lalle mun gamu da wahalhalu da yawa, ko da yake mun yi aikin share fage sosai. Ambaliyar ruwa ta datse hanyarmu, mun yi sa'o'I 27 muna jiran taimako."

Ban da wannan kuma, sabo da rashin takamaiman rahoto kan yanayi da koguna dake wurin, injiniyoyin kasar Sin sun yi bincike su da kansu. Ko da yake, sun gamu da wahalhalu da yawa, amma a karshe dai, sun gama aikin bincike da kyau, Madam Yang ta ce,

"Tsawon manyan bututun samar da ruwa ya kai kilomita 25, kuma tsawon sauran bututu ya kai kilomita 12, muna bukatar yin bincike kan dukkan wadannan bututu. A karo na farko da muka je birnin, muhimmin aikinmu shi ne tabbatar da wuraren da wadannan bututun za su wuce, shi ya sa, mu kan yi kai da kawowa a kan wannan hanyar wadda tsawonta ya kai kilomita 30."

Kasar Sin ta dauki nauyin tsara fasali da yin wannan aikin samar da ruwa, kuma kasar Sin ta ware kudaden don gina shi. A yayin da take magana kan dalilin da ya sa gwamnatin kasar Sin ta yi wannan aiki, Madam Yang ta ce,

"An mai da wannan aiki a matsayin aikin gaggawa a Jamhuriyar Nijer. Mazaunan birnin ba su iya samun ruwa ko kadan ba a yanayin rani. Na ga farar hula da yawa dake neman ruwa a ko ina. A yanayin damina, akwai ruwa a tabki, amma a yanayin rani, ruwa yana kasancewa tare da rairayi, sabo da haka, ana kasa yin amfani da wannan ruwa. Kasar Sin ta yi wannan aiki ne don daidaita matsalar da farar hula suke fuskanta."

Duk wanda ya taba zuwa birnin Zinder yana iya ganin wani shahararren gini, wato babbar hasumiya mai samar da ruwa. A ran 24 ga watan Yuni na shekarar 2005, bayan watanni 21 da aka yi kokarin aikin bincike da tsara fasali da kuma ginawa, kasar Sin ta cimma nasarar gama aikin gina babbar hasumiya mai samar da ruwa a birnin Zinder. A wannan rana, dukkan mutanen birnin Zinder sun yi farin ciki matuka, dubban mutane sun taru a gindin hasumiyar. Shugaban kasar Nijer Mamadou Tandja, shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Mamman Usman da kuma sauran ministocin kasar da 'yan majalisa da yawa su ma sun halarci bikin yanke kyalle ga babbar hasumiya a birnin Zinder dake da nisan kilomita fiye da 900 daga birnin Niamey, babban birnin kasar Nijer. Madam Yang ta waiwaya da cewa,

"A lokacin da muke gina hasumiyar, mazaunan birnin suna ta dora muhimmanci sosai kan aikinmu, kuma suna yin bege ga wannan hasumiyar samar da ruwa. Sabo da haka, a yayin da muka gama aikin, kusan daukacin mutanen birnin sun tsaya a kan titi don yin murna. Wannan hasumiyar da muka gina yana kan wani tsauni, amma mun kasa ganin wannan tsauni, sabo da yawan mutanen dake wajen, shugaban kasar Nijer da shugabanni da 'yan majalisa na kasar da kuma ma'aikatan ofishohin jakadancin kasashen waje su ma sun halarci bikin yanke kyalle."

Madam Yang ta gaya mana cewa, birnin Zinder garin shugaba Tandja ne. A gun bikin, malam Tandja ya yi bayani kan tarihin neman ruwa a wannan birni. Ya ce, an yi shekaru da yawa ana tattaunawa kan wannan aikin samar da ruwa, bangaren Nijer ya nemi tallafi daga kasashe daban daban. Bayan kasar Nijer ta nemi taimako wajen kasar Sin, Sin ta amsa gayyatar kasar Nijer nan da nan. Ya furta cewa, kasar Sin kawar ainihi ce ta Jamhuriyar Nijer, ya nuna godiya ga tallafin da gwamnatin kasar Sin ta bayar.

Aikin samar da ruwa ya ceci birnin Zinder dake karancin ruwa a tsawon tarihi. Muna iya cewa, ya samu yabawa sosai daga mutanen birnin. Bayan da aka cimma nasarar gama aikin gina hasumiyar samar da ruwa, farashin ruwa ya sauka, zaman rayuwar jama'a ya samu kyautattuwa sosai. A sa'i daya kuma, wannan aiki ya sada sassan birnin da ruwa, fiye da da, mutanen dake cibiyar birnin suna iya samun ruwa kai tsaye, yanzu, galibi dai, aikin ya daidaita matsalar karancin ruwan sha a birnin. An labarta cewa, za a cigaba da gina wannan aikin samar da ruwa, za a hada sabon bututu da wadanda Madam Yang ta gina, za a iya cimma burin samar da ruwa zuwa wajen birnin Zinder.

Injiniyoyin kasar Sin sun samu girmamawa daga gwamnati da jama'ar kasar Nijer, haka kuma, shugaban kasar Nijer ya gana da Madam Yang da sauran injiniyoyin kasar Sin har sau 4, Madam Yang ta samu lambar yabo da shugaban Nijer ya bayar a watan Agusta na shekarar 2006.

Aikin samar da ruwa da kasar Sin ta yi ya kyautata zaman rayuwar mutanen birnin Zinder, kuma ya sada dankon zumunci tsakanin kasashen biyu. A lokacin da take aiki a birnin Zinder, Madam Yang ba ta saba da yanayin wurin ba, ta kamu da zazzabin cizon sauro har sau 2. Amma, ta ci gaba da aiki a can.

Madam Yang Fenglan ta ce, abin da ya ba ta kwarin gwiwar cigaba da gudanar da aiki shi ne zumuncin dake tsakaninta da mazaunan birnin. Ta ce,

"Na yi iyakacin kokari a kan wannan aiki, a sa'I daya kuma, na fahimci mutanen Afrika ta wannan aiki. A wadannan shekaru biyu, na gamu da wahalhalu da yawa, alal misali, zazzabin cizon sauro. A lokacin da nake fama da zazzabin cizon sauro, ina kwana a kan gado, kawayena na Afrika suna zuwa wurina don gaishe ni tare da ba ni kyauta. Amma a hakika dai, suna fama da talauci sosai. Ta haka, sun burge ni kwarai da gaske. A wadannan watanni 21, ko da yake, na yi fama da wahalhalu da yawa, amma na yi farin ciki, kuma ina son Afrika matuka."

A shekarar 2006, Madam Yang Fenglan ta je birnin Zinder a karo na 4. A lokacin da ta isa birnin, dahun dare ya yi, amma ba ta yi tsammani ba, mazaunan birnin da yawa sun riga suna jiranta a can. Madam Yang ta ce,

"Mazaunan birnin da yawa sun tsabtace wurin da na taba zama a da, suna fatan zan cigaba da zama a can. Sun yi tadi da ni kan aikin samar da ruwa. Sun burge ni sosai?."

Madam Yang ta tuna da mazaunan birnin sosai. Tana fatan za ta gaishe da kawayenta dake kasar Nijer daga nan gidan rediyon kasar Sin.

"Sannunku, mutanen birnin Zinder, na gode muku sabo da taimakon da kuka ba ni. Kuma ina tunawa da ku sosai da sosai. Ina fatan za ku ji dadin zamanku, ku zama lafiya!"(Lami)