Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-17 16:03:20    
Ana sake maido da al'adun titin Qianmen na tsohon birnin Beijing a yankin Qianmen na Beijing

cri
Lokacin da muka gabatar da al'adun tsohuwar hedkwatar kasar Sin da ke birnin Beijing, da farko ne mutane suka iya tunawa da tsohuwar fadar sarakuna ta zamani aru aru da ke da tarihin da yawan shekarunsa ya kai 600. Amma a hakika dai ne, a wurin da ke kudancin tsohuwar fadar sarakuna ta Zijin, da akwai wani babban titi mai suna Qianmen a birnin Beijing, shi ne yana daya daga wuraren da aka kiyaye al'adun tsohon birnin Beijing da kyau. A kwanan baya, an yi kwaskwarima sosai kan yankin titin Qianmen, shi ya sa ana sake maido da tsohon halin tarihi da ake ciki a titin kasuwanci na Qianmen, wannan ya jawo hankulan mutanen birnin Beijing wajen tunawa da abubuwan da suka faru a da.

Da farko za mu bayyana masu sauraronmu tarihin kafa birnin Beijing. A farkon karni na 15, daular Ming ta kasar Sin ta kafa hedkwatarta a birnin Beijing, ta kuma mayar da fadar sarakuna bisa matsayin cibiyar birnin, sa'anan kuma an gina sauran gine-gine na birnin Beijing a gefunan biyu na muhimmiyar hanyar da ke hada da kudu da arewa , a cikin birnin, an gina kofofi guda tara, a kan babbar hanyar da ke fuskantar kudu, an gina kofar da ake kira "Zhengyang", jama'ar farar hula suna kan kiran kofar da cewar "Qianmen", a cikin darurukan shekaru na daular Ming da daular Qing, yankin Qianmen shi ne yanki mai wadata kuma mai cin kasuwanci sosai. Ina dalilin day a sa hakan ya samu? Duk saboda manyan hukumomin gwamnatoci na daular Ming da daular Qing an kafa su ne a gefunan biyu na babban titin Qianmen. Mutanen da ke zama a sauran wuraren kasar Sin sun kan tafi Qianmen don yin harkokinsu, saboda haka, an kafa shaguna da kantuna da dakunan cin abinci da wuraren jin nishadi da hotel hotel da yawa a titin nan na kasuwanci. Bisa abubuwan da aka rubuta, an bayyana cewa, a wancan lokaci, a yankin Qianmen da yawan fadinsa ya kai murraba'in wasu kilomita kawai, yawan dakunan da aka nuna wasanni kuma mutanen suka ji nishadi a nan ya kai 140 ko fiye, kai, an ci kasuwanci sosai da sosai.

Wani mai yin nazari na hukumar kula da kayayyakin tarihi ta birnin Beijing ya bayyana cewa, bayan kafa babban titin Qianmen a karni na 15, an yi masa kwaskwarima har sau biyar, saboda haka ya sami sauyawa sosai a kowane karon da aka yi masa kwaskwarima, musamman ma a karo na biyu, ya sami babbar sauyawa sosai, a wancan lokaci, a cikin tunanin mutanen birnin Beijing, musamman ma a cikin tunanin mutanen da shekarun haihuwarsu ya kai 70 ko 80, babban tiitin Qianmen ya sami babban sauyi fiye da kima.

Wani dan wasa mai suna Liang Houmin da ke da shekaru 68 da haihuwa, yana kaunar babban titin Qianmen sosai. Ya bayyana cewa:

Wadanda suke yin zaman rayuwa a wannan titi suna da zurfaffen tunani a kan titin. A tsohon birnin Beijing, jama'ar farar hula sun kan tafi babban titin don sayen abubuwan da suke bukata a yau da kullum, tsoffin shaguna da kantuna da yawa su ne sun yi suna sosai, wato shagunan Ruifuxiang da Neiliansheng da Majuyuan, tsoffin allunan nuna alamominsu ko sunayensu har wa yau dai suna nan suna kasancewa. A wancan lokaci, in mutanen iyalinmu sun ce za su sayi wani abu, sai sun tafi babban titin Qianmen don sayen abubuwan da suke bukata. Yanzu, wuraren sayar da abubuwa suna kara karuwa a birnin Beijing, shi ya sa a kai a kai ne ake rage karon zuwan titin.

Game da wasu shahararrun shaguna da kantuna da suka yi suna sosai, wato shagunan Ruifuxiang da ke sayar da siliki da Neiliansheng da ke sayar da takalmi da Majuyuan da ke sayar da huluna da sauransu, su ne suka yi suna sosai, akwai wata Magana da aka yi da cewa, sanya hular Majuyuan a kai, kuma sanya tufaffin Ruifuxiang a jiki, sa'anan kuma a sanya takalmin Neiliansheng a kafa. Wannan ya bayyana halin da ake ciki a wancan lokaci sosai dangane da babban titin, tamkar yadda ake kai da kawowa a manyan kantunan duniya don sayen kayayyakin da suke da suna sosai a duniya yanzu.

Amma, bisa albarkacin bunkasuwar zamantakewar al'umma, birnin Beijing ya zama babban birnin zamani da ke hedkwatar kasar Sin. A cikin birnin, a ko'ina ana iya samun sabbin shaguna da sabbin kantuna na yin ciniki da kasuwanci, saboda haka yankin babban titin Qanmen ya soma dagulewa a kowace rana, kuma gine-ginen da ke wurin suna lalacewa, don kiyaye tsohon halin da ake ciki na shahararren babban titin , sai daga shekarar bara, an soma yi wa yankin babban titin Qianmen kwaskwarima bisa babban mataki. Kafin yin kwaskwarimar, an yi bincike da tsara fasali sosai da sosai. Wanda ke shiga aikin binciken mai suna Wang Shiren ya bayyana cewe, an yi kwaskwarima a wannan karo ne bisa ka'idoji biyu, na farko, za a biya bukatun da ake yi wajen harkokin kasuwanci da maido da tsohon halin musamman na gargajiya, duk domin wurin nan wuri ne da ake yin harkokin kasuwanci, ya kamata a samar da hidimar zamani ga harkokin kasuwanci. Wurin nan babban titi ne na nuna halayen musamman na tsaohon birnin Beijing, dalilin da ya sa wasu suka je titin yawo shi ne don more halayen musamman nasa. Saboda haka a hada wadanda za a yi amfani da su da wadanda za a more su . Na biyu, ya kamata a kare kayayyakin tarihi, wasu an maido das u, wasu kuma an kare su sosai.

Bisa bayanin da Mr Wang shiren ya yi, an bayyana cewa, a gun kwaskwarimar da ake yi a wannan karo, a cikin hanyar titin da ked a tsawon mita 840, an kare gine-ginen tarihi 9 da aka gina a farkon karnin da ya wuce, an maido da tsoffin shaguna da kantuna 41 tare da manyan allunan gine-ginen gargajiya na kasar Sin guda uku, sa'anan kuma an tanada kuma an yi kwaskwarima da kara daga ingancin gine-gine guda 5, har ma an yi kwaikwayon gina gine-ginen tarihi d yawansu ya kai 52.

An bayyana cewa, tun daga ranar kafa hedkwatar daular Ming a birnin Beijing, sai babban titin Qianmen ya zama hanyar da dole ne sarakuna suka bi zuwa Tiantan don shiga bukukuwan nuna girmama wa sararin samaniya. Ta karon nan na yin kwaskwarima ne, an maido da tsohon halin titin da ake ciki a zamanin da , a tsakiyar titin da ke da fadin mita 21, an ske maido da hanya mai launin fari kuma mai fadin mita uku da sarakuna suka bi a da, a gefuna biyu na titin, sa akwai shagunan da suka hada da dakin cin gasassun agwagi na Quanjude da tsohon dakin sayar da littatafai da dakin daukar hotuna da ke da shekaru fiye da 80 da gidan nuna wasannin kwaikwayo, sa'anan kuma wani jirgin da ke da waguna daya yana zirga-zirga a kan kwangiri tare da buga kararawar ding-dang-ding-dang, wannan ya jawo tunanin da mutane suka yi a kan abubuwan da. (Halima)