A makonni bi da suka wuce, mun yi muku karin bayani kan ni'imtattun wurare da ke da halin musamman na lardin Sichuan, mun yi imani cewa, kun kara saninku kan irin kyan ganin Sichuan kadan. Yau ma za mu tabo magana dangane da wata alamar lardin Sichuan, wato dabbar Panda. Za mu kai ziyara ga shiyyar kiyaye halitta ta Wolong, wato gidan dabbar Panda, da ke da nisan kilomita dari 1 ko fiye a tsakaninta da birnin Chengdu, babban birnin lardin Sichuan.
Kamar yadda mu kan yi a da, kafin mu soma shirinmu na yau, ga wasu tambayoyi 2 da za mu yi muku, da farko shi ne, ko lardin Sichuan gari ne ga dabbobin Panda? Ta biyu kuma, Panda nawa ne suke zaune a cikin kungurmin daji da ke shiyyar kiyaye halitta ta Wolong? To, bari mu fara ziyararmu a yau.
Yau da shekaru 20 ko fiye da suka wuce, dimbin gororin da dabbobin Panda suke ciyar da kansu da shi sun mutu. A wancan lokaci, makadan kasar Sin sun tsara wakar da kuke saurara a yanzu domin tattara kudaden taimako ga dabbobin Panda. Yanzu a shiyyar kiyaye halitta ta Wolong, gorori na kara yalwa sosai. Panda kuwa, wadda wata irin dabba ce mai daraja kuma mafi dogon tarihi a duniya suna zaune lami lafiya cikin farin ciki a nan.
Shiyyar kiyaye halitta ta Wolong da ke arewa maso yammacin lardin Sichuan na kasar Sin na daya daga cikin manyan wuraren da aka fi samun dabbobin Panda. Shi ya sa aka mayar da lardin Sichuan tamkar garin Panda. Saboda a kungurmin daji a lardunan Sichuan da Shaanxi da kuma Gansu kawai, aka gano dabbobin Panda. Shi ya sa masu yawon shakatawa wadanda suke son ganin Panda su kan zabi cibiyar kula da Panda ta kasar Sin da ke cikin wannan shiyyar kiyaye halitta. Zhang Liming, jami'in shiyyar ya yi karin haske cewa,
"Manufar da shiyyarmu ke bi ita ce tabbatar da ganin Panda da ke ci gaba da kasancewa lami lafiya, da kuma bai wa masu sha'awar Panda na duk duniya wata damar taba Panda kai tsaye. Ban da wannan kuma, muna gaya wa matafiya dalilin da ya sa ake kiyaye muhalli da tarihin Panda, muna fatan za su fahimci muhimmancin Panda a matsayin wata irin dabba mai dogon tarihi a lokacin da suke kallonsu."
Tun da can, mutane suna nuna sha'awa sosai kan Panda saboda jikinta ya yi kama da wata kwallo, ta kan nuna alamu masu kyau, kuma tana da gashi baki da fari. Yanzu ana kiwon Panda fiye da 100 a cikin cibiyar kula da Panda ta kasar Sin. Suna jin dadin zaman rayuwarsu sosai a nan.
Abin da ya fi damun mutane shi ne abincin da ake bai wa Panda. Masu kiwon Panda sun yi bayanin cewa, da can Panda na cin nama, amma sun mayar da gorori a matsayin muhimmin abincinsu a maimakon nama sannu a hankali. Shiyyar Wolong ta cancanci samun gorori masu yalwa sosai, shi ya sa Panda suke zaune yadda ya kamata, kana kuma suke yin hayayyafa a nan. Ko da yake ba su ci gaba da cin nama ba, amma Panda ba su kyautata kwarewarsu ta narke abinci ba. Shi ya sa domin kiyaye karfinsu, Panda ba su motsa jiki sosai ba, kuma su kan yi abubuwa sannu-sannu.
Madam Rebecca Haase ta kasar Amurka ta dauki hotuna masu yawa kan Panda, ta yi zumudi sosai saboda ganin Panda a kusa da su a karo na farko. Ta ce,
"Na ji farin ciki sosai saboda ganin Panda a kusa da su, suna da kyan gani, kuma suna da koshin lafiya. Ina fatan za a kara samun Panda a shiyyar Wolong."
An gina wani dakin zamani don kiwon kananan dabbobin Panda a wannan cibiyar kula da Panda, inda mutane su kan ciyar da Panda jarirai don rage yawan mutuwar Panda jarirai. Matafiya suna iya kallon wadannan Panda jarirai da aka haife su ba da dadewa ba ta gilas. Girman wadannan Panda jarirai ya yi daidai da tafin hannun mutum, sun rufe idanunsu, ba su da gashi da yawa. Da wuya a yi zaton cewa, za su yi girma, za su sami gashi da yawa a jikunansu, za su yi tafiya sannu a hankali.
Mr. Zhang Shicang da ya zo daga yankin Taiwan na kasar Sin ya dade yana tsaye a wajen da dakin kiwon kananan Panda yake, a tsanake ya kalli yadda ake shayar da Panda jarirai madara. Ya ce,
"Na san fannonin ilmi da yawa kan wannan dukiyar ta kasarmu wato Panda a wannan gami. Mai jagorar matafiya ya gaya mana labari da tarihin Panda da muhallin da suke zaune. Yanzu na san cewa, da wuya su hayayyafa, iyayen Panda mata ba su iya shayar da yaransu yadda ya kamata."
Saboda karin masu yawon shakatawa da yawa sun nuna sha'awa kan Panda, shi ya sa da yawa daga cikinsu suka fi son yin aikin sa kai a shiyyar Wolong. Madam Kodama Midori, wadda ta zo daga kasar Japan na daya daga cikin irin wadannan masu aikin sa kai. Tare da sanya tufafin masu aikin sa kai. Ta gaya mana cewa, abokanta 3 da ita sun zo shiyyar Wolong, za su yi mako guda suna zaune tare da Panda cikin farin ciki. Ta ce,
"A ko wace rana da safe, na kan bai wa Panda abinci, na kan share dakunansu da kuma kawar da kashinsu da rana haka kuma da yamma. Ba zai yiwu ba in zama tare da Panda a kusa da su haka a zaman yau da kullun, shi ya sa na ji zumudi kwarai da gaske a wannan karo."
A hakika kuma, matafiya suna iya ganin yadda Panda suke yin girma a lokuta daban daban na ko wace shekara. Mr. Li Desheng, wani kwararre mai ilmin dabbar Panda ya gaya mana cewa, a lokacin zafi, Panda cike suke da karfi sosai saboda babu zafi a Wolong. A lokacin kaka, matafiya sun sami damar ganin yadda Panda mata suke haifar 'ya'yansu, a lokacin bazara kuwa, balagaggun Panda su kan yi barbara a ko ina, akwai labaru masu ban sha'awa da yawa a wannan fanni. Mr. Li ya ce,
"Panda na daji su kan sami damar daukar jagoranci wajen yin barbara bayan da suka ci nasara a cikin fadan da Panda maza suka yi. Amma an hana irin wannan fada mai zafi a tsakanin Panda da mutane suke kiwo. A lokacin bazara, muna sanya Panda maza suna makwabtaka da Panda mata, suna iya ganin juna. A zaman yau da kullum, Panda ba sa yin ihu, amma a lokacin barbara, su kan ihu. A mataki na farko, ihunsu ya yi kama da kukan tsuntsaye, a mataki na karshe, ihunsu ya yi kama da kukan kare. A lokacin da suke kasancewa a halin barbara, suna yin ihu kamar tunkiya. "
Ban da Panda da mutane suke kiwo, yanzu Panda fiye da 100 suna zaune a cikin kungurmin daji a shiyyar kiyaye halitta ta Wolong, wadanda yawansu ya kai misalin kashi 10 cikin dari da na dukkan wadanda ke zaune a cikin kungurmin daji na duniya. A can da an haramta wa masu yawon shakatawa shiga cikin wuraren da wadannan Panda na daji ke zaune, amma a kwanan baya, shiyyar kiyaye halitta ta Wolong ta gabatar da shiri na farko na kallon Panda na daji a kungurmin daji domin manyan baki da suka kawo wa shiyyar Wolong ziyara, ta haka suna iya kallon Panda wadanda ke zaune a kungurmin daji ta hanyar tsarin sa ido ta zamani.
Jama'a masu sauraro, muna muku maraba da ku bakunci a shiyyar kiyaye halitta ta Wolong, kuma muna maraba da ku a garin Panda. A karshen shirinmu na yau, bari mu maimaita tambayoyin da muke yi muku, da farko shi ne, ko lardin Sichuan gari ne ga dabbobin Panda? Ta biyu kuma, Panda nawa ne suke zaune a cikin shiyyar kiyaye halitta ta Wolong? To, masu sauraro, sai mako na gaba war haka, za mu sake saduwa da ku a cikin shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici ta 'Kai ziyara ga kyakkyawan lardin Sichuan'.
|