Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-15 17:14:36    
An tabbatar da sufuri da sadarwa da kuma cinikayya kai  tsaye tsakanin babban yankin kasar Sin da yankin Taiwan

cri

Jama'a masu sauraronmu, ko kuna sane da cewa, tun daga yau ne aka tabbatar da yin sufuri da sadarwa da kuma cinikayya kai  tsaye tsakanin babban yankin kasar Sin da yankin Taiwan. Hakan ya kirkiro wani irin sabon hali ga inganta dangantake da ke tsakanin gabobi biyu na Zirin Taiwan.

Yau da safe da misalin karfe 8, aka gudanar da bikin bude sabuwar hanyar zirga-zirgar jiragen sama kai  tsaye tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan a filin saukar jirgin sama na Pu Dong na birnin Shanghai, inda Mista Li Jiaxiang, shugaban hukumar kula da harkokin zirga-zirgar jiragen sama na fararen hula ta ma'aikatar sufurin kasar Sin ya yi hira a karon farko cikin tarihi tare da cibiyar sarrafa yanayin zirga-zirgar jiragen sama ta Taipei. Yana mai cewa: "Bari mu rike hannayen juna don kara fadada hanyoyin jiragen sama tsakanin gabobi biyu na mashin teku na Taiwan". Nan take, wani jirgin saman fasinja mai lamba MU 2075 ya tashi daga filin jirgin sama na Pu Dong a Shanghai zuwa filin jirgin sama na Tao Yuan a Taipei. Hakan na nufin cewa, daga wannan lokaci dai, jiragen sama na babban yankin kasar Sin ba su bukatar zagaya yankin Hongkong kafin ya sauka a yankin Taiwan. Wannan dai zai gajarta lokutan zirga-zirgar jiragen sama da akan kashe tsakanin gabobi biyu na Zirin Taiwan.

Jama'a masu sauraro, yau da safe da misalin karfe 9, an gudanar da bikin yin sadarwa kai da tsaye a hukumance tsakanin gabobi biyu na mashigin teku na Taiwan a wata tashar musayar abubuwan sakonni na zirga-zirgar jiragen sama ta Beijing, inda wani tsoho dan shekaru 81 a duniya mai suna Zheng Jian dake zaune a nan Beijing wanda kuma aka haife shi a Taiwan ya aike da wasika ta farko zuwa ga iyalinsa dake yankin Taiwan. Yana mai cewa: " Yau dai ina farin ciki matuka saboda na samu damar aika da wata wasika zuwa ga kanwata. Ina so ta more tare da mu bayan an soma yin sadarwa kai da tsaye tsakanin gabobi biyu na Zirin Taiwan".

Mataimakin shugaban Jam'iyyar Kwamintang Mista Lin Fongzheng ya furta cewa, yin sadarwa kai  tsaye, babban lamari ne da ka iya kawo alheri ga 'yan-uwa na gabobi biyu na Zirin Taiwan. Yana mai cewa: " Yin sadarwa kai da tsaye a ranar yau, labuddah zai samar da sauki ga 'yan-uwa na gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan yayin da suke aikawa da wasiku da abubuwan kunshi da kuma takardun musayar kudi".

Amiai 'yan Afrika, an gudanar da wani gagarumin bikin zirga-zirgar jiragen ruwa kai  tsaye tsakanin gabobi biyu na Zirin Taiwan a karon farko yau da safe a wata tashar jiragen ruwa ta Tianjin, wadda ta fi girma a arewacin kasar Sin. Mista Li Shaode, gami da shugaban babban kamfanin zirga-zirgar jiragen ruwa na kasar Sin ya fada wa wakilinmu cewa: "A da, jiragen ruwanmu sukan yada zango a tashar ruwa ta kasar Japan a kan hanyarsu ta zuwa tashoshin jiragen ruwa na Taiwan. Hakan yanabata lokuta da yawa. Amma yanzu masu karbar kayayyaki da kuma kasuwanni na iya cin gajiyar zirga-zirgar jiragen ruwa kai da tsaye da aka soma yi".

A gun bikin, daraktan ofishin kula da harkokin Taiwan na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, Mista Wang Yi ya furta cewa: " Yin sufuri da sadarwa da kuma cinikayya kai  tsaye tsakanin mashigin tekun Taiwan ya shaida mana wani labarin gaskiya cewa, duk wadanda suka dace da babbar moriyar 'yan-uwa na Zirin Taiwan da kuma bukatun inganta dangantakar dake tsakanin gabobi biyu, labuddah za a iya tabbatar da su bisa kokarin 'yan-uwa na gabobin biyu komai matsalolin da za su samu. Ko shakka babu ya kasance da kyakkyawar makoma ta samun zaman lafiya da bunkasuwar dangantakar dake tsakanin gabobi biyu na mashigin tekun Taiwan." ( Sani Wang )