Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-15 16:33:53    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri
---- Kwanan baya an kafa cibiyar binciken harshe da al'adun kabilar Manchu ta farko ta kasar Sin da ke cikin babban dakin ajiye kayayyakin tarihi na gargajiya na jami'ar horas da malaman koyarwa ta arewa maso gabashin kasar, wannan zai ba da taimako ga yin ceto da kuma ba da kariya ga harshe da al'adun kabilar Manchu.

Bayan kafuwar cibiyar binciken harshe da al'adunn kabilar Manchu, za a dukufa kan aikin farfaganda da yin bincike da yin ceton harshen, da buga littattafai da kuma horas da kwararrun mutane wajen harshe da al'adun kabilar Manchu. A wannan shekarar da muke ciki, cibiyar ta yi shirin buga littafin "Koyarwa kan harshen kabilar Manchu", daga shekara mai zuwa kuma za ta fara aikin buga littattafan kara sani.

An labarta cewa, yawan mutanen Manchu da ake da su yanzu ya wuce miliyan 10 a kasar Sin, amma daga cikinsu yawan mutanen da suke iya magana da harshen Manchu ba su kai 100 ba. Cikin 'yan shekarun nan, bisa kokarin da wasu masanan ilmi da mutanen da abin ya shafa ke yi, an samu kwarin gwiwa wajen binciken harshe da al'adun gargajiya na kabilar Manchu.

---- Kwanan baya an rufe "taron cinikin yawon shakatawa na bakin iyakar kasa na Xishuangbanna" a karo na 11 da aka yi a birnin Jinghong, hedkwatar yankin Xishuangbanna ta kabilar Dai mai ikon tafiyar da harkokin kanta na lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, jimlar kudin da aka samu wajen kasuwar sayar da kayayyaki na nan gaba da na yanzu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 93.5, wato ya karu da kashi 10 cikin 100 bisa na wancan taron cinikin da ya wuce.

An yi wannan taron ciniki ne a daidai lokacin da yankin Xishuangbanna ya shirya bikin al'adu da fasaha na bakin iyakar kasa a tsakanin kasashe 4 wato Sin da Laos da Burma da Tailand, da bikin fasahar kabilun tsakiyar kudancin lardin Yunnan a wannan karo, da yake an yi taron ciniki da bukukuwan 2 a lokaci daya, shi ya sa aka cimma manufar samun bunkasuwa tare wajen tattalin arziki da yawon shakatawa da al'adu.

Masana'antu fiye da 260 da suka zo daga kasashe 7 wato Tailand da Loas da Burma da Vietman da Singapore da Japan da Korea ta kudu, da larduna da jihohi masu ikon tafiyar da harkokin kansu da biranen da ke karkashin gwamnatin tsakiya kai tsaye fiye da 10 na kasar Sin, da yankuna da birane fiye da 12 na lardin Yunnan sun shiga taron cinikin, yawan mutanen da suka halarci taron kuma ya wuce 1,400.