Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-14 17:33:17    
Matan Tibet na kara samun guraben aikin yi

cri
An labarta cewa, mata wadanda aka nuna musu bambanci a lokacin da a jihar Tibet ta kasar Sin, suna kara samun guraben aikin yi a halin yanzu. Haka kuma, mata sun riga sun kasance babban karfi wajen daukaka cigaban tattalin arziki da zaman al'ummar Tibet.

Bisa kididdigar da hukumar bada tabbaci ga harkokin samun guraben aikin yi ta jihar Tibet mai cin gashin kanta ta bayar, an ce, a halin yanzu dai, adadin matan jihar wadanda suke samun guraben aikin yi ya zarce dubu 690, wanda ya dauki kashi 6.7 bisa dari na jimlar yawan mutane a Tibet.

Shugabar hadaddiyar kungiyar 'yan mata ta jihar Tibet mai ikon tafiyar da harkokin kanta, Can Muqun ta furta cewa, matan Tibet na kara samun guraben aikin yi sakamakon gyare-gyare da ake yi ta hanyar dimokuradiyya da manufar yin gyare-gyare cikin gida da bude kofa ga kasashen waje da ake aiwatarwa a jihar. Mata sun samu cikakken 'yanci da rayayyen karfi, wadanda suke kara samun guraben aikin yi da shiga cikin ayyukan zaman al'umma.(Murtala)