Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-12 21:31:48    
Internet a kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Alhaji Sani Yusuf, wanda ya fito daga garin Gusau, jihar Zamfara, tarayyar Nijeriya. A cikin Sakon Email da ya aiko mana, malamin ya ce, shin nawa ne a kasar Sin ke ziyartar internet, kuma yaya harkokin internet ke bunkasa a kasar Sin?

To, alhaji Sani Yusuf, mun gode maka da aiko mana wadannan tambayoyi biyu masu muhimmanci. A hakika dai, tun daga shekarar 1998, a ko wane watan Janairu da na Yuli, cibiyar samar da bayanan internet ta kasar Sin, ko kuma CNNIC a takaice, ta kan gabatar da rahotanni kan bunkasuwar harkokin internet a kasar Sin. Ga shi kuma a ran 24 ga watan Yuli na shekarar da muke ciki, cibiyar ta gabatar da rahoton a karo na 22, wanda ya yi nuni da cewa, yawan mutanen da ke amfani da internet na ci gaba da karuwa cikin sauri a kasar Sin, a farkon rabin shekarar da muke ciki kawai, yawansu ya karu da miliyan 43. Rahoton ya ce, ya zuwa karshen watan Yuni na wannan shekara, yawan mutanen da ke amfani da internet a kasar Sin ya riga ya kai miliyan 253, wato a karo na farko ne ya zarce na Amurka, har ya zo na farko a duniya. Amma duk da haka, matsakaicin yawan mutanen da ke amfani da internet ya kai kashi 19.1% ne kawai a kasar Sin, wanda bai kai kashi 21.1% ba, wato matsakaicin matsayi na duniya. Rahoton ya kuma yi nuni da cewa, daga cikin mutanen da ke amfani da internet a kasar Sin, yawancinsu 'yan makarantar sakandare ne, sa'an nan matan da ke amfani da internet na karuwa, wadanda sun kai kashi 46.4% daga cikin dukan mutanen da ke ziyartar internet.

Ban da wannan, cibiyar samar da bayanan internet ta kasar Sin ta kuma sanar da cewa, ya zuwa ran 22 ga watan Yuli na wannan shekara, yawan tashoshin internet da suka yi rajista da sunan .CN ya kai miliyan 12 da dubu 188, wanda ya wuce .de da ake amfani da shi a kasar Jamus, har ya zo na farko a duniya. Duk wadannan sun bayyana cewa, Sin ta sami babban ci gaba ta fannin bunkasa tashoshin internet.

Ban da wannan, bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan tashoshin internet na kasar Sin na dinga karuwa, wanda ya kai miliyan 1 da dubu 919 a halin yanzu, kuma yana karuwa da kimanin kashi 46.3% a kowace shekara. Daga cikin tasoshin internet da ake samu a kasar Sin a halin yanzu, akwai miliyan 1 da dubu 369 da suke amfani da .cn cikin adireshinsu, wanda ya dau kashi 71.3% na tashoshin internet baki daya a kasar Sin, wanda kuma ya shaida cewa, yanzu akasarin tashoshin internet na kasar Sin na yin amfani da .cn a cikin adireshinsu.

Yanzu internet ya riga ya zama wata muhimmiyar kafar yada labarai a kasar Sin. A nan kasar Sin, yawan mutanen da ke karanta labarai daga shafunan internet ya kai miliyan 206, har ma ya zama abu na biyu da ke jawo jama'a wajen ziyartar tashoshin internet. Ban da karanta labarai, a kan kuma yi amfani da internet wajen sayayya. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, yawan mutanen da ke amfani da internet wajen sayayya ya kai kashi 25% a kasar Sin, musamman ma a birnin Shanghai da ke gabashin kasar Sin, inda adadin ya kai 45.2%.

Yanzu a kasar Sin, jama'a suna kuma amfani da wayoyin salula wajen shiga tashoshin internet. Bisa binciken da aka yi, an ce, a rabin shekarar da ta wuce, kashi 28.9% na masu ziyartar shafunan internet na kasar Sin sun taba yin amfani da wayoyin salula wajen shiga internet. (Lubabatu)