Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-12 18:41:27    
Kasar Sin na daukar matakai domin kara inganta bunkasa tattalin arzikin masana'antu

cri
A sakamakon rikicin kudi a duniya da kuma tabarbarewar tattalin arzikin duniya, yanzu tattalin arzikin masana'antu na kasar Sin na fuskantar mawuyancin hali. Ran 12 ga wata, a nan Beijing, Li Yizhong, ministan masana'antu da fasahar yada bayanai na kasar Sin ya bayyana a gun taron manema labaru cewar, kasar Sin za ta taimaka wa masana'antu su jure wahalar da suke fuskanta a yanzu ta hanyar rage kudin haraji da ba da karin taimako ta fuskar rancen kudi. Sa'an nan kuma, za ta dauki matakan yin kwaskwarima kan fasaha da kyautata tsarin sana'o'i domin aza wa masana'antu harsashi yadda ya kamata wajen samun makoma mai kyau.

A gun taron, Li Yizhong ya bayyana cewa, yanzu masana'antun kasar Sin sun gamu da matsaloli da yawa da ba su taba gamuwa ba a da. Kasar Sin na fuskantar mawuyancin hali a tattalin arzikin masana'antu. Mr. Li ya ce,"A galibi dai, matsalar kudi ta duniya ta rutsa kasarmu sosai, haka kuma, yana kasancewa da manyan batutuwan da muka dade muna tinkararsu, saboda haka, an kara kawo illa ga masana'antu. Mun kiyasta cewa, har yanzu ba mu fita daga mawuyancin hali ba. A watan Disamba da muke ciki, illar da muka samu za ta kara tsananta."

Wannan jami'in Sin ya kara da cewa, matakai 10 na habaka bukata a gida da kuma sa kaimi kan ci gaban tattalin arziki da kasar Sin ta kaddamar da su sun taka rawar gani wajen kara inganta bunkasa tattalin arziki. Ban da wannan kuma, gwamnatin Sin ta fito da wasu matakai domin taimakawa masana'antu matsakaita da kanana da ba su da karfi sosai su jure wahalar da suke fuskanta. Ta rage buga wasu daga cikin wadannan masana'antu matsakaita da kanana haraji tare da ba su karin taimako ta fuskar rancen kudi domin warware matsalar karancin kudade.

Bugu da kari kuma, Mr. Li ya ci gaba da cewa, baya ga wadannan matakan da ya ambata a baya, gwamnatin Sin ta karfafa karfinta na yin gyare-gyare kan fasaha da kyautata tsarin sana'o'i domin sassauta mawuyancin hali da ake ciki. Ya yi karin bayanin cewa, ma'aikatar masana'antu da fasahar yada bayanai ta kasar Sin za ta samar da asusun yin kwaskwarima kan fasaha mai yawan kudin Sin yuan biliyan 15, za ta yi kokari domin shigar da kudin Sin yuan biliyan 300 zuwa biliyan 400 a cikin aikin yin kwaskwarima kan fasaha a masana'antu ta hanyar ba da rancen kudi da ba da taimakon kudi domin biyan kudin ruwa. Ya ce,"Mun gabatar da samar da kudin Sin Yuan biliyan 15 a fannin yin gyare-gyare kan fasaha, za mu dogara da ba da rancen kudi da ba da taimakon kudi domin biyan kudin ruwa, bayan da aka yi bincike kan masana'antu da shirye-shiryen da suka bayar, za a ba su goyon baya. In mun bi irin wannan hanya, na yi imani da cewa, ba kawai za mu iya daidaita matsalar kudi da muke fuskanta a yanzu, kuma za mu iya daga bunkasuwar tattalin arzikinmu ba, har ma wannan zai taka muhimmiyar rawa wajen kyautata tsarin sana'o'i da canza hanyoyin raya tattalin arziki domin shiga mataki na gaba na samun bunkasuwa a daidai wannan lokaci."

Dadin dadawa kuma, kasar Sin za ta kaddamar da yin gyare-gyare kan harajin da ake bugawa kan kayayyakin da aka kara darajarsu a cikin dukkan sana'o'i a duk fadin kasar, a zahiri, za ta soke harajin da ta buga wa masana'antu a fannin sayen injuna. Wannan mataki ya sassauta nauyin haraji da aka danka wa masana'antu tare da bayar da alamar cewa, kasar Sin za ta karfafa gwiwar masana'antu a fannonin kirkire-kirkire da kuma sabunta fasaha. Wang Jun, mataimakin ministan kudi na kasar Sin ya yi bayanin cewa, "Tun daga ran 1 ga watan Janairu na shekara mai zuwa, za a fara gudanar da matakin yin gyare-gyare kan harajin da ake bugawa kan kayayyakin da aka kara darajarsu, don haka, yawan kudaden da ke cikin baitulmalin tsakiya na kasar Sin zai ragu da kudin Sin yuan biliyan 120 ko fiye a ko wace shekara. Za mu yi amfani da wannan kudade domin goyon bayan masana'antu da su sayi sabbin injuna, ta haka za su iya sabunta kayayyakin da suke kera da kuma kyautata tsarin sana'o'i."(Tasallah)