Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-11 17:36:40    
Mr. Li Honggui, wato mai aikin masana'antu na musulmi

cri

Kamfanin harkokin nama na musulmi na Hua Xiang na lardin Hebei yana kebabben wurin kafa masana'antu na Xianghe, shi ne kuma masana'antar zamani da ke da ayyukan kiwo da yanka shannu da awaki, da kuma gyara da sayar da nama. Alamar "Jing Hua Xiang" ta kamfanin ta riga ta zama shahararriyar alama a nan kasar Sin, kayayyakin da kamfanin ya fitar sun bazu a ko wane wurare a dukkan kasar Sin. An samun bunkasuwar kamfanin Hua Xiang sakamakon kokarin da shugaban kamfanin Mr. Li Honggui, da kuma ma'aikatansa suka yi tare.

Bayan da Mr. Li Honggui ya yi ritaya daga rundunar soja a shekarar 1986, sai ya yi aikin tsaro a gidan 'yan sanda na garinsa. Bayan shekaru biyu da suka wuce kuma, sai ya soma cinikin fatan shannu har shekaru 13. A karkashin kokarin da ya yi, ya tattara wasu kudadde, kuma ya koyi wasu fasahohin yanka shannu da awaki, a lokacin kuma, yana fatan kafa kamfanin kansa.

A shekarar 2000, Mr. Li Honggui ya kafa kamfanin Hua Xiang. Kayayyakin da kamfaninsa ya fitar sun shiga manyan hotel da yawansu ya kai 150 a birnin Beijing. Ban da wannan kuma, Mr. Li Honggui ya kafa sassan kamfannoni a wasu manyan birane na kasar Sin, ciki har da Tianjin, da Zhengzhou, da Taiyuan, da Shenzhen, da dai sauransu. Gaskiya ne, ya samu nasara sosai kan kamfaninsa.

Bayan da ya kafa kamfaninsa ba da dadewa ba, sai ya tsara manufar gudanarwar kamfanin ta nuna amincewa. Mr. Li Honggui ya gayawa ma'aikatansa cewa, ba yi karya ba yi yaudara ma'aunin da'a ne na musulmi, kamfaninmu na ba da hidima ga musulmi, saboda haka, ya kamata mu mayar da da'a da amincewa a gaban kome wajen gudanar da kamfaninmu. Ya kamata mu kafa kamfanin Hua Xiang da ya zama wani kamfanin harkokin nama mai da'a da ke bisa imanin musulunci. Mr. Li Honggui yana ta tsayawa tsayin daka kan ka'idoji da ma'auni na musulunci wajen ayyukan yanka, da tanadi, da kuma jigila, har ma kamfaninsa ya samu tabbatarwar musulunci daga majalisar musulunci ta kasar Sin.

Domin kai kamfaninsa kan hanyar zamani, Mr. Li Honggui ya zuba kudi da yawa kan shigar da kayayyaki, da na'urori, da kuma fasahohi irin na zamani, don tabbatar da ingancin nama. A shekarar 2006, Mr. Li Honggui ya samu lambar "Manyan masu aikin masana'antu goma na musulmi na shekarar 2005", a waje daya kuma, an lakantawa samfur "Jing Hua Xiang" suna "Manyan alamomin musulmi guda goma mafi kawo tasiri a nan kasar Sin na shekarar 2005".

Kwararru su babban tushe ne wajen bunkasuwar masana'antu, kara kwarewar masana'anta na ba da tabbaci ga cigaban masana'antu. Mr. Li Honggui ya shigar da kwararru masu kwarewa da yawa cikin harkokin gudanarwar kamfaninsa, kazalika kuma yana mayar da hankali sosai kan horar da ma'aikata. Shi da kansa kuma ya yi kokari kan karatu, bayan 'yan shekaru da suka wuce, ya samu digiri na MBA na kwalejin horarwa ta kimiyyar sha'anin noma. Bugu da kari kuma, ya kan shirya ayyukan horar da ma'aikata kan ilmin da ke da nasaba da abincin musulmi, da kuma gasar fasaha.

Kamfanin Hua Xiang ya yi suna a dukkan kasar Sin, ba saboda ingancin kayayyakin da ya fitar kawai ba, har ma saboda ayyukan sadaka bisa shawarar da Mr. Li Honggui ya gabatar. Li Honggui ya kan ba da taimako ga gidajen tsoffafi da suka rasa kayayyakin yau da kullum, da kuma makarantun da suka rasa kayayyakin karatu. Bayan aukuwar girgizar kasa a gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan a watan Mayu na shekarar da muke ciki kuma, Mr. Li Honggui ya bayar da kudi bisa son rai ga yankuna masu fama da bala'in. A matsayinsa na wani musulmi, Mr. Li Honggui ya mayar da hankali kan masallatai. Har sau uku ne ya bayar da kudi don gyara masallatai., a waje daya kuma, ya yi kira ga sauran masana'antun musulmi da su bayar da kudi tare kan wannan.

Bayan haka kuma, Mr. Li Honggui ya samu tabbaci daga gwamnatin wurin saboda ya taimakawa manoma da su yi kiwon shannu da awaki domin samun wadatuwa. A karkashin taimakon da ya bayar, manoma musulmi da yawa sun kawar da talauci, wasu kuma sun gina sabbin gidaje, da sayi motoci.

Kamfanin Hua Xiang ya samu babban cigaba a karkashin kokarin da Mr. Li Honggui da ma'aikatansa suka yi, nan gaba kuma, za su kara kokarinsu don cimma babban burinsu na fita daga gida, za su kara mayar da hankali kan gudanarwar kamfaninsu, da kara ingancin kayayyaki, da wadatar kayayyaki, da kuma kara karfin raya kasuwa, ta yadda za su gabatar da kayayyakinsu ga musulmi, da sauran abokai na dukkan duniya.