Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-10 18:36:04    
Kasar Sin tana fatan kafuwar kwalejin Confucius za ta sa kaimi kan raya kasancewar al'adu da yawa a duniya

cri
Ran 9 ga wata, a nan Beijing, an bude babban taron kwalejojin Confucius a karo na 3 na tsawon kwanaki 2, inda shugabannin kwalejojin Confucius daga sassa daban daban na duniya da kuma na jami'o'i fiye da dari 5 suka halarci taron. A gun bikin bude taron, madam Liu Yandong, shugaban kwamitin zartaswa na babban zauren kwalejin Confucius ta bayyana cewa, harsuna da al'adu na matsayin gada ce ta zurfafa zumunci da amincewa a tsakanin jama'ar kasashen duniya. Gwamnatin Sin tana fatan kafuwar kwalejojin Confucius za ta iya sa kaimi kan raya kasancewar al'adu da yawa a duk fadin duniya.

Madam Liu ta yi karin bayani da cewa,"A halin yanzu, kasar Sin ta riga ta kafa kwalejojin Confucius 249 da kuma dakunan karatu na Confucius 56 a kasashe da yankuna 78. Tana shirya kwasa-kwasai na koyon Sinanci sau dubu 6 ko fiye a makarantun firamare da na midil da jami'o'i da unguwanni da kuma masana'antu ta hanyoyi daban daban bisa halin da suke ciki, mutane kimanin dubu 130 sun yi rajista. Ban da wannan kuma, an shirya harkokin yin mu'amalar al'adu iri daban daban masu kayatarwa, inda mutane fiye da miliyan 1 da dubu 400 suka halarta."

An yi karin bayani cewa, wadannan kwalejojin Confucius da ke sassa daban daban na duniya suna koyar da Sinanci ta hanyoyi da dama a fannoni daban daban, sa'an nan kuma, suna shirya jerin kwasa-kwasai da harkokin da ke nuna al'adun al'ummar Sin bisa halayen musamman na wurin. Alal misali, a kwalejin Confucius da ke jami'ar London South Bank ta kasar Birtaniya, ana koyar da ilmin likitancin gargajiya na kasar Sin, wanda ya sami karbuwa sosai a wurin.

Timothy O'Shea, shugaban jami'ar Edinburgh ta Birtaniya ya bayyana cewa, wadannan harkokin da ake yi a kwalejojin Confucius sun kyautata sanin mazauna wurin kan kasar Sin. Ya ce,"A shekarar bana, kwalejin Confucius da ke jami'armu ta shirya shekarar al'adu ta kasar Sin na tsawon watanni 10, inda ta hada da harkokin 115, mutane kusan dubu 17 daga jami'armu da kuma sauran wurare sun shiga ciki."

An ce, domin samar da dandalin yin mu'amala a tsakanin kasashen duniya, kwalejin Confucius ta gayyaci shugabannin makarantun midil da na firamare da malamai da 'yan makarantu fiye da dubu 1 da dari 5 da suka zo daga kasashen Amurka da Birtaniya da Japan da su zo kasar Sin. Haka kuma ta horar da malaman koyar da Sinanci fiye da dubu 20 domin kasashe da yankuna fiye da 40. Bugu da kari kuma, kasar Sin ta aika da malaman koyar da Sinanci da masu aikin sa kai kusan dubu 4 zuwa kasashe fiye da 150."

Domin kyautata tafiyar da kwalejojin Confucius, yanzu babban zauren kwalejin Confucius yana kokarin samar da littattafai da kamus na koyar da Sinanci cikin harsuna 43 da ake amfani da su a duk duniya. Makasudinsa shi ne tabbatar da ganin dukkan kasashen da ake koyar da Sinanci a ciki za su iya amfani da littattafan da kasar Sin za ta samar. Ban da wannan kuma, babban zauren kwalejin Confucius ya yi shirin gabatar da littattafai kan al'adun kasar Sin masu saukin ganewa. Dadin dadawa kuma, kasar Sin za ta fito da asusun kwalejin Confucius a shekara mai zuwa, za ta gayyaci malaman koyar da Sinanci na waje da 'yan kwalejin Confucius da dalibai masu dalibta dubu 3 su yi karatu a kasar Sin.

A gun bikin bude taron da aka yi a wannan rana, madam Liu ta bayyana cewa,"Jama'ar Sin na mai da hankali kan koyon harsunan kasashen duniya da kuma al'adunsu. Yanzu a kasar Sin, mutane fiye da miliyan 200 suna koyon harsunan waje, kana kuma, a jami'o'in kasar Sin, ana koyar da harsuna fiye da 60 na kasa da kasa. Sa'an nan kuma, kasar Sin na maraba da kasashen duniya da su zo kasar Sin domin yayata harsunansu da al'adunsu, yanzu kasashe da yawa suna tafiyar da makarantun koyar da harsunansu da al'adunsu a kasar Sin. Gwamnatin Sin tana samar musu da yanayi na sauki da sharadi mai kyau cikin himma."(Tasallah)