Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-09 19:46:54    
Fahimtar ainihin addinin Buddha a manyan duwatsun Emeishan da Leshan

cri

Jama'a masu sauraro, muna muku godiya da sauraren shirinmu na musamman na gasar kacici-kacici wato 'Kai ziyara ga kyakkyawan lardin Sichuan'. A cikin shirinmu na yau, za mu kai ziyara ga manyan duwatsun Emeishan da Leshan. Kafin mu soma shirinmu na yau, bari mu yi muku tambayoyi 2 tukuna. Da farko shi ne ko babban dutse na Emeishan na daya daga cikin wurare masu tsarki na addinin Buddha na kasar Sin ko a'a? Na biyu, mutum-mutumin babban Buddha na Leshan mutum-mutumi ne mafi girma na Buddha a duk duniya, tsayinsa ya kai mita nawa ne? To, bari mu fara ziyararmu a yau!

Babban dutse na Emeishan ya zama na farko a duk kasar Sin tun zamanin da can. A cikin dukkan sanannun manyan duwatsu na kasar Sin, babban dutse na Emeishan mai tsayin mita fiye da dubu 3 yana kan gaba a fannin tsayi. Tsire-tsire iri daban daban suna yaduwa saboda zafin nan ya sha bamban sosai a tsakanin kololuwar wannan babban dutse da kuma gindinsa. Bisa kididdigar da aka yi, yawan ire-iren tsire-tsiren da aka samu a babban dutse na Emeishan ya zarce dubu 5, wanda ya yi daidai da jimlar ire-iren tsire-tsiren da aka samu a dukkan kasashen Turai, daga cikinsu kuma akwai wasu ire-irensu da ba safai a kan gan su ba a sauran sassan duniya. In mutum ya sa kafa a kan babban dutsen, sai idanunsa su yi arba da korayen ganye saboda tsoffin dogayen itatuwa suna kan gefunan hanyoyi. Kyan ganin babban dutsen Emeishan ya sha bamban sosai bisa sauye-sauyen yanayi da kuma bambancin tsare-tsaren babban dutsen. Mun iya gano kyan ganin wannan babban dutse daga sunansa a Sinance, bisa abubuwan da ke cikin littattafan tarihi, ma'anar Emei a bakin Sinawa a can da shi ne gashin girorin wata budurwa. An kwatanta babban dutsen Emeishan da wata kyakkyawan budurwa.

Halin musamman da babban dutse na Emeishan ke nunawa ya danganta da al'adun addinin Buddha, wanda ya aza harsashi a nan sosai. A cikin karni na 1, an yada addinin Buddha daga kasar Indiya zuwa babban dutse na Emeishan, an kuma gina gidan ibada na addinin Buddha na farko na kasar Sin a nan. Saboda kafuwar sauran gidajen ibada na addinin Buddha da ke kewayensa, babban dutse na Emeishan ya zama daya daga cikin wurare masu tsarki na kasar Sin a fannin yada addinin Buddha sannu a hankali. Mutane suna ta yin aikin ibada a nan.

Ana nuna wa Bodhisattva mai suna Puxian girmamawa a babban dutsen Emeishan. Yanzu 'yan addinin Buddha maza da mata kamanin 300 suna zaune a gidajen ibada na addinin Buddha kusan 30 a babban dutsen.

Ganiyar babban dutse na Emeishan da ake kiransa 'kololuwa ta zinariya', wato Golden Summit a Turance, shi ne anihin kyan ganin wannan babban dutse. Ban da manyan zauruka masu girma guda 3, mutum-mutumin Bodhisattva mai suna Puxian mai tsayin mita misalin 48 da aka yi da zinariya ya fi jawo hankulan mutane.

Mr. Lee Geun Won wanda ke nuna imani sosai ga addinin Buddha, ya zo babban dutsen Emeishan daga mahaifinsa kasar Korea ta Kudu don bauta wa Bodhisattva mai suna Puxian. Ya ce, "Na ji a zuciyata cewa, kasar Sin wata kasa ce mai girma! Saboda na ga mutum-mutumin Bodhisattva mai suna Puxian mai girma hakan a babban dutse na Emeishan. Na durkusa a gaban mutum-mutumin Bodhisattva mai suna Puxian har sau 10, na durkusa sau 3 a cikin manyan zauruka 3, ban da wannan kuma, na ba da kyautar kudi, ko da yake ba shi da yawa, amma ina son in bayyana imanina."

Kololuwar zinariya ta babban dutse na Emeishan ba ma wurin aikin ibada ne kawai ba, har ma shi ne wuri mafi dacewa da jin dadin kallon fitowar rana da kuma tekun gajimare.

Bugu da kari kuma, in sun taki sa'a, masu yawon shakatawa za su iya ganin hasken Buddha mai matukar daraja a wannan ganiyar babban dutsen. Ana kiran wannan haske 'Buddha's Halo' a Turance. Hasken rana yana kasancewa kamar wani zobe mai launuka 7, inuwar mutane tana tsakiyar wannan zobe, in mutane sun yi tafiya da kafa, to, wannan kyakkyawan zobe yana tafiya. Wannan yana da ban mamaki ainun. An samu wannan haske mai ban mamaki ne saboda hasken rana da tsare-tsaren kasa da sauran dalilai sun taka rawarsu tare. Masu sauraro, ko kuna sha'awar kawo wa babban dutsen Emeishan ziyara? Ko za ku taki sa'ar kallon wannan kyakkyawar zobe?

Addinin Buddha ya taka muhimmiyar rawa a fannin bunkasuwar babban dutsen Emeishan, ya kyautata al'adu na wannan babban dutse. Musamman ma dimbin gidajen ibada na addinin Buddha da mutum-mutumin Buddha su ma sun nuna muhimmanci sosai ta fuskar al'adu kamar yadda ni'imtattun wurare na babban dutse na Emeishan suke kasancewa. Shi ya sa, Hukumar ilmi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta tanadi wannan babban dutse a cikin takardar sunayen wuraren tarihi na al'adu da na halitta na duniya.

Yanzu babban dutsen Emeishan ba ma kawai ya jawo hankulan mutanen da suka zo daga kasashen Asiya, kuma al'adunsu sun kusan yi daidai da na kasar Sin ba, a shekarar bara, wannan babban dutse ya zama daya daga cikin wuraren yawon shakatawa a kasar Sin da mazauna kasashen Turai suke fi son kawo musu ziyara. Du Hui, wani jami'in kula da wurin yawon shakatawa na babban dutsen Emeishan ya bayyana cewa, na'urorin yawon shakatawa a babban dutsen na samun kyautatuwa sannu a hankali, babban dutsen Emeishan yana maraba da abokai daga kasashen duniya. Mr. Du ya ce,"Na'urorin da ake amfani da su a babban dutsen Emeishan sun sami kyautatuwa. Muna amfani da motocin yawon shakatawa da hanyar zamani wato kebir da hanyoyin masu tafiya da kafa da dai sauransu. Mun gina otel-otel masu taurari 3 zuwa 5 a nan, wadanda suke da gadaje fiye da dubu 3. Mun gina su da kuma yi musu kwaskwarima ne bisa ma'aunin kasashen duniya."

Masu sauraro, idan babban dutsen Emeishan bai ishe ku ba, kuna son su kara fahimta kan addinin Buddha, to, a wurin da ke da nisan kilmita 30 a tsakaninsa da babban dutsen Emeishan a yamma, akwai mutum-mutumi na Buddha mai girma da Sinawa su kan kira shi Leshan Dafo, wanda ya fi girma a duk duniya. Bayan ganin wannan mutum-mutumin Buddha mafi girma a duk duniya, tabbas ne za a mamaki da imanin da masu bin addinin Buddha suka nuna ga addinin Buddha a zamanin da.

An fara sassaka wannan mutum-mutumi mai tsayin mita 70 ko fi a jikin babban dutse don yin kaka-gida a koguna a misalin shekara ta 700. Tsayinsa ya yi daidai da na wannan babban dutse. An yi shekaru misalin 90 ana sassaka shi. Mutanen yanzu sun yi mamaki sosai domin nagartacciyar fasaha ta zamanin da, da kuma jarumtakar da mutane suka nuna a lokacin da suka sassaka wannan mutum-mutumin Buddha. Saboda haka, masu bin addinin Buddha da yawa sun zo nan domin nuna girmamawa, Norbu Rinpoche, wanda 'yan kabilar Tibet ke kiransa Huofo, wato Buddha da ke kasancewa a duniya, ya zo nan domin nuna wa babban mutum-mutumin Buddha din nan wato Leshan Dafo girmamawa daga gidan ibada na Dong Na La Qing a lardin Qinghai da ke yammacin kasar Sin, ya gaya mana cewa,"A ganin mu dukkan 'yan addinin Buddha, mun iya kwantar da hankulanmu da kuma kyautata hazakarmu sosai saboda kawo ziyara da kuma nuna girmamawa ga wannan babban mutum-mutumin Buddha mai girma kuma mai dogon tarihi, wanda ya nuna kirki da kuma tausayin mutane bisa kamanninsa."

Jama'a masu sauraro, ko kuna bin addinin Buddha, ko ba ku bi addinin, kyawawan wurare masu ni'ima na manyan duwatsun Emeishan da Leshan da kuma al'adun addinin Buddha mai dogon tarihi da ban mamaki sun cancanci ku kawo musu ziyara.

To, kafin mu sa aya ga shirinmu na yau, bari mu maimaita tambayoyin da muka yi muku. Da farko shi ne ko babban dutse na Emeishan na daya daga cikin wurare masu tsarki na addinin Buddha na kasar Sin? Na biyu, mutum-mutumin babban Buddha na Leshan mutum-mutumi ne mafi girma na Buddha a duk duniya, tsayinsa ya kai mita nawa ne?