Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-09 19:43:46    
'Yan sama-jannati na kumbon kirar "Shenzhou-7"

cri

An haifi dukkan 'yan sama-jannti uku na kumbon kirar "Shenzhou-7" a shekara ta 1966, an zabe su da su shiga kungiyar gudanar da aikin zirga-zirgar kumbon kirar "Shenzhou-7" mai dauke da mutane a watan Yuni na shekara ta 2008, kuma su ne 'yan sama-jannti na rukuni na uku na kasar Sin wajen zirga-zirgar sararin sama, wato bayan Yang Liwei na rukuni na farko da Fei Junlong da Nie Haisheng na rukuni na biyu. Wasu daga cikinsu sun taba shiga kungiyar zirga-zirgar kumbon kirar "Shenzhou-5" da na "Shenzhou-6", amma a karshe dai ba a harba su zuwa sararin samaniya ba. Bayan da aka kafa babbar kungiyar zirga-zirgar sararin sama ta kasar Sin a shekara ta 1998, sun dade suna jiran zuwa sararin sama har kusan shekaru goma. A karshe dai sun cimma wannan burinsu a shekara ta 2008. To, yanzu bari mu kara fahimtar wadannan 'yan sama-jannati uku.

Zhai Zhigang, an haife shi a watan Oktoba na shekara ta 1966 a birnin Qiqiha'er na lardin Heilongjiang da ke arewa maso gabashin kasar Sin. A shekara ta 2008, an zabe shi da ya shiga kungiyar gudanar da aikin zirga-zirgar kumbon kirar "Shenzhou-7", kuma a cikin aikin fitowa daga kumbon, Zhai Zhigang ya kula da aikin yin tafiya a sararin sama, ta haka ya zama mutum na farko na kasar Sin wajen yin tafiya a sararin sama. Bayan da ya kammala aikin cikin nasara, Zhai Zhigang ya fara yin hira tare da jama'a a doron kasa a cikin kumbon, yana cewa "Muna cikin koshin lafiya, muna yin gwajin ilmin kimiyya kan sararin sama bisa shirin da aka tsara, kuma mun kammala aikin fitowa daga kumbo lami lafiya. Ina jin dadin tafiya a sararin sama, kuma tufafin da na sanya don yin tafiya yana da matukar kyau. Na fi yin alfahari da kasarmu lokacin da nake makeken sararin samaniya."

An haifi Liu Boming a watan Satumba na shekara ta 1966 a gundumar Yi'an ta lardin Heilongjiang. A cikin aikin fitowa daga kumbo, Liu Boming ya kula da aikin taimaka wa Zhai Zhigang, da kuma sarrafa wasu injuna. Liu Boming ya bayyana cewa, aikin zirga-zirgar sararin samaniya wani irin aiki ne da aka shirya don jarumai, domin sauke wannan nauyin musamman da aka dora masa, Mr. Liu ya rinka yin kokari. Kuma ya ce, "Bisa wani matsayi, sararin sama ya fi jawo hankalina in an kwatanta da doron kasa, shi ya sa na yi kokari har shekaru 10 wajen tsayawa tsayin daka kan aniyar zuwa sararin sama, kuma ban taba yin watsi da ita ko kadan ba."

Jing Haipeng, an haife shi a watan 10 na shekara ta 1966 a birnin Yuncheng na lardin Shanxi. A cikin aikin yin tafiya a sararin samaniya, ya kula da aikin da ke cikin kumbo, wato sanya ido kan halin da kumbon ke ciki domin tabbatar da lafiyar kumbon da kuma yin saduwa da doron kasa. Jing Haipeng ya bayyana cewa, a cikin wannan kungiyar aiki, amfaninsa shi ne samar da goyon baya ga sauran mutane biyu da kuma hadin gwiwa sosai tare da su. Kuma ya kara da cewa, "Halina na musamman shi ne samar da taimako gare su, wato lokacin da suke yin tafiya a sararin sama, na dudduba abubuwan da ba a mai da hankali a kai ba a cikin kumbon domin tabbatar da lafiyar kumbon. Shi ya sa a ganina, lokacin da muke gudanar da aiki, ciki har da horon da muka yi a doron kasa, aikina shi ne yin iyakacin kokari wajen share fage da hadin gwiwa tare da su da samar da goyon baya da taimako gare su."