Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-09 13:58:59    
Afirka ta samu cigaba kan daidaita matsalar shiyya-shiyya bisa karfin kanta a shekarar 2008

cri

Nahiyar Afirka tana taka muhimmiyar rawa a siyasar kasa da kasa. A shekarar 2008, yawancin kasashen Afirka sun samu bunkasuwar tattalin arziki da hauhawar matsayinsu a cikin kasashen duniya, wannan ya karfafa gwiwoyinsu kan neman daidaita matsalar nahiyar bisa karfin kansu. Wannan hanyar da ake binta ta sa kasashen Kenya da Zimbabwe, daya bayan daya suka kau da matsalar da suka fuskanta a wajen siyasa.

'Ina so in gaya wa membobin tawagar shahararrun mutanen Afirka, da Mista Benjamin Mkapa, tsahon shugaban kasar Tanzaniya, da kuma dukkan jama'ar Kenya cewa, yau mun gama shawarwarinmu, wato yadda za mu kawo karshen rikicin siyasa a Kenya '

Mista Annan, tsohon sakataren janar MDD ya fadi haka ne, lokacin da aka kafa gwamnatin raba madafun iko a kasar Kenya a farkon rabin shekarar bana, bisa kokarin sulhuntawar da tawagar shahararrun mutanen Afirka da Mista Annan, da ke shugabantar tawagar, suka yi. Bayan batun, bai kai rabin shekara ba, shugabannin manyan jam'iyyun siyasar kasar Zimbabwe sun sa hannu kan yarjejeniyar raba madafun iko, sun kafa gwamnatin hadin gamin gambiza, a sabili da sulhuntawar da Thabo Mbeki, shugaban kasar Afirka ta Kudu na lokacin ya yi.

Daidaita matsalar shiyya-shiyya bisa karfin kansu wani buri ne na kasashen Afirka cikin lokaci mai tsawo. Samun nasarar daidaita matsala a Kenya da Zimbabwe alama ce da ke nuni da cewa, Afirka ta samu babban cigaba kan hanyar neman cika burin. Lumumba Kaluma, wani lauyan kotun koli na kasar Kenya, ya samu ganin sauyin da idanunsa.

'A da, yayin da ake kula da batun Congo Kinshasa. Wadanda suka isa kasar kafin sauran mutane su ne ministocin harkokin waje ne na kasashen Birtaniya da Faransa, da ganin hakan ya faru, na ji bakin ciki. A lokacin , ban ga wakilan kasashen da ke makwabtaka da kasar Kenya da suka zo kasar ba, balle ma na ji muryar kungiyar tarayyar Afirka ta AU. Amma yanzu mun fara ganin fuskokin 'yan Afirka yayin da kasashen Afirka ke neman daidaita matsalar nahiyar, wannan wani mafari mai kyau ne.'

Aikin da kungiyar AU ya yi ya zama daya daga cikin dalilan da suka sa kasashen Afirka suka samu irin wannan cigaba. Cikin ayyukan da ta yi na shirya shawarwari tsakanin bangarori daban daban na kasashen Kenya da Zimbabwe da Kongo Kinshasa , da na kare zaman lafiya a kasashen Somaliya da Sudan, kungiyar AU ta nuna niyyarta ta kare kwanciyar hankali a nahiyar Afirka.

Nicolas Bwakira, manzon musamman na kungiyar AU mai kula da batun Somaliya ya ce, 'Idan mu duba al'amuran kasashen duniya, za mu sane cewa, nahiyar Afirka ta riga ta nuna halinta na hadin gwiwa. Karfinmu na da iyakarsa, amma bisa karfin kanmu, mu je Somaliya, mu je Congo Kinshasa, ba wai don kiyaye zaman lafiya ba, muna zuwa wadannan kasashe ne don shifimda muhallin da zai haifar da zaman lafiya.'

Bunkasuwar Afirka na bukatar goyon baya daga gamayyar kasa da kasa, amma wannan goyon baya ba wai umarci kasashen Afirka da su yi kaza, ba tare da kula da halin da kasashen ke ciki ba. Bari mu saurari maganar da Mista Annan ya yi, lokacin da ya sauka a Narobi a ran 22 ga watan Janairu na shekarar bana don daidaita matsala a Kenya. 'Ba mu zo da wani shirin da za mu bi ba. Za mu nemi hanyar da ya dace da aikin daidaita matsala, kuma zai amfana wa kasar Kenya da jama'ar Kenya da nahiyar Afirka gaba daya '. Ya ce, ba su je Kenya tare da wani shirin da ya kamata a bi shi ba. Wannan halin da Mista Annan ya nuna na girmama kasashen Afirka ya sa aka samu nasarar kawo karshen rikicn kasar Kenya. (Bello Wang)