Da safiyar ranar Alhamis din nan ne, aka kaddamar da shawarwari tsakanin Sin da Amurka kan harkokin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare a karo na 5 a nan birnin Beijing, inda mataimakin firaministan kasar Sin Wang Qishan, da ministan kudin Amurka Henry M. Paulson suka shugabanci tawagoginsu domin halartar shawarwarin. A wajen bikin kaddamar da shawarwarin, bangarorin biyu sun yi jawabin cewar, suna fatan ta hanyar yin shawarwarin ne za su cigaba da yin musayar ra'ayi kan muhimman batutuwan tattalin arziki tsakaninsu, da yin kokari kafada da kafada domin cimma daidaito da nasarori.
An kaddamar da shawarwari tsakanin Sin da Amurka kan harkokin tattalin arziki bisa manyan tsare-tsare a wannan karo ne a lokacin da matsalar hada-hadar kudi ke addabar dukkanin duniya, haka kuma kasar Amurka ta zabi sabon shugabanta ba da jimawa ba, shi ya sa shawarwarin sun kara jawo hankalin duniya. A cikin jawabin da ya yi a gun bikin bude shawarwarin, Wang Qishan ya jaddada cewa, yayin da duniya ke fuskantar kalubale mai tsanani a fannin tattalin arziki, inganta hadin-gwiwar kasashen Sin da Amurka ta hanyar yin shawarwari na da muhimmanci kwarai da gaske, inda ya bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin kan tinkarar matsalar hada-hadar kudi ta duniya:"Bayan barkewar matsalar hada-hadar kudi, bangaren Sin ya rika bada hadin-kai ga bangaren Amurka, domin nuna masa goyon-baya wajen tabbatar da dorewar kasuwannin hada-hadar kudi. Abun da ya kamata a ba fifiko shi ne, a sa kaimi ga tabbatar da daidaiton da aka cimma a wajen taron koli tsakanin kasashe membobin kungiyar G-20 kan kasuwannin kudi da tattalin arzikin duniya, da farfado da imanin kasuwanni ba tare da bata lokaci ba, da hana yaduwar matsalar hada-hadar kudi, domin riga-kafin koma-bayan tattalin arzikin duniya, musamman ma a rage illar da matsalar kudi ke kawowa kasashe masu tasowa."
Wang ya kara da cewa, Sin ta rigaya ta dauki kwararan matakai domin bunkasa tattalin arziki da kyau kuma cikin sauri, ciki har da gudanar da manufar kudi kamar yadda ya kamata, da kara biyan bukatun jama'a cikin gida, da dai sauransu. Lallai kasar Sin tana bayar da muhimmiyar gudummowa ga cigaban tattalin arzikin duniya.
Rayawa da yin amfani da sabon makamashi cikin hadin-gwiwa, fanni ne da kasashen Sin da Amurka suke maida hankulansu dukka a kai. Wang Qishan ya nuna cewa, bayan da bangarorin biyu suka rattaba hannu kan takardar yin hadin-gwiwa tsakanin Sin da Amurka a fannonin makamashi da muhalli, an samu babban cigaba a fannoni da dama wajen gudanar da hadin-gwiwarsu, ciki har da harkokin ruwa, da iska, da wutar lantarki, da sufuri da dai sauransu. Wang yana fatan bangarorin biyu za su karfafa hadin-gwiwa ta hanyar shawarwarin.
"Fasahohin Amurka a harkokin makamashi da muhalli na kan gaba a duniya, a halin yanzu, Sin tana gaggauta aikin yin tsimin makamashi da rage fitar da yawan abubuwa masu gurbata muhallin halittu. Ina fatan bangarorin biyu za su cigaba da gudanar da aikin cude-ni-in-cude-ka a fannin fasahohi."
A nasa bangare kuma, ministan kudin Amurka Henry M. Paulson ya nuna babban yabo ga rawar a-zo-a-gani da kasar Sin ke takawa wajen shawo kan matsalar hada-hadar kudi, da muhimmiyar rawar da shawarwari tsakanin Sin da Amurka kan harkokin tattalin arziki ke takawa wajen daukaka cigaban huldodin kasashen biyu, inda ya nuna cewa:"Yayin da ake samun kiki-kakar ciniki, shawarwarin Sin da Amurka na taimaka mana wajen daidaita matsalolin zuba kudi. Yanzu, bangarorin biyu na sa himma wajen yin shawarwari kan yarjejeniyar bada kariya ga harkokin zuba jari, ta yadda jama'ar kasashen biyu za su samu alfanu."(Murtala)
|