Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-05 21:25:11    
Jan kyalle, duniya da babu nuna bambanci

cri
A wannan mako, za mu amsa tambayar malam Isa Babangida, wanda ya fito daga Kano, Nijeriya. Kwanan nan, malam Isa ya rubuto mana cewa, ranar 1 ga watan Disamba rana ce ta yaki da cutar kanjamau a duniya, kuma ana iya ganin alamar nan da ake kira "red ribbon" a bukukuwan da aka shirya na yaki da cutar. To, shin mene ne ma'anar alamar? Ina fatan za ku ba ni tarihinta.

To, alamar nan ta "red ribbon" ko kuma "jan kyalle", alama ce da ake amfani da ita a duniya wajen yaki da cutar sida.

A karshen shekarun 1980, jama'a na daukar cutar sida a matsayin cuta mai ban tsoro, kuma an nuna bambamci sosai ga masu cutar. A gun wani taron duniya da aka yi kan cutar sida, masu cutar sun yi kira ga jama'a da su fahimce su, kuma an jefa wani jan kyalle mai tsawo sosai a saman wurin taron, magoya bayansu sun yanka shi gajajjeru, sun nade su sun sanya a gaban kirji. Daga baya, kungiyoyi da sassan kiwon lafiya da wayoyin neman shawarwari da dama sun sa sunan "jan kyalle", har ma sannu a hankali, jan kyalle ya zama alamar duniya ta fuskar kira ga al'umma su mai da hankulansu kan yaki da cutar sida, da nuna kulawa ga masu cutar.

Tun lokacin da manazarta na Amurka suka gano mai cutar sida ta farko a duniya a shekarar 1981, cutar ta yi ta yaduwa cikin sauri a duk fadin duniya, har ma ta zama abin da ke daukar hankulan duniya baki daya. Yanzu a duk duniya, akwai masu dauke da cutar kimanin miliyan 33 da dubu 200.

Kowace ranar 1 ga watan Disamba rana ce ta yaki da cutar sida a duniya. A ran 30 ga watan Nuwamba, a shekar tsuntsu, wato babban filin wasan kasar Sin da ke birnin Beijing, inda aka gudanar da wasannin Olympic a watan Agusta na bana, an daga wasu manyan jajayen kyalle masu tsawon mita 20 da fadin mita 17. Ashe, a ran nan a wurin, babbar kungiyar "Red Cross" ta kasar Sin da ma hukumar UNAIDS sun gudanar da babban bikin da ke da taken "buri daya, duniya da babu nuna bambanci".

A wurin bikin, kungiyoyin duniya da hukumomin gwamnati da kuma wasu kungiyoyin jama'a wadanda ke gudanar da ayyukan yaki da cutar sida sun kafa rumfunan wayar da kai, don fadakar da jama'a a kan cutar.

Mr.Pu Cunxin, wani shahararren dan wasan kwaikwayo na kasar Sin, wanda aka nada shi a matsayin manzon yaki da cutar sida, ya ce, yanzu al'umma sun kawar da nuna bambanci ga masu cutar sida, wannan muhimmin tabbaci ne wajen shawo kan cutar. Ya kuma ce, "Bisa kokarin da muka yi cikin 'yan shekarun baya, mun kara fadakar da al'umma a kan cutar sida, wannan babban cigaba ne."

Kang Xu, wata daliba mai aikin sa kai ta ce, "Sabo da mu nuna babu bambanci ga masu cutar sida, na taba shiga darasin , kuma an ilmantar da ni a kan cutar. Ina ganin ya kamata mu kara nuna kauna da kulawa ga masu cutar."

Jan kyalle ya hada jama'ar duniya a gu daya ta fannin yaki da cutar sida, kuma ita alama ce ta goyon baya da ake nunawa masu cutar, haka kuma alama ce ta kaunar rayuka da zaman daidaici.(Lubabatu)