Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-05 15:59:52    
Kayayyakin tarihi na al'adun kabilar Hezhe sun kara haske

cri
Kabilar Hezhe tana daya daga cikin kananan kabilun da ke da mutane marasa yawa a kasar Sin. 'Yan kabilar suna zama a gabobin kogin Wusuli da ke arewa maso gabashin kasar Sin daga zuri'a zuwa zuri'a, ba su da kalmomin harshe, amma suna da fasahar wake-waken gargajiya da suka yi da harshensu na kansu a cikin tarihin da yawan shekarunsa ya wuce 100, wato ana kan kiran fasahar da cewar wai Yimakan. Dayake an sami sauyawar hanyar zaman rayuwa, a wani lokaci, fasahar gargajiyar da ke da tarihin da ya wuce shekaru 100 ta taba fuskantar rikicin mutuwa. A shekarar 2006, fasahar Yimakan an mayar da ita cikin littafin tanada sunayen kayayyakin tarihi na al'adu ba kayayyaki ba a rukunin farko na kasar Sin. Bisa kokarin da bangarori daban daban suka yi, ana soma rera wakar Yimakan a tsakanin jama'ar kabilar Hezhe.

Jama'a masu sauraro, abin da kuke saurara yanzu shi ne wakar da dan kabilar Hezhe mai suna Wu Liangui ya rera a babban dakin taruwar jama'a na birnin Beijing a lokacin da aka murnar ranar cika shekaru 30 da kafa Jamhuriyar Jama'ar Sin . Wadanda suka zo daga bayansa sun bayyana cewa, a wancan lokaci, mawaki Wu Liangui ya sanya riguna masu kauri sosai, kuma ya sanya kyalle da ke da kusurwoyi uku a kansa , ya nuna fasahar Yimakan a dakalin nuna wasannin fasaha, wani lokaci, muryarsa ta musamman ta fito ne tare da sauti mai laushi, wani lokaci ma muryarsa ta fito ne tare da sauti mai lankwashe, 'yan kallo da masu saurarensa suna jin nishadi tamkar yadda suke shan giya suke buguwa.

Fasahar Yimakan ana mayar da ita bisa matsayin littafin koyarwa a kan al'adun kabilar Hezhe. An mai da hankali ga bayyana tarihin kabilar da jarumansu da aikin kawo albarka a zamantakewar al'umma da al'adar gargajiya da addinansu, salonta shi ne, ana Magana a wani lokaci, a wani lokaci daban kuma ana rera waka, mawaka sun yi tunani sosai tare da nuna mamaki, kuma suna habaici tare da sha'awa sosai, har ma suna kwaikwayo hirar da mutane daban daban suka yi da kukan tsuntsaye, kai, abin da suka yi tamkar yadda aka yi cikin gaskiya sosai, kakani-kakanin 'yan kabilar Hezhe sun rera wakoki sun ji nishadi bayan da suka fama da wahaloli da yawa, sa'anan kuma sun sami babban karfi wajen yin aikin wurjanjan.

Amma, yanzu ba su da yawa da suka iya rera wakar Yimakan, Malam Wu Liangui yana daya daga cikin wadanda suke iya rera irin wannan waka. Bayan mutuwarsa, sai jikansa mai suna Wu Baochen ya gaji fasahar, ya bayyana cewa,

A bakin kogin Helongjiang, da akwai wani tsohon garin da ake kira "Jiejunkou", muna kan hawan tsaunin da ke gabashin garin, muna rera waka , muna fuskantar inda rana take fitowa.

To yanzu za mu sanya muku wata wakar da ke da lakabi haka: wakar jiragen ruwa da ke zirga-zirga a Kogin Wusuli. To ga ta:

wata Magana da ta sifanta zaman rayuwar 'yan kabilar Hezhe cewa, an dinki riguna da fatun kifaye, kuma an zuba giya a kasaa don nuna girmama ga aljannu, 'yan kabilar Hezhe sun yi amfani da karnuka don jan keke a kan kankara. 'yan kabilar Hezhe sun yi wa fatun manyan kifaye dukanci , har ma sun yi taushi sosai tamkar yadda zawwati, sa'annan kuma sun yi amfani da su don dinki tufaffi. Yanzu, ba a iya samun wanda yake sanya rigunan fatun kifaye ba, an riga an tanada irin wadannan riguna a cikin gidan baje kolin kayayyakin tarihi,, amma ba su manta fasahar Yimakan ba, bayan aikin da suka yi a rana, sai suka taru a wani wuri daya suka rera wakar Yimakan suna jin nishadi sosai. Mr Wu Baochen ya bayyana cewa,

A lokacin da nake karami, bayan dawowar jiragen ruwa masu kamun kifaye, sai yara suka taru a inda jiragen ruwa ke zamewa, suke rera waka a wurin, in ranar bikin kabilar Hezhe ta zo, sai wasu suke raye-raye, wasunsu suke rera wakoki, wasu ma su ke ba da labarai, wasu kuma suke kada kayayyakin kida da aka yi da tsirkiyoyi.

A lokacin ba da dadewa ba, ma'aikatar al'adu ta kasar Sin ta tabbatar da cewa, Mr Wu Baochen shi ne mai gadon fasahar Yimakan bisa matsayin kasa. A ganinsa, fasahar Yimakan ita ce fasaha mai daraja sosai da ke iya wakiltar tarihi da al'adu da al'adar zaman rayuwa da bikin nuna da'a da sauransu na kabilar Hezhe, ya kamata a yada ta daga zuri'a zuwa zuri'a, ya bayyana cewa,

Yanzu, ana iya bayyana cewa, fasahar Yimakan ita ce abu mafi daraja ga 'yan kabilar Hezhe, ya kamata mu yada ta daga zuri'a zuwa zuri'a.

Wu Baochen shi kansa ya yi iyakacin kokari wajen gadon fasahar Yimakan da yadada ta ba tare da kasala ba. Amma dayake hanyar zaman rayuwa na kabilar Hezhe ya sami sauyawa, shi ya sa fasahar yana fuskantar ricikin mutuwa. Yanzu wadanda suka iya rera wakokin yawansu ya kai biyar kawai. Malam Wu Baochen ya bayyana cewa,

Kodayake ina da himma sosai wajen yada fasahar, amma matsalolin da na samu na da yawan gaske, halin da ake ciki kuma ake nuna yabo gare shi ta hanyar fasahar Yimakan ya sami sauyawa, sa'anan kuma kabilar Hezhe ba ta da rubuce-rubuce, shi ya sa yaduwarta na da wuya sosai, saboda haka cetonta da kare ta ayyuka ne da ake yi cikin gaggawa , Mr Wu Baochen ya ci gaba da bayyana cewa,,

Shekaruna da haihuwa sun riga sun kai 50, wajen al'adun kabilar Hezhe, in ban je koyon al'adun kabilar Hezhe ba, to ban iya fahimtar fasahar ba, balle a ce yaranmu, su ba su fahimci kome da kome dangane da fasahar Yimakan ba.

Gwamnatinmu a kai a kai ne ta gane abin da ke kasancewa yanzu, bayan da aka mayar da fasahar Yimakan bisa matsayin kayayyakin tarihi na al'adu ba kayayyaki ba a kasar Sin, sai hukumar da abin ya shafa ta tsara matakai da hanyoyin da za a bi don yada fasahar.

Amma, mataimakin shugaban birnin Tongjiang mr You Lijun ya bayyana cewa, wajen kabilar da ke da mutane kadan, kwararru da masana sun riga sun shiga ayyukan ceton fasahar Yimakan da kare ta , amma wannan bai isa ba, ya kamata za a yada ta a tsakanin jama'a. Mr Yu Lijun ya bayyana cewa,

Abu mai muhimmanci shi ne yin gado da yadada al'adun kabilar. Ana yada al'adun kabilar a inda 'yan kabilar suke zaman rayuwa, ta hakan, za a iya yada da gadon fasahar a tsakanin jama'a.

Saboda haka gwamnatin wurin ta tsara shiri da kuma shirya ayyukan al'adun da ke da halayen musamman na kabilar, dadin dadawa kuma ta ware kudaden musamman ga wadanda suka yi gadon fasaha don yada fashar ta hanyarsu ta kansu.(Halima)