Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-04 16:31:55    
Labaru masu ban sha'awa na kasar Sin

cri
Wani saurayi ya yi iyakacin kokarinsa wajen samo kyakkyawar mata. Bisa labarin da aka bayar a shafin yanar internet a makon da ya gabata, an ce wani saurayi yana so ya hadu da wata yarinyar da take so, yana so ya ba ta mamaki,sai a wata rana ya tafi tashar jirgin kasa dake karkashin kasa,yana jiran wata yarinyar da ya ke so, ya shirya mata wani kunshin dake da tufaffi masu inganci a ciki,bisa kunshin kuwa da awaki hoton yarinyar da ya dauka da wayar salularsa a bayanta, ban da wannan kuma, ya sanya sunansa da kuma lambar wayarsa a jikin kunshi. Wannan saurayi mai suna Chen ya zo ne daga lardin Jiangsu, ya ga yarinyar da ya ke so ne a tashar jirgin domin yarinyar tana da dogon gashi bakin da ya dauke hankalinsa, yana tsammanin idan yana jira zai iya same ta. Duk da haka ta sami yarinyar daga baya,amma yarinyar ta ki karbar kunshinta, ta tafi abinta. Ba ta sake zuba idonta kan saurayi ba.

Wata mata mai daura aure ta gaza. Bisa labarin da aka buga a cikin jaridar Modern Express ta birnin Nanjing na lardin Jiangsu, an ce da akwai wata mata mai daura aure da take da kwarin gwiwa wajen daura aure. Ita ma wata dirakta ce ta kwamin kula da unguwa a birnin Nanjing duk da haka tana da sha'awa sosai wajen taimakawa samari samu aure. Sunan matar Fu tana da shekaru 49 da haihuwa,ta daura aure tsakanin diyar abokin aikinta da wani ma'aikacin kamfnain hanyar dogo shekaru 28 da suka shige. Daga baya ta nuna sha'awarta wajen daura aure domin samari sama da 20 a cikin shekaru 18 da suka gabata, amma ta gaza samun nasara. Ta ce " ban sani ba ina soyayya take, mutanen yau sun rikide. Ba aiki mai sauki ba ne daura aure." Matar Fu ta kuma ci gaba da cewa samarin yau suna so su sake masoyinsu yadda za su sami wasu da suka fi dacewa da su, sun sha banban da mutane na zamani wadanda suka samu aure ta hannun mai daure aure." Duk da haka matar Fu ta kaunaci aikinta na daura aure kome hassara da ta sha.

Wani saurayi ya yi bara a titi. Bisa labarin da aka buga a jaridar Qingdao Morning News ta lardin Shandong a makon da ya gabata, an ce an gano wani sauraryin da ya sa farin kaya kuma dauke da jakar fatu yana bara a titin wani birnin Taidong na lardin Fujian a makon da ya gabata. Saurayin nan yana da suna Huang. Duk lokacin da ya wuce wani mutum a kan titi,sai ya daga hannunsa ya jinjina ga wanda ya gan shi, ya kuma roki matafiya da ya ba shi tsaraba. Wani sa'I mutane masu kirki sun tambaye shi me ya sa ya yi bara a kan titi, ya ki ya ce uffan. Daga baya wannan saurayi ya gaya wa dan jarida cewa shi dan wasa ne ya yi wasa ne a kan titin. Wannan saurayi da abokansa guda uku su kan yi haka dalili kuwa shi ne ba su gamsu da halin da ake ciki a yanzu ba,suna so su ga bakon abu. Da ya ke mutane da dama sun yi hakuri da wasan da samarin suka yi a kan titin,amma ba su dauki abin da suka yi a matsayin wasa ba.