Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-03 16:18:29    
Gasar cin kofin Masters ta kwallon tennis ta Shanghai ta yi ban kwana da kowa bayan shekaru 5

cri
A dare na ran 16 ga watan Nuwamba na shekarar da muke ciki, aka rufe gasar cin kofin Masters ta kwallon tennis ta karo na karshe a karkashin rufi mai siffar furen farin Magnolia na cibiyar wasan kwallon tennis ta Qizhong da ke birnin Shanghai tare da wata waka mai suna 'Zhufu' wato 'nuna fatan alheri' da Jackie Chang, wani mawaki na Hong Kong ya rera. Gasar cin kofin Masters ta yi ban kwana da birnin Shanghai, sa'an nan kuma, kasashen duniya sun yi ban kwana da gasar cin kofin Masters ta kwallon tennis. An sauya sunan gasar da za a yi a birnin London na kasar Birtaniya a shekara mai zuwa zuwa 'zagaye na karshe na gasar kwallon tennis ta hadaddiyar kungiyar wasan kwallon tennis ta maza ta duniya wato ATP'. An sa aya ga tarihin gasar cin kofin Masters ta kwallon tennis a birnin Shanghai. Game da wannan gasa, masu sha'awar wasan kwallon tennis sun tuna da abubuwa da yawa a zukatansu, har ma ba za su manta da su ba har abada. Mai yiwuwa ne za a tuna da abubuwa mafiya ban sha'awa da suka fi burge mutane, a maimakon takara mai zafi a tsakanin 'yan wasa.

Wasu za su tuna da wani karamin kayan wasa na bear, wanda ya sanya tufafin wasanni masu launin shudi tare da sanya wani farin madauri a ka, ya rike da raket a hannu, a bayan tufafin wasansa an rubuta lamba '1'. Wannan karamin kayan wasa na bear yana da kamannin mutum mai saukin kai da kuma mai gaskiya, ana kiransa 'Feder-bear'. 'Feder-bear' shi ne asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF da kungiyar ATP suka gabatar da shi cikin hadin gwiwa domin jin dadin jama'a. An fito da shi ne bisa surar dan wasa Roger Federer na kasar Switzerland, an kuma nada sunan wannan kayan wasa bisa sunan Federer. A wancan lokaci, Roger Federer ya zama na farko a duk duniya. Ana sayar da ko wane 'Feder-bear' da dalar Amurka 8. Ana yin amfani da kudaden da ake samu daga wajen sayar da 'Feder-bear' domin taimakawa yaran da ke fama da talauci a duk duniya. A cikin gasar cin kofin Masters ta kwallon tennis ta Shanghai da aka yi a shekara ta 2005, an fara sayar da wannan kyakkyawan kayan wasa a hukunce, har zuwa yanzu mutane na Allah-Allah domin sayen wannan karamin kayan wasa na bear.

Dimbin mutane sun tuna da wannan kayan wasa na bear a zukatansu ne domin Roger Federer a zahiri. Mutane suna son wannan dan wasa ne a sakamakon nagartacciyar fasaharsa ta wasa da kwallon tennis da kuma bullowarsa sau 5 a cikin gasar cin kofin Masters ta Shanghai, inda ya zama zakara sau 2, haka kuma, yana dukufa wajen saudakar da kansa domin taimakon jama'a. A matsayinsa na jakadan kawo fatan alheri da asusun UNICEF ya nada, Mr. Federer ya bayyana cewa,"Har kullum ina sha'awar gudanar da ayyukan jin dadin jama'a. Na sami irin wannan dama da yawa. Haka kuma na kafa asusu da kaina. Zan ci gaba da ayyukan da na yi a da."

Amma duk da haka, a lokacin da ake gudanar da gasar cin kofin Masters ta karo na karshe a Shanghai, a shagunan sayar da abubuwan tunawa, babu wannan kayan wasa na 'Feder-bear', kamar yadda muka gani a karon karshe na gasar, wato a shekaru 4 da suka wuce, a karo na farko ne Roger Federer bai bullo ba a cikin karon karshe na wannan gasa.

Watakila wasu kuma sun tuna da abubuwan bakin ciki a zukatansu. Yanzu da zarar tabo magana kan janye jiki daga gasa, sai hankalin Brad Drewett, babban darektan kungiyar ATP mai kula da harkokin duniya, kuma babban darektan kula da gasar cin kofin Masters ya tashi. A shekara ta 2005, 'yan wasa 5 masu karfi sun janye jikinsu daga gasar cin kofin Masters a sakamakon rauninsu, ciki har da Andre Agassi da Rafael Nadal da Marat Safin da suka fi samun karbuwa a tsakanin Sinawa. Wannan batu ya sanya masu kishin wasan kwallon tennis na kasar Sin da kuma masu ba da kudi domin gasar nuna rashin gamsuwa kwarai da gaske. Mr. Drewett ya sifanta batun cewar,"Wannan shi ne hadari mafi tsanani! Ba na so in sake fuskantar irin wannan hadari a sauran raina."

Ko da yake haka ne, lamarin ya zama tarihi. A sakamakon kokarin da bangarori daban daban suka yi cikin himma da kwazo, an sami cikakkiyar nasarar shirya gasar cin kofin Masters a shekaru 3 a jere bayan shekara ta 2005. Ko da yake wasu 'yan wasa sun janye jikinsu saboda rauni, amma masu kishin wasan kwallon tennis na kasar Sin sun kyautata ra'ayoyinsu, sun mai da hankulansu kan gasar ba domin 'yan wasa taurari kawai ba.

A zahiri, masu kishin wasan kwallon tennis ta kasar Sin sun shaku a cikin zukatan 'yan wasan kwallon tennis mafiya nagarta a duniya. 'Yan wasa da yawa sun taba bayyana cewa, a duk fadin duniya, sai kasar Sin daya tilo ne da suka sami irin wannan karbuwa. Roger Federer ya fi samun goyon baya a Shanghai. A lokacin da wannan dan wasa da ke fama da rauni tare da yin gwagwarmaya mai zafi tare da Andy Murray a cikin karon karshe na gasa ta kungiya-kungiya a wannan shekara, ya saurari irin wannan amo daga 'yan kallo a duk filin wasa. "Roger! Roger!"

Dukkan 'yan kallon fiye da dubu 15 a filin wasan sun kira sunan Federer da murya daya domin karfafa gwiwarsa. A wancan dare, sau da yawa 'yan kallo sun yi haka. Bayan gasar, Federer da ya sha kaye ya nuna wa masu kishin wasan kwallon tennis na kasar Sin godiya da zuciya daya.

A zuciyar dan wasa Novak Djokovic na kasar Serbia, wato zakara ta karshe ta gasar cin kofin Masters, ya tuna da abubuwa masu kyau. Ya bayyana mana cewa, a ko wace rana da yake Shanghai, a kalla ya kan sami abubuwan kyauta 3. Wannan saurayi ya ce,"Ina fatan zan koma gida tare da wadannan abubuwan kyauta duka. Ina matukar gode wa masu kishin wasan kwallon tennis na kasar Sin bisa goyon bayan da suke nuna mini. A duk raina na wasan kwallon tennis, ban taba samun irin wannan karbuwa ba tukuna."

Gasar cin kofin Masters ta wasan kwallon tennis ta Shanghai da aka yi a shekaru 5 da suka wuce ta shaku a cikin zukatan 'yan wasa da masu kishin wasan kwallon tennis, sa'an nan kuma, ta nuna wa rukunin wasan kwallon tennis duka alamar al'adun kasar Sin. A bayyane ne mutane suka tuna da cewa, a gun bikin bude gasar cin kofin Masters ta Shanghai ta karo na farko a shekara ta 2002, 'yan wasa gwanaye sun sanya tufafi masu halin musamman na kasar Sin. Tufafi irin na kasar Sin da ke jikin 'yan wasan sun nuna kyan ganin kasar Sin sosai. Bugu da kari kuma, mutum-mutumin tabo irin na Wuxi da aka yi bisa siffofin 'yan wasa suna da kyan gani sosai. Dadin dadawa kuma, mutum-mutumin soja da dawaki da aka kera a zamanin daular Qin na kasar Sin wato yau shekaru fiye da dubu 2 da suka wuce ya shahara sosai a duk duniya. Shi ya sa a cikin lokacin gasar cin kofin Masters ta Shanghai da aka yi a shekara ta 2007, an kera mutum-mutumin soja bisa surorin 'yan wasa mahalarta gasar, har ma an ajiye wadannan mutum-mutumi a cikin dakin nune-nunen kayayyakin tarihi kan budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta Wimbledon har abada.

Abubuwan da muka ambata a baya su ne alamu kawai. Wani batu ya cancanci kowa da kowa ya waiwaya. A farkon lokacin da ake shirya gasar cin kofin Masters ta wasan kwallon tennis a Shanghai, alkalan wasanni ba su iya tuntubar 'yan kallo yadda ya kamata ba, saboda ba su iya Sinanci ko kadan ba. Bayan shekaru 2,'yan kallo Sinawa sun san wasu kalmomin Sinanci marasa daidaici daga bakin alkalan wasannin. Amma a cikin gasar cin kofin Masters ta karo na karshe, a gasanni da dama, wadannan alkalan wasanni sun sami amincewa sosai daga 'yan kallon da ke filin wasa, sun yi musu ban tafi, saboda alkalan wasannin sun iya tuntubar 'yan kallo Sinawa yadda ya kamata bisa Sinanci mai kyau. Wannan shi ne nasarar da alkalan wasan kwallon tennis na duniya suka samu, haka kuma, nasarar da gasar cin kofin Masters ta samu, bugu da kari kuma, wannan shi ne nasarar da kasar Sin ta samu a fannin al'adu.(Tasallah)