Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-03 15:47:47    
Alayyaho ya iya kara karfin kwanjin jiki

cri
Bisa labarin da tashar Internet ta Jaridar Telegraph ta kasar Birtaniya ta bayar a kwanan nan, an ce, ta yin gwaji, masu ilmin kimiyya sun shaida cewa, sinadarin da ke cikin alayyaho ya iya kara karfin kwanjin jiki, da kuma kara saurin canja abubuwan gina jiki wato sinadarin protein zuwa kwanjin jikin dan Adam. Kuma masu ilmin kimiyya sun kiyasta cewa, idan ana son kara girman kwanjin jiki, to ya kamata a ci alayyaho a kalla kilogram daya a ko wace rana.

Elijah Ruskin da dai sauran manazarta na jami'ar Rutgers ta kasar Amurka sun ja wani sinadarin musamman daga alayyaho, da kuma yin gwaji kan amfaninsa. Daga baya kuma sun gano cewa, bayan da aka kara irin wannan sinadari, saurin girman samfur kwanjin jikin dan Adam ya karu da kashi 20 cikin dari.

Ban da wannan kuma mujallar 'sabbin masu ilmin kimiyya' ta kasar Birtaniya ta ba da rahoton nazari, cewar berayen da aka ja irin wannan sinadari cikin jikinsu har tsawon wata guda sun fi karfi.

Kafin wannan, wani nazari ya bayyana cewa, alayyaho da ke kunshe da Vitamin C da A da kuma K tana iya ba da taimako wajen rage saurin kashewar kitse, ta haka ba za a ji yunwa ba cikin dogon lokaci, da kuma rage nauyin jikinsa. Bugu da kari kuma wani nazari daban ya bayyana cewa, alayyaho zai iya ba da taimako wajen wartsakar da mutane.

To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu ci gaba da yin muku bayani kan kwanjin jiki..

Wani rahoton nazari da Amurka ta bayar a kwanan nan ya nuna cewa, shan kofi yana iya ba da taimako wajen sassauta zafin kwanjin jiki sakamakon motsa jiki fiye da kima.

Manazarta na jami'ar Georgia ta kasar Amurka sun ba da rahoto a kan mujallar zafin jiki, cewar bayan da suka gudanar da bincike ga dalibai mata 9 da ba safai su kan sha kofi da kuma motsa jiki ba, sun gano cewa, muddin aka samu sinadarin Caffeine kalilan da yawansa ya yi daidai da wadanda suke ciki kwaf biyu na kofi, to zafin kwanjin jiki da suke ji zai ragu da kashi 48 cikin dari.

Kuma rahoton ya bayyana cewa, dukkan wadannan dalibai mata sun ji zafin kwanjin jikinsu bayan kwanaki biyu da suka motsa jiki. Kuma a daidai wannan lokaci, manazarta sun sa wasu daga cikinsu su sha abin sha da yake kunshe da sinadarin caffeine yayin da sauransu suka sha abin sha da ba ya kunshe da sinadarin ba, daga baya kuma sun ci gaba da motsa kafafunsu. A karshe dai, an gano cewa, zafin kwanji da mata da suka sha abin sha da yake kunshe da sinadarin caffeine suka ji ya ragu da kashi 48 cikin dari in an kwantanta su da sauran mata yayin da wannan jimla ta kai kashi 26 cikin dari a cikin gwajin motsa kafafunsu.

Manazarta sun nuna cewa, ko da yake sinadarin caffein yana iya sassauta zafin kwanjin jiki sakamakon motsa jiki, amma kullum ya kan ba da amfani ga mutanen da ba safai su kan sha kofi ba. Shi ya sa wannan dabara ba za ta iya taimakawa wadanda su kan sha kofi ba.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Muna fatan kun ji dadinsa, da haka Kande ta shirya muku wannan shiri kuma ke cewa mako gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Kande Gao)