Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-02 22:17:54    
Kasuwar Hongqiao na da muhimmanci sosai kamar yadda Babbar Ganuwa take a cikin zukatan baki mata

cri

A cikin shahararrun kasuwanni da ke nan Beijing, akwai wata kasuwar da ta dogara da sayar da kayan ado na lu'ulu'un Pearl, inda a ko ina ake iya ganin baki masu saye-saye, haka kuma, mutane suna yin ciniki cikin Turanci, ban da wannan kuma manyan jami'an kasashen waje da kuma jakadun kasashen waje a kasar Sin da yawa su ma su kan zagaya nan a lokacin hutu. Wannan kasuwa ita ce kasuwar Hongqiao, tana daya daga cikin kasuwannin cinikin kayan ado na lu'ulu'un Pearl mafiya girma a kasar Sin.

Kasuwar Hongqiao da ta kafu a shekara ta 1995 tana da benaye 3 a karkashin kasa da kuma wasu 5 a kan kasa. A cikin dukkan shaguna fiye da dubu 1 da dari 1 a kasuwar, yawancinsu suna sayar da lu'ulu'u. Wasu shaguna ba su da girma, suna sayar da lu'ulu'u masu inganci kuma mai rahusa, wasu manyan shaguna 'yan sari kuwa suna sayar da lu'ulu'un da darajarsu ta kai dubunnan Yuan, har ma fiye da miliyan guda. Karin kamfanonin cinikin lu'ulu'u da suka kaddamar da cinikinsu a kasuwar Hongqiao sun yi shahara a duniya. Wang Lilong, darektan ofishin kula da kasuwar Hongqiao ta Beijing ya yi mana karin bayani cewa, "Yanzu kasuwar Hongqiao tana dogara da sayar da lu'ulu'u. Dalilin da ya sa hakan shi ne domin a tsakiyar shekaru 1980, kasuwar Hongqiao ta fara sayar da lu'ulu'u, yanzu ta yi shekaru fiye da 20 tana cinikin lu'ulu'u. A halin yanzu adadin lu'ulu'un Pearl da ake samu a kasar Sin a ko wace shekara ya kai misalin ton dubu 1 da dari 6. A matsayin kasuwa ta karshe bisa tsarin sayarwa, kasuwar Hongqiao ta kan sayar da lu'ulu'u fiye da ton dari 2 a ko wace shekara. Shi ya sa kasuwar Hongqiao take da matukar muhimmanci a tsakanin kasuwanni na karshe bisa tsarin kasar Sin na cinikin lu'ulu'u."

A kasuwar Hongqiao, babban ginin sayar da lu'ulu'u mai halin musamman na gargajiya da kuma muhallin da ke cikin babban zauren ginin, wato kasuwa na ci sosai suna dacewa da juna matuka. Kayayyakin ado da abubuwan fasaha iri daban daban da aka yi da lu'ulu'u a kan kantoci sun sanya masu saye-saye na gida da na waje su manta da komawa gida. A gaban kusan ko wace kanta, akwai baki matafiya da dama, masu sayarwa sun iya Turanci sosai, har ma sun iya yi wa masu saye-saye karin bayani kan abubuwan da suke sayarwa. Kasuwar Hongqiao kasuwa ce ainu ta duniya da ke sayar da abubuwan da ke shafar yawon shakatawa.

Kasuwar Hongqiao na da suna daban na Turanci, wato Pearl Market. An ce, in baki sun kai ziyara a Beijing, amma ba su je Pearl Market ba, to, za su yi matukar da na sani. Mr. Wang ya kara da cewa,"Yanzu baki da yawa sun zo kasuwarmu ta Hongqiao domin kai ziyara da kuma sayen lu'ulu'u. A ko wace shekara, mu kan karbi baki dubu 500 zuwa dubu 600, a ciki har da shugabannin kasashe da matayensu. A zukatan mutanen kasashen waje, kasuwar Hongqiao ita ce babbar ganuwa wato Great Wall a ganin matan da suka zo daga kasashen waje. In ba su zo kasuwarmu ba, to, za su yi da na sani sosai."

A babban zauren kasuwar Hongqiao, wasu mutane sun sayi lu'ulu'u su kadai, wasu kuma sun je tare da iyalansu. Kungiyoyin yawon shakatawa da suka zo daga kasashen waje da yawa su ma su kan mayar da kasuwar Hongqiao tamkar wurin da tilas ne a kai masa ziyara. Colin Lemont, ya yi shekaru da dama yana aiki a kasar Sin mahaifinsa dan kasar Amurka ne, yanzu yana yin aikin koyarwa a wata jami'a a birnin Yinchuan. Ya kan yi saye-saye a kasuwar Hongqiao. Yau ma ya raka abokansa da suka kawo wa kasar Sin ziyara a karo na farko, dan su yi saye-saye a kasuwar Hongqiao. Colin ya ce,"A ganina, wannan kasuwa na da kyau sosai, inda ake iya sayen lu'ulu'u da kayayyakin jade. Ina gamsuwa da abubuwan da na saya a nan. 'Yan kasuwan da ke aiki a kasuwar sun iya Turanci sosai. Ina koyar da Turanci a wata jami'a a arewa maso yammacin kasar Sin, ina mamaki sosai kan Turanci da 'yan kasuwa kan furta. Musamman ma, yawancinsu ba su koyi Turanci a hukunce a makaranta ba. Yau ma na zo nan domin sayen abun kyauta ga abokaina. A da, na taba sayen abun kyauta ga iyalina. A ko wane karon da abokaina da iyalina suka zo Beijing, na kan raka su da su yi saye-saye a wannan kasuwa."

Baya ga abubuwan ado na lu'ulu'u, ana sayar da kayayyakin lantarki da siliki da jakunkuna a kasuwar Hongqiao, wadannan abubuwa su ma sun sami karbuwa sosai a tsakanin baki masu saye-saye. Madam Rudi ta zo kasuwar Hongqiao a karo na farko. Ko da yake tayi a tsakaninta da 'yan kasuwa ya kan ba ta wahala kadan, amma ta gamsu da abubuwan da ta saya a nan. Ta ce,"Na dauki renon wata yarinya Basiniya. Na san kasuwar Hongqiao daga wajenta. Ta raka ni da na yi kasuwanci a nan. Wannan kasuwa na da kyau, kuma abubuwan da ake sayarwa a nan na da rahusa, akwai abubuwa iri daban daban da ake sayarwa a nan. Tayin da 'yan kasuwa da masu saye-saye suka yi ya ba ni wahala sosai. Tilas ne ka yi ta tayi, ba za su yarda da farashin da ka bayar ba, sai dai ka yi shirin tashi. Amma na gamsu da abubuwan da na saya. Na kan ji gajiya sosai bayan da na koma otel. Bayan da na koma Amurka, zan tuna da wannan kasuwa. Ina son Beijing sosai."

Diyyar Rudi ta gaya mana cewa, a kasuwar Hongqiao, ana sayar da tufafi da takalman da suka dace da Turawa, shi ya sa kasuwar Hongqiao ta cancanci masu saye-saye da suka zo daga kasashen waje.

Ko da yake madam Rudi ba ta son tayi amma wasu masu saye-saye da suka zo daga kasashen waje suna son yin tayi a tsakaninsu da 'yan kasuwa. Yin tayi ya zama ruwan dare a kasashensu. Gao Ling, wata daliba da ta zo daga kasar Isra'ila, ta yi shekaru 5 tana karatu a Beijing, Gao Ling, sunanta ne a Sinance. Ta gaya mana cewa, "A karo na farko ne na zo kasuwar Hongqiao tare da abokaina. Dukkansu sun san Hongqiao, suna neman yin kasuwanci a nan. Sun gamsu da abubuwan da suka saya a nan. Suna son abubuwa masu halin musamman na kasar Sin. Kafin su zo kasar Sin, sun san kasuwar Hongqiao a kan Internet, shi ya sa suke fatan zuwa wannan kasuwa. Ga masu yawon shakatawa, kasuwar Hongqiao ta yi kyau a gare su saboda akwai abubuwan da suke so, kamar jakunkuna da tufafi."

A idon 'yan kasuwa da ke aiki a kasuwar Hongqiao a ko wace rana, yin tayi ya zama ruwan dare a gare su. Don yin wa matafiya baki karin bayani yadda ya kamata, 'yan kasuwa su kan tuntube su cikin Turanci. Xiao Luo, wata 'yar kasuwa ta yi shekaru 5 tana aiki a kasuwar Hongqiao. Saboda ta iya Turanci sosai, shi ya sa baki da yawa su kan kewaya shagunta. A lokacin da muke yaba wa Turancin da ta yi, Xiao Luo ta yi tawali'u sosai, ta ce, "A'a, ban iya Turanci sosai ba. Mun koyi Turanci a kasuwar Hongqiao. A wasu lokuta, mutanen kasashen waje sun koya mana wasu. Ban iya Turanci sosai ba, a wasu lokuta, sun san abubuwan da na fada, wasu lokuta kuma, na san abubuwan da suka fada. Abun da ya shaku cikin zuciyata shi ne a wasu lokuta, mutanen kasashen waje su kan gaya mana abubuwa masu ban sha'awa kan kasashensu."

Kamar yadda Xiao Luo take yi, yawancin 'yan kasuwa a kasuwar Hongqiao sun iya Turanci, wasu kuma sun iya Rashanci da Japananci da harsunan Korea da Spain. Su kan ba matafiya baki mamaki sosai.

Tun daga ran 28 ga watan Yuni zuwa karshen watan jiya na wannan shekara, an yi bikin al'adar lu'ulu'un Pearl na duniya a karo na 2 a kasuwar Hongqiao. Babban taken bikin shi ne al'adar lu'ulu'un Pearl da al'adar mutum da kuma gasar wasannin Olympic ta Beijing. A gun wannan biki, wata muhimmiyar harka ita ce shirya nune-nunen lu'ulu'un Pearl. Darektan Wang ya yi karin bayani cewa, "Lu'ulu'un Pearl da muka nuna a wannan gami sun hada da iri daban daban, suna da inganci sosai. A lokacin gasar wasannin Olympic ta Beijing, baki masu yawa sun yi kasuwanci da kuma yin ziyara a kasuwar Hongqiao, sa'an nan kuma, an mayar da kasuwar Hongqiao a matsayin daya daga cikin muhimman hukumomin da suka karbi baki da kuma titunan kasuwanci guda 9 a Beijing. Mun yi amfani da damar shirya gasar wasannin Olympic wajen shirya bikin lu'ulu'un Pearl a wannan karo, ta haka mutanen da suka zo daga wurare daban daban na duniya sun san Beijing, da kasuwar Hongqiao da kuma lu'ulu'un Pearl da kasar Sin take samarwa."