Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-02 16:29:58    
Afirka ta sami sakamako mai kyau wajen yaki da cutar kanjamao tare da tinkarar kalubale

cri

Ran 1 ga watan Disamba na shekarar bana, rana ce ta yaki da cutar kanjamao ta duniya a karo na 21. Bisa sabon adadi da hukumar tsara shiri kan yaki da cutar kanjamao ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayar, an ce, ya zuwa karshen shekarar 2007, a yankunan da ke kudu da hamadar Sahara a Afirka, mutane kimanin miliyan 22 sun kamu da cutar kanjamao, wadanda yawansu ya kai kashi 67 cikin dari bisa na duk duniya. Ya zuwa yanzu Afirka ita ce yankin da aka fi samun masu kamuwa da cutar kanjamao a duk duniya. Ko da yake wannan yanki ya sami sakamako mai kyau wajen yaki da wannan mummunar cuta, amma cutar tana ci gaba da addabrsa sosai.

Kyawawan fasahohi da kasashe da yawa suka samu sun nuna cewa, yin rigakafin cutar kanjamao na iya saukaka yaduwar kwayoyin cutar yadda ya kamata. Alal misali, kasar Saliyo ta dade tana daukar matakan yin rigakafin wannan cuta, ta haka yawan mutane baligai da suka kamu da cutar kanjamao ya yi kasa da guda wato kashi 0.9 cikin dari kawai.

Sa'an nan kuma, yin binciken cutar kanjamao tare da samun amincewa yana matsayin daya daga cikin muhimman bangarori na shirin yin rigakafin cutar kanjamao. A sakamakon yada hanyar binciken kwayoyin cutar kanjamao cikin gajeren lokaci, yanzu binciken cutar kanjamao tare da samun amincewa ya riga ya zama hanya mafi dacewa, haka kuma, ya sami karbuwa sosai a yawancin kasashen da ke kudu da hamadar Sahara. Ban da wannan kuma, bayar da kwaroron robar hana daukar ciki ita ce hanya ta daban ba tare da biyan makudan kudade ba a fannin yin rigakafin cutar kanjamao. Yanzu wannan hanya tana bazuwa cikin sauri a Afirka.

Ba da magungunan hana sake bullowar kwayoyin cutar HIV yana iya kyautata halin da masu fama da cutar kanjamao suke kasancewa sosai. Kasar Botswana tana cikin sahun gaba a tsakanin kasashen duniya a wannan fanni. Bayan da ta kaddamar da shirin a shekarar 2002 har zuwa yanzu, gwamnatin Botswana ta ba da magunguna ga yawancin masu fama da cutar. Bisa adadin da Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya wato WHO ta bayar, an ce, a karshen shekarar 2007, mazauna Botswana kimanin dubu 93 suna samun irin wadannan magunguna, yawan wadanda suke samun irin wadannan magunguna ya kai kashi 80 cikin dari bisa jimlar masu fama da cutar.

Ko da yake wasu kasashen Afirka sun sami ci gaba sosai a fannin yaki da cutar kanjamao, amma ya zuwa yanzu talauci ya fi addabar kasashen Afirka da ke kudu da hamadar Sahara wajen yaki da cutar kanjamao. A sakamakon talauci, marasa abin hannu da ke zaune a birane da yankunan karkara sun gaza wajen samun ilmin yin rigakafin cutar kanjamao, haka kuma, matan da ke fama da yunwa suna yin zaman kansu domin samun na abinci, ko da yake suna sane de barazanar kamuwa da kwayoyin cutar kanjamao, sa'an nan kuma, dimbin masu fama da cutar kanjamao ana iya cewa, suna nan suna jiran mutuwa ne a sakamakon rashin kudin sayen magani, bugu da kari kuma, gwamnatoci sun gaza wajen bai wa masu fama da cutar shawara da kuma magani saboda karancin likitoci da kayayyakin aiki.

Rashin abinci mai gina jiki a sakamakon talauci ya kan tsananta lafiyar masu fama da cutar kanjamao. Yunwa tana tilasta wa wasu masu fama da cutar su yi musayar abinci da maganin da suka samu ba tare da biyan kudi ba daga hukumomin ba da agaji.

Dadin dadawa kuma, nuna bambanci da jin tsoro su ne suka hana Afirka ta yaki da cutar kanjamao. Alal misali, a kasar Zambia, a shekarar 2007, mutanen kasar da yawansu ya kai kashi 16 cikin dari bisa jimlar mutanen kasar sun kamu da kwayoyin cutar kanjamao, amma mutanen da yawansu ya kai kashi 13 cikin dari ne kawai suka so a yi musu bincike ta fuskar kamuwa da kwayoyin cutar kanjamao tare da samun amincewarsu. Mutane da yawa da ba su so a yi musu bincike suna ganin cewa, in sun sun san kamu da kwayoyin cutar, to, za su rasa burinsu na ci gaba da zaman rayuwa. Game da wannan, wasu kasashen Afirka suna bin wasu hanyoyi na tilastawa, kamar yin binciken kwayoyin cutar kanjamao a gidaje da kuma binciko masu dauke da cutar a maimakon jiransu kawai, a takaice dai, suna kokari kan yi wa karin mutanensu bincike a fannin kamuwa da kwayoyin cutar kanjamao.(Tasallah)