Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-12-01 15:53:58    
Labaru game da kananan kabilun kasar Sin

cri
---- Yayin da ake murnar ranar cikon shekaru 50 da kafuwar kwalejin kabilu ta jihar Tibet, Mr. Hu Jintao, babban sakataren kwamitin tsakiya na JKS, shugaban kasar Sin, kuma shugaban kwamitin soja na tsakiya ya rubuta wasika domin taya murna.

A ran 5 ga watan Oktoba, an yi murnar ranar cikon shekaru 50 da kafuwar kolejin kabilu ta jihar Tibet wadda aka kafa a birnin Xianyang na lardin Shanxi. Cikin wasikar da Mr. Hu Jintao ya rubuta ya ce, kwalejin kabilu ta jihar Tibet wata babbar kwaleji ce da gwamnatin tsakiya ta kafa a karo na farko a cikin kasar Sin bayan da aka 'yantar da jihar Tibet cikin lumana. Cikin shekaru 50 da suka wuce na bayan kafuwar kwalejin, kolejin tana tafiyar da ka'idojin ba da ilmi da manufofin kabilu na jam'iyya cikin nitsuwa, kuma ta tsaya kan manufar ba da ilmi da yin hidima ga jihar Tibet, tana tafiyar da manufar kwalejin ta kishin kasa da raya jihar Tibet da yin kokarin karatu da kuma dukufa kan aikin koyarwa, sabo da haka ta tallafawa tarin ma'aikatan hukuma 'yan kananan kabilu da kwararrun fasaha mai nagarta na sana'o'in musamman, kuma ta ba da babban taimako domin bunkasa tattalin arziki da samun ci gaban zamantakewar jihar Tibet.

Mr. Hu Jintao yana fatan ganin kwalejin kabilu ta jihar Tibet za ta tafiyar da tunanin babban taro na 17 na JKS daga duk fannoni, kuma ta yada al'ada mai kyau, ta yi babban taki haye bisa hanyar zamani, kuma ta yi kokarin binciken dokokin ba da ilmi ga 'yan kananan kabilu, kuma ta daga matsayin kula da harkokin koyarwa da na karatu, da kara yin amfani a fannin tallafawa ma'aikatan hukuma na jihar Tibet, ta yadda za ta kara ba da babban taimako domin ingiza ci gaban tattalin arziki da zaman al'umma na jihar, da kyautata zaman rayuwar jama'a 'yan kabilu daban-daban na jihar, da sa kaimi ga samun kwanciyar hankali da hadin kai a jihar.

---- Kwanan baya wakilinmu ya samu labari daga wajen taron tattauna batun rayawa da kuma yin amfani da makamashin da abubuwa masu rai suka samar a jihar Tibet, an ce, jimlar albarkatun kasa da abubuwa masu rai na jihar Tibet suka samar ta kai nauyin kusan ton biliyan 1.3, ana iya kyautata zaton cewa za a samu makoma mai kyau wajen raya wadannan albarkatun kasa da yin amfani da su.

Kwararru sun bayyana cewa, kashi 80 cikin 100 na dukkan makamashin da aka yi amfani da shi a kowace shekara a jihar Tibet suna samuwa ne daga kashin shanu da kasar da ke dauke da ciyayi da kirare da sauran makamashi daban-daban da abubuwa masu rai suka samar. Sabo da ana dogaro bisa wadannan makamashi sosai, shi ya sa ake sare itatuwa da tsirrai da yawa, kuma ake haddasa illa ga filaye masu ciyayi sosai.