Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-28 16:51:29    
Jihar Tibet da kabilar Tibet na kasar Sin

cri

A wannan mako, za mu amsa tambayar malama Fatima Musa Abbas, Wadda ba ta bayyana mana wurin da ta fito ba. A cikin sakon Email da ta aiko mana, ta ce, "Don Allah menene ake nufi da Tibet? Shin sunan wani lardi ne a kasar Sin? Ko sunan wata kabila ce? Ina fatan za ku yi mani cikakken bayani."

To, madallah, malama Fatima, Tibet suna ne na wata jiha ta kasar Sin, sa'an nan, muna kuma kira wata kabilar da ke zama a yankin 'yan kabilar Tibet. Da malama Fatima da dai sauran masu sauraronmu, yanzu sai ku gyara zama ku saurari wani bayani dangane da Tibet.

Masu sauraro, jihar Tibet tana kudu masu yammacin kasar Sin, kuma fadinta ya kai muraba'in kilomita sama da miliyan 1 da dubu 220, wanda ya dau kashi 12.8% na duk fadin kasar Sin. Kasancewarta a kan platon Qinghai-Tibet, ana kiranta "kololuwar duniya", sabo da matsakaicin tsayinta ya kai sama da mita 4500 daga leburin teku. Sabo da haka, ana samun rana sosai a Tibet, ga shi kuma akwai sanyi. Jihar Tibet tana da hedkwatarta a birnin Lhasa, wanda ke tsakiyar jihar.

Tibet tana da wadata a fannin bishiyoyi da dazuzzuka, kuma fadin dazuzzukan da take da su ya kai kadada miliyan 7 da dubu 170, wanda ya zo na farko a kasar Sin. Bayan haka, Tibet tana kuma daya daga cikin manyan makiyaya biyar na kasar Sin sakamakon arzikin filayen ciyayi da take da su.

Bayan haka, Tibet tana da arzikin ma'adinai iri iri, kuma yawan ma'adinai da aka riga aka gano a jihar ya kai sama da 100. Sa'an nan, Tibet tana wadata da albarkatun ruwa da makamashin rana. A Tibet, akwai kuma dabbobi da tsire-tsire iri iri masu daraja, daga cikinsu, akwai dabbobi iri iri 125 da suke samun kariya sosai daga gwamnati, tare kuma da 45 masu daraja da ake samunsu kawai a kasar Sin.

Tibet ta kuma shahara a wajen yawon shakatawa. A Tibet, akwai tsaunuka 59 da tsayinsu ya wuce mita 7000 tare kuma da tsaunuka 7 da tsayinsu ya wuce mita 8000. Ban da wannan, kwarin kogin Brahmaputra ya kasance kwari mafi girma a duniya. A birnin Lhasa, hedkwatar jihar Tibet, akwai wata fada da ta fi tsayi daga leburin teku a duniya, wadda ake kiransa fadar Potala. Fadar ta yi suna sosai da zane-zanenta da kuma sassaka da kayayyaki na tarihi da ke cikinta. Tare kuma da al'adun musamman na al'ummar Tibet, Tibet na jawo masu yawon shakatawa daga wurare daban daban na duniya.(Lubabatu)

Ban da wannan, Tibet shi kuma suna ne na wata kabila. Akasarin 'yan kabilar suna zaune ne a jihar Tibet, tare kuma da wasu wurare a lardunan Qinghai da Gansu da Sichuan da kuma Yunnan na kasar Sin, kuma yawan 'yan kabilar Tibet ya kai miliyan 4 da dubu 590.

'Yan kabilar Tibet sun samo asalinsu ne daga wata tsohuwar kabila manoma da ke zaune a gabobin kogin Brahmaputra. 'Yan kabilar Tibet suna da harshensu da kuma rubutunsu, kuma suna da al'adu masu albarka. Labarin sarki Gesar nasu ya kasance tsarin waka mafi tsayi a duniya. Ban da wannan, 'yan kabilar Tibet suna kuma kwarewa a wajen wasan kwaikwayo da wakoki da raye-raye da kuma sassaka. Maganin 'yan kabilar Tibet ma ya shahara sosai, wanda wani muhimmin kashi ne na maganin kasar Sin.