Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-27 17:09:01    
Manufa mai gatanci da gwamnatin jihar Ningxia ta dauka a fannin ba da ilmi ga kananan kabilu ta kyautata zaman rayuwar musulmi na kabilar Hui.

cri

A matsayinta na wata jihar musulmi ta kasar Sin, akwai 'yan kabilar Hui miliyan 2.17 a jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui, wato sun kai kashi 35.5 cikin dari bisa na dukkan mutanen jihar. Amma, saboda dalilin tarihi, 'yan kabilar Hui na jihar Ningxia sun fi taru a kauyuka, musamman ma a yankuna masu fama da talauci da ke kudancin jihar, inda aka samu bunkasuwar tattalin arziki a hankali a hankali, kuma yawan kudin da aka samu kadan ne.

A cikin wannan hali kuma, shugabannin jihar suna ganin cewa, idan ana son canja halin zaman rayuwar musulmin da yawansu ya wuce miliyan 2 a jihar, tilas ne a kara saurin bunkasuwar ba da ilmi ga kananan kabilu, da kuma kara kwarewarsu. Saboda haka ne, gwamnatin jihar Ningxia ta tsara da kuma dauki matakai masu gatanci a fannin ba da ilmi ga kananan kabilu.

Domin kara saurin ayyukan horar da kwararru na kananan kabilu, a lokacin da ake zaben dalibai na jami'ai da makarantun sakandare, jihar Ningxia ta dauki mataki na rage layin maki ga dalibai daga kananan kabilu. Kazalika kuma, ta kafa kwasa kwasai na share fage a jami'ai, don karbar dalibai na kananan kabilu musamman. Bugu da kari kuma, jihar ta dauki wasu matakai, don kara yawan dalibai na kananan kabilu da za a dauka.

He Jun, 'dan shekaru 26 na kabilar Hui yana aikin shugabanci a sashen albarkatun 'dan Adam na wani kamfanin kasashen waje da ke jihar Ningxia. He Jun ya gaya wa wakilinmu cewa, aikin ba da ilmi ya canja halin rayuwata, idan ban samu shiga jami'a ba, watakila yanzu ina aikin gona kamar kakanina."

Bisa sharadi mai gatanci na rage layin maki ga dalibai 'yan kananan kabilu ne, He Jun ya shiga jami'ar jihar Ningxia, don koyon fasahar gudanarwar ciniki, haka kuma an canja rayuwarsa. He Jun ya ce, "Ni mutum na farko ne na iyalina da na fita daga kauye."

A hakika dai, ba He Jun shi daya kawai da ya ci gajiya daga manufofi masu gatanci a fannin ba da ilmi ga kananan kabilu ba. A karkashin tasirin da al'adun gargajiya na kabilar Hui ke kawowa, 'yammata na kabilar kadan ne ke iya shiga makaranta, saboda haka, abin da ya fi mawuyaci wajen ayyukan ba da ilmi shi ne, aikin ba da ilmi ga 'yammata.

Domin kara yawan 'yammata da za su shiga makaranta, jihar Ningxia ta dauki matakai a jere, ciki har da kyautata muhallin zaman al'umma, da iyalai, da makarantu wajen ayyukan ba da ilmi ga 'yammata, da kafa kwasa-kwasai, da makarantun 'yammata, da horar da shugabanni, da malaman 'yammata na kabilar Hui, da kuma rage yawan kudin karatu na 'yammata, da dai sauransu.

Ma Mi, wata yarinya daga gundumar Xiji ta jihar Ningxia tana karatu a kos din kananan kabilu na makarantar sakandare ta 'yan kabilar Hui. Ta gayawa wakilinmu cewa, tana iya cigaba da karantunta saboda ban da kudin kwana ba za ta biya sauran kudade ba, bayan haka kuma, tana iya samun kudin alawas da ya kai RMB 30 a ko wane wata, ta yadda ba ta kara nauyin tattalin aiziki da ke bisa wuyan iyalinta ba.

Mr. Wang Ziyuan, wani jami'in hukumar ba da ilmi ta gundumar Xiji ya gabatar da cewa, tun daga shekaru 80 na karnin da ya wuce, gwamnatin gundumar, da ta jihar Ningxia sun soma bayar da kudin alawas na kananan kabilu ga makarantun firamare da na sakandare na 'yan kabilar Hui da ke gundumar, wadanda yawansu ya kai 16, sakamakon haka, aka sassauta nauyin da ke bisa wuyan dalibai 'yan kabilar Hui a fannin tattalin arziki.

A lokacin da ake neman kara yawan dalibai masu shiga karatu, a waje daya kuma, ba a manta da kyautata halin kafa makarantu, da kuma kara kwarewar malamai a fannin ayyukan ba da ilmi na kananan kabilu ba. Gwamnatin jihar Ningxia mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Hui ta taba gudanar da muhimman ayyukan ba da ilmi a jere, don kyautata halin makarantu.

Bayan haka kuma, jihar Ningxia ta dauki matakai, ciki har da kafa kwasa-kwasan horar da malamai mata 'yan kabilar Hui, da kuma bayar da taimakon kudi ga dalibai mata na kabilar Hui, wadanda ke karatu a jami'an horar da malamai, don kara horar da malamai na kabilar Hui, musamman ma na mata, ta yadda za a kara yawansu a cikin dukkan malamai a jihar.

A karshen ziyarar, He Jun, wanda ke aikin shugabanci a sashen albarkatun 'dan Adam na wani kamfanin kasashen waje da ke jihar Ningxia ya ce, "Kasar Sin na mayar da hankali, da kara nuna goyon baya, da kuma tsara manufofi don nuna gatanci ga ayyukan ba da ilmi ga kananan kabilu, sanadiyar haka, 'yan kabilar Hui sun canja ra'ayoyinsu a fannin ba da ilmi, kuma iyalan kabilar Hui da yawa suna kara kulawa da ayyukan ba da ilmi, gaskiya ne suna fatan canja halin zaman rayuwarsu ta hanyar samun ilmi."