Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-26 17:21:05    
Cin abinci mai bayar da karfi ga jiki kadan zai iya rage kiba da kuma yawan kitsen da ke taruwa a jijiya

cri
Bisa labarin da mujallar 'sabon ilmin likitanci na England' ta kasar Amurka ta bayar a ran 17 ga watan Agusta na shekarar da muke ciki, an ce, bayan da manazarta na kasar Isra'ila suka yi nazari, sun gano cewa, hanyar rage kiba ta Atkins da ta ba da shawara kan rage yawan abinci mai bayar da karfi ga jiki wato sinadarin carbohydrate da ake ci yayin da kara yawan abinci mai gina jiki wato sinadarin protein ta fi ba da amfani a fannin rage yawan kitsen da ke taruwa a jijiya, wanda ke hana jini gudu in an kwatanta da hanyoyin rage kiba na gargajiya, kuma hanyar Atkins ta samu kyakkyawan sakamako a fannin rage kiba.

An gudanar da wannan nazari ga mutane 322 har shekaru 2 a cikin wani dakin nazarin nukiliya ta kasar Isra'ila a gefe guda. Kuma mutanen da yawansu ya kai kimanin kashi 85 cikin kashi dari da suka shiga nazarin sun bi ka'idojin abinci, wato sun ci abincin rana a cikin dakin cin abinci da aka samar, da kuma cin abinci daban daban bisa kungiyoyinsu daban daban. Haka kuma sun zabi karin kumallo da abincin dare bisa shawarar manazarta, amma an bukace su wajen rubuta takardun tambayoyi bayan abincin.

Ta yin haka, manazarta sun iya kwantata hanyar rage kiba ta Atkins da ta gargajiya da kuma ta Bahar Rum da ta ba da shawara kan cin naman dabbobin gida da kifaye da man zaitun da kuma ire-iren 'ya'yan itatuwa, daga baya kuma an gano cewa, hanyar rage kiba ta Atkins ta fi ba da amfani wajen rage yawan kitsen da ke taruwa a jijiya.

Hanyar Atkins wata hanya ce da ta taba samun farin jini sosai a kasar Amurka wajen rage kiba, wani likita mai suna Atkins shi ne ya gabatar da ita, kuma muhimmiyar hanya da ake bi ita ce cin abinci masu gina jiki yayin da ake cin abinci masu ba da karfi ga jiki kadan. Game da mutanen da suka bi hanyar Atkins, matsakaicin yawan nauyin jikinsu ya ragu da kilogram 4.6, yayin da wannan jimla ta kai 4.5 ga wadanda suka bi hanyar Bahar Rum, kuma wannan jimla ta kai 2.9 ga wadanda suka rage nauyinsu ta hanyar gargajiya.

To, masu saurari, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu ci gaba da yin muku bayani kan rage kiba.

Manazarta na kasar Birtaniya sun gabatar da sabon ra'ayi kan rage kiba ta cin abinci ta gargajiya, wato sun nuna cewa, motsa jiki da cin abinci masu ba da karfi ga jiki wato sinadarin carbohydrate da ke kunshe da sukari da kuma kitse kadan za su ba da taimako wajen rage kiba.

Manazarta na jami'ar sarauniyar Margaret ta birnin Edinburgh ta kasar Birtaniya sun bayyana cewa, kullum masu neman rage kiba suna ganin cewa, bai kamata su ci abincin da ke kunshe da sukari ba, amma watakila yin haka ba ya iya cimma burinsu na rage kiba. A maimakon haka, cin sukari yadda ya kamata zai ba da taimako ga masu neman rage kiba wajen tsayawa tsayin daka kan shirinsu na rage kiba ta hanyar cin abinci.

A cikin gwajin da aka yi har makwanni 12, manazarta sun kasa mutane 69 da matsakaicin shekarunsu ya kai 41 da haihuwa cikin kungiyoyi uku domin su ci abinci da kuma motsa jiki bisa mataki daban daban.

Daga baya kuma manazarta sun gano cewa, bayan watanni uku, game da wadanda suka ci abincin da ke kunshe da sukari da kuma motsa jiki, sun fi samun lafiyar jiki, kuma yawan nauyin jikinsu ya ragu da kashi 4.7 cikin dari, kuma yawan kitse da ke cikin jininsu ya samu raguwa sosai.

To, jama'a masu sauraro, shirinmu na yau na ilmin zaman rayuwa ke nan. Muna fatan kun ji dadinsu, da haka Kande ta shirya muku wannan shiri kuma ke cewa mako gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Kande Gao)