Kamar yadda kuka sani, birnin Beijing shi ne babban birnin kasar Sin, kuma yana jawo hankulan kasashen duniya sosai bisa tsarinsa na musamman wajen al'adu. Saboda haka 'yan kasashen waje da yawan gaske sun zo birnin domin aiki da karatu da kuma zaman rayuwa. Wadannan 'yan kasashen waje suna jin dadi a Beijing kuma suna motsa jiki ta hanyoyi daban daban a kowace rana kamar yadda suka saba. Wasu kuwa sun fi sha'awar wasan kwallon gora a kan kankara, musamman ma ga wasu mutanen da suka zo daga kasashen Turai da Amurka. To, a cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku bayani kan wannan.
Yanzu, Beijing ya riga ya shiga lokacin sanyi, shi ya sa kusan kowace ranar Lahadi da dare, a kullum ana yin gasar wasan kwallon gora a kan kankara sau biyu a cibiyar wasan kankara dake titin Chaoyang na Beijing. Yawancin 'yan wasan da suke halartar gasar da aka shirya su ne mutanen da suka zo Beijing daga kasashen waje domin aiki da karatu, a sanadiyar haka, ana kiran gasar da suna 'hadaddiyar gasar wasan kwallon gora a kan kankara ta duniya ta Beijing'. Kodayake 'yan wasa sun yi matukar kokarin takara a gun gasa, amma makasudinsu na shiga gasa shi ne domin motsa jiki da kuma nishadi kawai, saboda gasa tsakaninsu ba gasar cin kofi ba ce, ita ma ba gasar sana'a ba ce.
Ray Plummer, injiniyan fasahar gina gini ne daga kasar Canada, ya riga ya yi aiki a Beijing da shekaru fiye da goma, shi ma daya daga cikin mutanen da suka shirya hadaddiyar gasar wasan kwallon gora a kan kankara ta duniya ta Beijing. Plummer ya gaya mana cewa, tun daga farkon shekarar 1990, 'yan kasashen waje mazauna Beijing sun riga sun fara yin wasan kwallon gora a kan kankara, amma a wancen lokaci, mutane ba su da yawa, sai sun kafa kungiyoyi biyu ne kawai. A shekarar 2003, 'yan kasashen waje mazauna Beijing wadanda ke sha'awar wasan kwallon gora a kan kankara sun kara karuwa. Ya zuwa shekarar 2004, a hukunce an kafa hadaddiyar gasar wasan kwallon gora a kan kankara ta duniya ta Beijing. Kawo yanzu, an riga an kafa kungiyoyi biyar, kuma 'yan wasa sun riga sun kai wajen dari daya. Plummer ya kara da cewa, "Yan wasanmu muna yin aiki daban daban a Beijing, alal misali, malamin makaranta da manajan kamfanin gina gini da injiniyan fasahar wayar salula da jami'in ofishin jakadanci da mai sana'ar dafa abinci da manajan otel da manajan kamfani mai zaman kansa da lauya da dalibi da sauransu. Ana iya cewa, mun zo ne daga kusan dukkan sana'o'in da 'yan kasashen waje ke yi a Beijing."
Kodayake 'yan wasa sun zo daga sana'o'i daban daban, amma sun zo gu daya bisa kishinsu na wasan kwallon gora a kan kankara. Saboda gasarsu ba za ta samu riba ba, shi ya sa dole ne kowanen 'dan wasa ya biya kudin da yawansa ya kai kudin Sin Yuan 2500 a kowace shekara domin biyan kudin haya wurin gasa da kayayyakin wasa da abin sha da sauransu. Don rage kudin kashewa, 'yan wasa wadanda ba su shiga gasa ba za su zama alkalan gasa da ma'aikatan shirya gasa, saboda haka 'yan wasa za su zama masu aikin sa kai na hadaddiyar gasar.
Lallai hadaddiyar gasar wasan kwallon gora a kan kankara ba gasar sana'a ba ce, amma tsarin gasarsu ya yi daidai da na gasar sana'a. Alal misali, su kan fara kowace shekarar gasa daga watan Satumba na wannan shekara, kuma za su kawo karshenta a watan Mayu na shekara mai zuwa, a cikin wannan shekarar gasa, kowace kungiya za ta shiga gasa sau 25, daga baya kuma za a zabi kungiyoyi biyu bisa makin da suka ci, su biyu za su kara yin gasa, a karshe dai zakara za ta fito. Ban da wannan kuma za a zabi daya daga cikinsu saboda ya zama gogagen 'dan wasa bisa sakamakon kididdigar da aka yi bayan gasa. Domin kara kyautata ingancin gasa, 'yan wasa su kan yi la'akari sosai kan karfin wasa na kowanen 'dan wasa yayin da suke kafa kungiyar wasa. Plummer ya ce, "Kafin a kafa wata kungiya, dole ne a yi wa 'yan wasa horo, wani lokaci su kan yi gasa tsakaninsu, wani lokaci kuwa su kan yi atisaye tare, za a raba fitattun 'yan wasa a cikin kungiyoyi daban daban, makasudinmu shi ne domin muna so mu kafa kungiyoyi biyar wadanda karfinsu ya yi daidai da juna. Wato kowace kungiya tana da fitaccen 'dan wasa kuma kowace kungiya tana da 'dan wasa wanda fasahar wasansa ba ta da kyau, da haka kuma za mu kara jin dadin takara a cikin gasar da muka shirya a kowace karshen mako."
Ban da wannan kuma, Plummer ya kan je sauran biranen kasar Sin domin yin gasar sada zumunta da kungiyar 'yan wasan kasashen waje ko kungiyar 'yan wasan sana'a tare da sauran 'yan wasa wadanda ke da lokacin hutu a kowane wata. Kawo yanzu, sun riga sun je birnin Harbin da na Qiqihaer da na Shanghai da na Dalian da na Kunming da sauransu. Kazalika, idan sun samu dama, wani lokaci kuma sun taba tafi sauran kasashe domin yin gasar sada zumunta, alal misali, a watan Oktoba na bana, sun je kasar Korea ta arewa da kasar Thailand bi da bi domin yin gasa a can.
Plummer ya ce, ba ma kawai hadaddiyar gasar wasan kwallon gora a kan kankara ta duniya ta Beijing ta kawo wa 'yan kasashen waje mazauna Beijing damar motsa jiki ba, har ma ta kawo musu damar jin dadin zaman rayuwa bayan aiki. Ban da wasan kwallon gora a kan kankara, Plummer da sauran 'yan wasa su kan yi taro inda su kan yi hira tamkar abokai domin yin musanyar ra'ayoyi kan fannoni daban daban, lallai su ne abokai, ana iya cewa, hadaddiyar gasar wasan kwallon gora a kan kankara ta duniya ta Beijing babban iyali ne gare su.
Olivier Rochefort shi ma ya zo daga kasar Canada, yanzu yana yin aiki a wani otel na Beijing, kuma ya zama manaja, ya ce, wani abokinsa ne ya gaya masa wannan labari wato an kafa wannan hadaddiyar gasar wasan kwallon gora a kan kankara a Beijing, da zarar ya ji labarin, sai ya shiga kowace gasar da aka shirya. Kuma yayin da Olivier yake yin gasa, kullum babansa Pierre Rochefort ya kalli gasar da ya yi, ko ana yin iska mai karfi ko ana yin ruwan sama, ba su taba daina ba. Dalilin da ya sa haka shi ne domin suna kishin wasan ainun.
Pierre ya gaya mana cewa, "Muna jin babban mamaki, kuma muna jin dadi kwarai. Kowace rana Olivier ya je aiki, kuma yana shan aiki, ban da wannan kuma, wurin wasan kwallon gora a kan kankara ya yi nisa da cibiyar birnin, dole ne mu kashe awa daya kan hanya, Olivier ya yi wasa a dakin wasan kwallon gora a kan kankara da awa daya kawai, daga baya kuma mu koma gida. Litinin da safe, Olivier zai je aiki kamar yadda ya saba, duk da haka, yana kishin wasa sosai." (Jamila Zhou)
|