Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-24 21:37:11    
Hu Jintao ya gana da shugaban Rasha Medvedev

cri

A ran 23 ga wata, Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya gana da Dmitry Medvedev, shugaban kasar Rasha a birnin Lima, babban birnin kasar Peru.

Hu Jintao ya bayyana cewa, muhimmin aikin da ke gabanmu a yanzu shi ne kasar Sin da ta Rasha su yi kokari tare don kawar tasirin da rikicin hada-hadar kudi na duniya ya kawo, kuma su sa kaimi ga gyare-gyaren tsarin hada-hadar kudi na duniya yayin da suke ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kasashen biyu. Kuma za su aiwatar da ka'idojin da aka tanada a yarjejeniyar hadin gwiwar sada zumunci a tsakanin Sin da Rasha. Za su kara yin shawarwari kan tsaro bisa manyan tsare-tsare, kuma su yi musanyar ra'ayoyinsu kan muhimman batutuwan duniya da na yankuna cikin lokaci. Za su ci gaba da nuna goyon baya ga juna wajen muhimman matsalolin da ke shafar moriyarsu. Za su hada bunkasuwar dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare a tsakanin kasashen biyu da ka'idar kasuwanci don inganta hadin gwiwa a duk fannoni.

Mr Medvedev ya ce, bangaren Rasha yana son yin hadin gwiwa da shawarwari tare da bangaren Sin wajen warware rikicin hada-hadar kudi na duniya, kuma za su tattauna kan nasarorin da aka samu daga taron koli a tsakanin shugabannin G-20 game da kasuwar hada-hadar kudi da tattalin arzikin duniya da kwarya-kwaryan taron shugabannin APEC.

A wannan rana, Hu Jintao ya gama ziyararsa a kasar Peru tare da nasara, kuma ya tashi daga birnin Lima na kasar Peru zuwa kasar Greece a ran 23 ga wata da yamma.(Zainab)