Gundumar Wenchuan ta lardin Sichuan na kasar Sin tana daya daga cikin yankunan da ke fama da girgizar kasa mai matukar tsanani wadda ta auku a ran 12 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki. A ran 1 ga wata da misalin karfe 8 da minti 40 na safe, 'yan makaranta fiye da 250 na kabilun Tibet da Qiang da suka zo daga gundumar Wenchuan sun shiga bikin kaddamar da karatu a cikin wata makarantar firamare ta birnin Yibin da ke da nisan fiye da kilomita 400 a tsakaninsa da Wenchuan. Liu Xiao mai shekaru 8 da haihuwa shi ne wanda ya fi kankanta a cikin wadannan 'yan makaranta fiye da 250. Kuma ya gaya wa wakilinmu cewa, yana sa ran alheri sosai wajen samun darasi na farko a cikin wannan sabuwar makaranta. Kuma ya ce, "Yau za a kaddamar da darasi na farko, ina farin ciki sosai. Kuma ina son gaya wa iyayena, cewa wurin na da kyau sosai, don Allah su kwanta da hankalinsu, kada su nuna mana danuwa. Zan yi kokari wajen karatu domin raya kyakkyawan garina na Wenchuan bayan da na yi girma."
Ana iya samun 'yan makaranta fiye da miliyan 3.4 a duk lardin Sichuan wadanda suka samu illa daga girgizar kasa kamar Liu Xiao, kuma dukkansu sun sake shiga makaranta a ran 1 ga wata.
A cikin wata makarantar firamare ta birnin Pengzhou da ke fama da bala'in mai tsanani, wakilinmu ya gano cewa, ko da yake ba a iya samun kyawawan sharuda a nan ba, amma makarantar ta haye wahaloli iri daban daban da kuma kaddamar da karatu bisa lokacin da aka tsara. Yi Kongdong, shugaban makarantar ya bayyana cewa, ba za a iya yin amfani da dakunan kwana na 'yan makaranta ba sai dai zuwa ran 10 ga wata, amma domin 'yan makarantar suka iya sake kaddamar da karatunsu tun da wuri, malamai sun samar da dakunansu bisa son rai. Kuma ya kara da cewa,"Domin ba da tabbaci ga 'yan makarantarmu wajen shiga makaranta a yau. da kuma tabbatar da lafiyarsu, mun dauki wani mataki, wato dukkan malamai sun samar da dakunansu na kwana domin 'yan makarantar ke iya zama a ciki. Malamai sun sha wahala, amma 'yan makaranta sun samu sauki, dalilin da ya sa muka yi haka shi ne sabo da muna son tabbatar da cewa, dukkan 'yan makarantarmu za su iya shiga makanrata wajen karatu, ba za mu manta da ko wanensu ba."
A hakika dai, kafin a kaddamar da karatu, hukumomin ilmi na lardin Sichuan sun aika da kungiyoyin aiki da yawa zuwa yankunan da ke fama da bala'in domin yin bincike kan dakunan kwana da na cin abinci na makarantu, ta yadda za a iya ba da tabbaci ga 'yan makaranta wajen samun wani muhallin karatu mai inganci. Madam Yang Li, shugaba ta wata kungiyar aiki ta bayyana cewa, sun riga sun gudanar da bincike sau da yawa ga makarantun birnin Pengzhou, sun gamsu da sakamakon binciken. Kuma ta kara da cewa, "Mun gudanar da wannan bincike daga dukkan fannoni domin ganin ko an riga an share fage sosai wajen kaddamar da karatu ko a'a. Ko da yake makarantun sun taba fama da bala'in mai tsanani, amma yanzu ana sake gina su, kuma muna iya gano cewa, yankunan karatu suna da tsabta, dakunan cin abinci kuma suna da inganci."
Bisa labarin da muka samu, an ce, a cikin sabon zangon karatu, hukumomin gwamnatin lardin Sichuan za su kara samar da taimako ga 'yan makaranta masu fama da talauci, kuma za a amince da marayu da yaran da suka nakasa sakamakon bala'in da su shiga makarantun da ke kusa da gidajensu, da kuma nuna musu kulawa sosai. (Kande Gao)
|