Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-11-25 19:49:19    
Bunkasuwar kasar Sin ta kawo wa kasashen duniya alheri

cri

Tun bayan shekarar 1978 da kasar Sin ta fara yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga waje, a cikin wadannan shekaru 30 da suka wuce, kasar Sin ta sami saurin ci gaban tattalin arziki da zaman al'ummar kasa da ke jawo hankulan mutane sosai. Kasashen duniya sun mayar da irin wannan bunkasuwa a matsayin abin al'ajabi irin na kasar Sin. An iya dauka cewa, wadannan kalmomi da kafofin yada labaru na yammacin duniya suka kirkire wato abin al'ajabi irin na kasar Sin na iya takaita nasarorin da kasar Sin ta samu bisa manufofin yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga waje. Bunkasuwar kasar Sin ba kawai ta warware mastalar abinci da tufafi da Sinawa mai yawan biliyan 1.3 suka fuskanta tare da kyautatuwar zaman rayuwar fararen hula na kasar Sin sosai ba, har ma ta kawo wa duk duniya alheri.

Yanzu kasar Sin tana taka muhimmiyar rawa a fannin raya tattalin arzikin duniya bai daya. Game da wannan, Wang Yusheng, tsohon babban jami'in kasar Sin a kungiyar APEC ya bayyana cewa,"Yau da shekaru 30 da suka wuce, ko da yake akwai wasu cikas, amma ma iya cewa, sabuwar kasar Sin ta sami ci gaba bayan kafuwarta, ta aza harsashi. Bayan da ta fara yi gyare-gyare a gida da bude kofarta ga waje a shekarar 1978, kasar Sin ta sami saurin bunkasuwa, ta tabbatar da samun farfadowar al'umma a mataki na farko. Bayan shekaru 30, karfinta ya sami kyautatuwa sosai. Yanzu muhimmancinta a manyan kungiyoyin duniya a fannin tattalin arziki ya sami saurin ingantuwa. Ana daukar cewa, yanzu kasar Sin na taka muhimmiyar rawa a duk duniya."

Bunkasuwar kasar Sin ta kuma samar wa kasashen duniya dama. Yanzu an sami ra'ayi daya a duk fadin duniya, wato manyan kamfannoni mallakar wasu kasashe in ba su shiga kasar Sin ba, to, wannan ya nuna cewa, za su rasa fifiko bisa manyan tsare-tsare.

A sakamakon bunkasuwar kasar Sin, masana'antun kasar Sin sun fara fita zuwa ketare. Yanzu masana'antun kasar Sin sun zuba jari a kasashe da yankuna fiye da 160 kai tsaye. Jarin da suka zuba a Afirka da Latin Amurka da kuma Asiya kai tsaye ya kara inganta bunkasuwar tattalin arzikin wurin.

A fannin kayayyaki kirar kasar Sin kuwa, fararen hula na sassa daban daban na duniya, ciki har da na kasashe masu ci gaba da masu tasowa, dukkansu sun ci riba sosai daga wadannan kayayyaki kirar kasar Sin. Ingantattun kayayyakin kasar Sin masu rahusa sun sanya kasashen duniya rage kudaden shigowa, haka kuma sun sanya masu saye-saye na duk duniya kara jin dadin zamansu.

Dangane da tasirin da kasar Sin ke kawo wa tattalin arzikin duniya bisa bunkasuwarta, Mr. Wang Yusheng ya ce,"Bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin na iya wakiltar wasu kasashe masu tasowa, kamar kasashen Indiya da Brazil. Tabbas ne irin wannan bunkasuwa za ta canza tsarin duniya. Da farko, ta canza matsayin da kasashen duniya ke tsayawa. Kasashe masu tasowa sun kyautata matsayinsu a cikin tsarin tattalin arziki na duniya sosai. Na biyu kuma, tabbas ne a gaggauta raya duniya a matakai daban daban. Ba za a iya hana haka ba."

Bugu da kari kuma, bunksuwar tattalin arzikin kasar Sin tana matsayin wata angar zaunar da tattalin arzikin duniya. A shekarar da muke ciki, a lokacin da matsalar kudi ta duniya take addabar duk duniya, kasar Sin ta kaddamar da shirin zuba jari da yawansa ya kai kudin Sin yuan biliyan dubu 4. Ta sami babban yabo daga duk duniya.

Shekaru 30 sun wuce cikin sauri. Ma iya cewa, in kasar Sin ba ta yi gyare-gyare a gida da kuma bude kofarta ga waje ba, ba za a iya samun nasarori kamar haka ba. A matsayinta na mai shiga aikin raya tattalin arzikin duniya bai daya cikin kwazo, kasar Sin, wadda take yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga waje, za ta ci gaba da nuna budaddiyar zuciya domin fuskantar sabuwar takara da kuma sabon kalubale da tattalin arzikin duniya ke kawo mata, za ta ci gaba da samar da abin al'ajabi irin na kasar Sin ga kasahsen duniya, sa'an nan kuma, za ta ci gaba da kawo wa kasashen duniya karin dama.(Tasallah)